Yadda Aka Yi Gwagwarmayar Tattatar Da Darikar Tijjaniyya Cikin Lumana A Kasashen Turawa.

TIJJANAWA ƳAN GWAGWARMAYA NE A CIKIN LUMANA….

 

A cikin shekarar 1925, aka kafa dokar hana kiran salla a ƙasar Turkiyya, da harshen Larabci wanda akwai hukunci mai tsanani ga dukkan wanda ya karya wannan doka..

 

Tun a wannan lokacin mabiya ɗariƙar Tijjaniyya ba su amince da wannan kuduri da gwamnati ta kawo ba, kuma a wannan lokaci suna da yawa sosai, domin Mista Marmostein ya kawo kididdigar mabiya ɗariƙar Tijjaniyya, wanda ya ce za su kai kusan mutane miliyan daya ko su haura, a cikin wani littafinsa na tarihin kafuwar ƙasar Turkiyya, ta zamani.

 

Wannan yawa ya yi matuƙar taimakon mabiya ɗariƙar Tijjaniyya wajen bijirewa wannan mummunan hukuncin zalunci. Duk da a wannan lokacin ba sa amfani da abin sauti mai karfi…

 

A cikin shekarar 1948 ƙasar Turkiyya, sun yiwa dokar gyara inda suka ba da damar cewa za’a iya yin kiran salla amman a ranakun bikin addini kawai…

 

A shekara ta 1949 wasu da suka kasance jagorarin ɗariƙar Tijjaniyya, su biyu akwai wani mai suna Muhiddin Ertuğrul, da kuma Osman Yaz, sun karanta kiran salla da harshen larabci a gaban majalisar dokokin garin Ankara a yayin wani zaman majalisa, don nuna adawa da sauran haramcin da ya rage…

 

Dr. Cathlene Dollar, wani malamin Jami’ar Cape Town, da ke ƙasar Afirka ta Kudu, ya rubuta a wata makalarsa da ya yi a kan, siyasar Mustafa Atatürk, cewa: ” Misalin ɗariƙar Tijjaniyya a ƙasar Turkiyya, ya kasance na musamman, kuma abin sha’awa duk da asalinta ya fito daga Arewacin Afirka.

 

Kuma ta samu bambanci da sauran ɗariƙun sufaye, wanda ragowar sun fi mai da hankali akan maganganun kishin ƙasa na sabuwar Jamhuriyar, da ra’ayin kyamar Kemal, da kuma ra’ayin cusawa yara masu tasowa kyamar, rushasheshiyar daular Ottoman”….

 

Saɓanin haka, ɗariƙar Tijjaniyya ta ci gaba da kasancewa da kyakkyawar tafiyar addini da kuma nunawa duniya, kyamar sababin dokakin gwamnatin waɗanda suka saɓawa haƙiƙanin koyarwar addinin musulunci..

 

Allah ya cigaba da taimakon musulunci da musulmi.. Amiiin Yaa ALLAH

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button