Yadda Madinatu Sheikh Ibrahim Inyass Dake Ƙasar Senegal Ya Sha Ado Ga Haske.

ALLAHU AKBAR:

 

Yadda Madinatu Sheikh Ibrahim Inyass Dake Ƙasar Senegal Ya Sha Ado Ga Haske Duk A Domin Murna Da Watan Maulidin Annabi Muhammadu (SAW).

 

Watarana ANNABI S.A.W ya hau MIMBARI sai yace

 

“MAN ANA” ? Sai mutanen suka ce masa “kai ne RASULULLAH”

 

Sai ANNABI S.A.W yace Eh lallai kun sanni amma ba wannan nake Tambayarku ba, Sai ya sake tambayarsu Waye ni?

 

Sai suka ce “kai ne MUHAMMADU Ibn ABDULLAH Ibn ABDUL-MUDDALIB Ibn HASIM”

 

Sai ANNABI S.A.W yace “Na’am Walakin man Ana”

 

Lailai haka yake nasan kun sanni amma ba wannan nake tambayarku ba. Har yanxu dai Waye ni?

 

To sai jama’a sukayi shiriu sun kasa bada amsar, Sai ANNABI S.A.W yace “ANA SAYYIDUN WALA DA ADAMA WALA FAQRA”

 

Ma’ana: “Ni ne Shugaban Yayan Adamu gaba daya bada Alfahari ba”

 

Allah ya kara mana soyayyan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button