Ya ALLAH! Yi Salati Da Taslimi Gare SHI Da Iyalan Gidansa Masu Alfarma, Da Sahabbansa Masu Albarka.

ANNABI MASOYIN AL’UMMARSA (S.A.W)!

 

A LOKACIN AWUN MIZANI(Ayyuka):

 

SHI Ne Lokacin Da Iyaye Ke Guje Ma ‘Ya’yansu, Su Ma ‘Ya’yan Suna Gudun Iyayensu. Miji Yana Guje Ma Matarsa, Ita Ma Matar Tana Guje Ma Mijinta. Ballantana ‘Yan Uwan Juna Ko Abokai a Wannan Lokacin Zasu Rika Tsine Ma Junansu(Sai Dai Wadanda Suka Yi Abotarsu Domin ALLAH).

 

Amma Shi MANZON ALLAH(S.A.W) Yana Zaune a Wajen Yana Kallon Irin Awun Da Za’a Yiwa Al’ummarsa. Har Ma Akwai Wadanda Za’a Tafi Da Su Wuta, Amma Shi Zai Shiga Tsakani. Ya Hana Tafiya Da Mutumin. Har Ma Zai Fito Da Wata Takarda Mai ‘Dauke Da Wani Salatin Da Wannan Mutumin Ya Ta6a Yi Masa. Idan Aka ‘Dora Wannan Salatin Akan Mizani Sai Ya Rinjayi Dukkan Zunubansa. Don Haka Sai a Tafi Da Shi Aljannah.

 

Ya ALLAH! Yi Salati Da Taslimi Gare SHI Da Iyalan Gidansa Masu Alfarma, Da Sahabbansa Masu Albarka, Da Dukkan Salihan Bayinka Har Zuwa Ranar Sakamako.

 

ALLAH YA ‘KARA MANA SON MA’AIKI (S.A.W) AMEEEEN.

Share

Back to top button