Yadda Azumi Yake A Wurin Bayin Allah Sufaye.

AZUMI A WURIN SUFAYE

 

Allah ya tabbatar da cewa abubuwa guda biyu babu wanda yasan adadin ladan su, sai shi kadai, sune HAQURI da AZUMI. Dalili kuwa, haquri da azumin duk suffar bayin sa ne waliyai, babu wanda kuwa yasan girman su a wajen sa, shiyasa ma in ka taba waliyyin sa, shi da kanshi zai yaqe ka.

 

A bisa koyarwar Shari’a, Azumi shine kamewa daga ci, sha, kusantar iyali, nisantar ayyukan sharri da kuma qarfafa ayyukan alheri a cikin ranakun wata na tara (ramadan) a watannin arabiya, tsawon kwana 29 zuwa 30.

 

Amma a wurin sufaye, azumi shine kamewa daga son zuciyar ka, zuwa abinda Allah yake so ta yadda yake so, a ko da yaushe.

 

Wannan muqami ne na waliyai, wayanda ko da yaushe suke kokarin aikata abinda Allah zai ji dadi, da barin duk abinda zaisa Allah yayi fushi dasu. Ba kuma sai a cikin wata daya ba, A’a, kullum cikin haka suke.

 

Kalmar azumi a larabci shine صوم (Saum).

Harafin ص adadin sa shine 90, Harafin و adadin sa shine 6, adadin م adadin sa shine 40.

90 + 6 + 40 = 136.

 

136 din nan in ka juya shi zuwa haruffa, zai baka ولي (Waliy) wato waliyyi.

 

Ko babu yawan azkarai da nafiloli, in ka kame kanka daga biyewa son zuciyar ka, zaka shiga sahun waliyan Allah ma’abota girman daraja.

 

Dan haka yan’uwa, kamar yadda muke gasa da juna wurin tara abin duniya, ya kamata muyi fiye da haka wurin neman yardar Allah (wulaya).

 

Amma matakin samun yardar Allah na farko, shine rashin cutar da halittun sa, da kuma yawan yafiya garesu in suka cuce ka, sai sanin sa sani na haqiqa, sannan kiyaye umurni ko hanin sa gwargwadon iko.

 

Allah kasa mu fi qarfin zuciyar mu, ka bamu abin masarufi cikin wannan wata da za a shiga mai albarka, ka rufa mana asiri cikin ludufin ka, ka bamu ikon azumtar watan, idan munyi ka karɓa, domin darajar Madinah da wanda yake kwance cikin ta.

 

✍️Sidi Sadauki.

Share

Back to top button