Yan’Bndiga sun Kashe Dalibi Daya Tare da yin Awon Gaba da Mutun 9 Ana Tsaka Da Mauludi a Zagami Ta Garin Faskari.

LABARI MARA DADI:

 

‘Yan bindiga sun kashe ɗalibi ɗaya tare da yin awon gaba da mutum 9 ana tsaka da Mauludi a Zagami ta karamar hukumar Faskari.

 

A daran Alhamis wayewar garin yau Jumu’a, yan bindiga sun tarwatsa wurin da ake tsaka da gudanar da bikin mauludi, a kauyen Zagami dake ƙarƙashin ƙasar Yankara, yankin karamar hukumar Faskari nan jihar Katsina, inda har suka kashe ɗalibi daya, tare da sace akalla mahalarta taron Mauludin mutum 9.

 

Lamarin ya afku ne da wajen misalin karfe 12am da yan mintota na daran jiya Alhamis wayewar garin yau Jumu’a, kamar yadda mai Unguwar garin ya tabbatar wa Katsina Daily News

 

“Yanzun nan muka dawo zana’idar yaron da suka kashe, wanda dalibi ne a makarantar malam Hadi, ta Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi dake Sheme, sun kuma saci mutum 9 ciki har da dan uwan marigayin.” Inji mai Unguwar.

 

Za a iya tuna cewa ko a ranar Lahadin da ta gabata wayewar Litinin, an sami irin wannan harin na yan bindiga, da suka afkawa masu mauludi a kauyen Kusar Fulani dake cikin karamar hukumar Musawa duka a nan cikin jihar Katsina, inda suka hallaka akalla mutum 14 tare da jikkata sama da 20 da munanan raunuka na harbin bindaga.

 

Credit: Katsina Daily News

Share

Back to top button