Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Taimakawa Farfesa Ibrahim Maqari Akan Yunkurin Kawo Gyara A Najeriya.

YA KAMATA GOBNATIN NIGERIA TA FITO TA DAFA MASA BISA IRIN SADAUKARWAR DA YAKEYI, DUK DA BA MURADINSA HAKAN BA.

 

Jami’an tsaro zasu huta daga kashesu da sanya rayuwarsu cikin hatsari da akeyi, talakawa zasu samu kwanciyar hankali da nutsuwa, Alkalai zasu huta da kawo musu shara’oin kisan kai tare da dangoginsa masu rikitarwa, Gobnatin tarayya zata huta daga ware makudan kudade domin siyo makamai a kasafin fannin tsaro, muddin yunkurin da ya dauko ya dore.

 

Domin lallai ne shi ainashin tushen matsalolin da suke haifar da wadancan matsalolin na sama yake kokarin kawarwa a aikace, wadanda suka kare cikin “RASHIN KULAWA DA MASU RAUNI, KARSHE SU TASHI SU ADDABI AL’UMMAR DA TA WATSAR DASU KUMA SU ADDABETA.

 

Ina bibiya bibiya na tsanaki, cikin zantuka da ayyuka na fitattun mutanen da suka sadaukar da karfinsu, lokacinsu da kuma tunaninsu akan magance matsalolin al’umma, amma lallai shi din a irin wannan lokacin ya fita na daban, domin irin zantukan zaburarwa da yakeyi a Majalisan da yakeyi na Qafilatul Mahabba, wallahi ba zantuka bane na zallar shauki face zantukane na zallar kishinsa, zallar tsagwaran begensa akan tayaya al’ummar yau zata zamo silar dakile matsalolin al’ummun da da za suzo nan gaba.

 

kamar dai yadda duk ababe masu amfani da ayau muke alfahari dasu, to wasu daga magabatan jiyane suka sadaukar da lokutansu, tunaninsu, kudinsu da kuma damarsu wajen samar mana su.

 

Duk da ALLAH da dafa masa ko a halin yanzu an cimma tarin nasarori daga soma yunkurinsa na ganin ya tallafawa Gobnati da Al’umma baki daya da irin damar da yake da ita, wajen kokarin assasa Majalisai a karkashin wannan gidauniya ta “QAFILATUL MAHABBA” ta hanyar fito da Maudu’ai da kuma ayyukan da zasu zamo silar magance matsalolin da kasa ke ciki, dama wanda zaizo nan gaba.

 

To amma lallai Gobnati irinsa ya kamata ta tallafawa da duk abinda ake da muradi domin fadada cimma wannan manufa, domin wallahi wannan manufar tasa, da aikin da ya dauko cikinsa muke jiwo kamshin samun zaman lafiya mai dorewa da kuma ci gaba ta dukkanin fuskoki na rayuwa.

 

ALLAH YASA HAKAN YA TABBATA ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W). AMIIN YAA ALLAH.

 

DAGA: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button