Wata Rana Shehul Hadi Murtaniya, yana zaune tare da almajiransa sai wani jirgin sama ya wuce sai aka ga Shehu ya kama kuka.

“Wata Rana Shehul Hadi Murtaniya, yana zaune tare da almajiransa sai wani jirgin sama ya wuce sai aka ga Shehu ya kama kuka.

 

Sai almajirinsa ya tambayeshi, Sheikh lafiya kake Kuka ?”

 

Sai yace wani jirgi ne naga ya wuce; sai almajirin yace ni ma na ganshi, sai Shehul Hadi yace ka ganshi? Sai yace Eh, na ganshi? Yace Eh, sai Shehul Hadi yace wani irin kala ne? Sai yace ban sani ba, sai yace ya tsawon jirgin fa? Sai yace ban sani ba, ya faɗinsa yake? Yace ban sani ba, yace ya cikinsa yake ? Yace ban sani ba, yace kasan kujerun cikinsa? yace a’a, kasan adadin mutanen da ya ɗauko? Yace a’a, yace kasan Direbobin sa ko nawa ne? yace a’a, yace kasan inda ya fito? Yace a’a, yace kasan inda zai je? Yace a’a, yace kasan mai shi? Yace a’a, Shehul Hadi yace to wallahi haka Shehu Ibrahim Niasee (Radiyallahu anhu) yazo duniya ya wuce ba wanda ya san ko shi wanene, sai almajirinsa shima ya fashe da kuka Allah ya ƙara mana kaunarsa.

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button