Watarana Wani saurayi ne yaje wajen ANNABI S.A.W, yace ya Annabin Allah kai min izini na yi zina

Watarana Wani saurayi ne yaje wajen ANNABI S.A.W, yace ya Annabin Allah kai min izini na yi zina.

Sai mutane suka hayyako masa suna cewa, tir da kai! Sai Annabi yace masa ya matso kusa da shi, Sai ya matso ya zauna.

 

Daga nan sai ANNABI S.A.W yace masa, za ka so ma mahaifiyarka yin Zina ? Sai yace, ‘A’a Wallahi!

 

Sai Annabi yace masa, hakanan mutane ba za su so ma mahaifiyarsu yin zina ba.

 

Sai Annabi yace masa, za ka so ma ‘yarka zina?

 

Sai ya ce, ‘A’a Wallahi! Sai Annabi S.A.W yace, hakanan mutane ba za su so ma ‘yarsu zina ba.

 

Sai Annabi yace masa, za ka so ma kanwarka zina?

 

Sai yace, A’a Wallahi,.

 

Sai Annabi yace, haka nan mutane ba za su so ma kanwarsu zina ba.

 

Sai Annabi ya sake ce masa, za ka so ma goggonka zina? Sai mutumin yace, A’a Wallahi!

 

Sai Annabi yace, hakanan mutane ba za su so ma goggonsu zina ba.

 

Sai ya sake ce masa, za ka so ma innarka zina?

 

Sai Mutumin yace, A’a Wallahi!

 

Sai Annabi yace, hakanan mutane ba za su so ma innarsu zina ba.

 

Daga nan Sai ANNABI S.A.W ya yi masa Addu’a yace: “Ya Allah ka gafarta masa zunubinsa, ka tsarkake zuciyarsa, ka kuma katange masa farjinsa”.

 

Jama’a Wallahi mu kiyaye Duk Abunda baka son ayi maka wallahi karka Yarda ka yiwa Wani. Idan ka bata Yar wani wallahi kaima sai an bata Yarka wannan ko shakka babu.

 

Allah ya tsaremu da Sharrin Shaidan Albarkan ANNABI S.A.W. Amiin

Share

Back to top button