Yadda Aka Gudanar Da Gagarumin Taron Mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani RA A Birnin Bauchí.

AN GUDANAR DA GAGARUMIN MAULIDIN SHEIKH AHMAD TIJJANI (RTA) A GARIN BAUCHI

 

Daga Umar Aliyu Adamu

 

An gudanar da gagarumin maulidin Maulana Sheikh Ahmad Tijjani RTA a garin Bauchi kamar yadda aka saba gabatar duk shekera maulidin ya gududana ne a filin wasa na Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa dake garin na Bauchi

 

Taron ya gudana ne ƙarkashin kulawar gidauniyar maulana Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi RTA wato Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi Foundation wadda khadimul faidah Genaral Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi RTA yake jagoranta taron ya samu halartar manyan Shehanai, Malamai, Zakirai dama Sha’iran daga jahohin daban daban na cikin kasar nan

 

Khalifan Sheikh Ahmad Tijjani RTA Khalifa Sheikh Ali Bel Arab shine ya kasanche babban bako a taron maulidin inda ya samu rakiyar sharifai malamai dama wakilan kasar Algeria, daga sauran ƙasashe kuwa kamar Senigal da Morocco suma anasamu baki mahalarta taron

 

Gwamnan Jahar Alh. Bala Muhammad (Kauran Bauchi) wadda ya samu wakilchin mataimakin shi Alh. Muhammad Auwal Jatau ya nuna farin cikin matuƙa ga dubban al’umma mahalarta taron tare da godiya na musamman ga maulana Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi RTA da irin soyayyar da yake nunawa musu na kawo musu wannan babban taro garin Bauchi

 

Maulana Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi RTA ya gabatar da jawabai masu matuƙar mahimman manchi tare da janhankalin al’umma akan aƙara dagewa da addu’oi.

 

Allah ubangiji zai kawo mana saukin yanayin da ake ciki Alfarman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Allah ubangiji ya maimaita mana Amiin

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button