Yadda Nisabin Zakka Da Sadaki Da Diyyar Rai Zai Kasance A Shekarar, 1444/45 Ah 2023
Gidan jarida ta Alfijr ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta wallafa yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana 1444 Ah 2023, kamar yadda ta saba duk shekara.
MAFI KARANCIN SADAKI
₦24, 637 shine mafi karanci, amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.
Kimar Yanke Hannu A Sata
₦24,637 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.
NISABIN ZAKKA ZAI FARA DAGA ₦1,970,968. 00.
Za a kasa wannan kucin gida (40) wanda zai zamanto ₦49,274.2 shi za a bayar
Idan kudin ya haura Nisabi, za a kasa gida Arba’in (40) a bayar da kashi daya (1/40).
Diyyar Rai A MUSULUNCI
₦98,548,405,00
Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci, sakamakon hawa da saukar Dinare.
NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA
RAKUMA: Daga (5 – 9) Akuya 1
Daga (10 – 14) Awaki 2.
Daga (15 – 19) Awaki 3
Daga (20 – 24) Awaki 4.
Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.
SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki
AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da
Akuya/Tunkiya. Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har Zuwa dari biyu da daya, sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da ɗaya.
NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA
1 Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).
2 Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).