Wata Rana Wani Balarabe (A Lokacin MANZON ALLAH(S.A.W) Yana Cikin Tafiya a Daji Bayan Ya Kamo.
‘KISSAR DAMO;
Wata Rana Wani Balarabe (A Lokacin MANZON ALLAH(S.A.W) Yana Cikin Tafiya a Daji Bayan Ya Kamo Wani ‘Katon Damo Domin Ya Kai Gidansa Ayi Abinci Da Shi, Yana Cikin Tafiya Sai Ya Hangi Wani Taron Mutane.
Ya Riski Mutanen Yana Tambayarsu Shin Me Yake Faruwa Ne???
Sai Mutanen Suka Ce Da Shi: “Wai Muhammadu Ne ‘Dan Abdullahi Ya Zo Yana Cika Mana Baki Wai Shi Annabin ALLAH Ne”.
Take Balaraben Nan Ya Samu Ya Kutsa Kansa Da Karfin Gaske Cikin Taro Ya Riski MA’AIKI(S.A.W) Inda Ya Ce Da Shi: “Ya MUHAMMADU! Ba Zan Yi Imani Da Kai a Matsayin Annabin ALLAH Ba Har Sai Wannan Damon Yayi Imani Da Kai”
Nan Take Ya Jefa Wannan Damon Akan ‘Kafar SHUGABA(S.A.W) Cikin Hanzari Damon Ya Nemi Ya Gudu Daga Wajen Sai NABIYYUR-RAHMATI(S.A.W) Ya Yiwa Damon Nan Magana Inda Ya Ce Da Shi Ya Tsaya Kuma Ya Juyo Baya.
Take Damon Ya Juyo Ga MA’AIKI(S.A.W) Ya Ce Da Shi:
“Ina Jiran Umarninka Cikin Girmamawa Ya RASULULLAH!”.
*.GA YADDA HIRARSU TA KASANCE:
MANZON ALLAH(S.A.W): “Waye Kake Bautawa???”
DAMO: “Ina Bautawa ALLAH Ne Wanda Buwayarsa Da MulkinSa Yake Ko Ina, Mamallakin Sammai Da ‘Kassai, Wanda Ya Sanya RahamarSa a Aljannah, AzabarSa Kuma a Wutar Jahannama”.
MANZON ALLAH(S.A.W): “Waye NI Kuma???”
DAMO: “Kai Ne MANZON ALLAH Ma Mallakin Sammai Da ‘Kassai, Kuma Cikamakon Annabawa, Amincin ALLAHU Su Tabbata a Gare Ka, Duk Wanda Ya So Ka Ya Tsira, Wanda Kuwa Ya ‘Kika Ya Halaka”.
Balaraben Nan Yana Jin Hakan Kawai Sai Jikinsa Yayi Sanyi, Ya Ce; Baya Buqatar Wata Shaida Bayan Wannan Inda Take Ya Ce;
Ya Shaida Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH Kuma ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) BawanSa Ne Kuma ManzonSa Ne.
Sai Kuma Ya ‘Kara Da Cewa:
“Lokacin Da Na Tarar Da Kai a Farko, Na Rantse Babu Wani Halitta a Doron ‘Kasa Da Nafi Tsana KamarKa(S.A.W),
Amman Yanzu Da Na Saurare Ka Wallahi Na Fi Sonka Fiye Da Idanuwana, Kunnuwa Na, Baba Na, Mama Ta, Da ‘Ya’yana”,
ALLAH Ya ‘Kara Mana ‘Kaunar ‘DAHA (S.A.W), Ya ‘Kar6i Rayukanmu Da ‘KaunarSA (S.A.W). Amiiiin