Yanda Darikar Tijjaniyya Ta Bunkasa A Kasashen Turawa.

Babban Shehin ɗariƙar Tijjaniyya a ƙasashen Turai Sheikh Abdussamad Bolag.

 

Shehin asalinsa ɗan ƙasar Isra’ila ne, amman mazaunin ƙasar Jamus. Kafin gudun hijirarsa a dalilin yakin duniya na biyu zuwa ƙasar Indiya, ya kasance malami ne a addinin Yahudawa.

 

A ƙasar Indiya ya musulunta, bayan komai ya yi sauƙi na yakin da ya ke faruwa ya dawo ƙasar Switzerland inda a wannan ƙasa ya haɗu da Sheikh Hampet, babban almajirin Sheikh Tierno Bukar, shi ne ya fara ba shi ɗariƙar Tijjaniyya…

 

Sheikh Abdussamad Bolag ya yi kokari sosai wajen musuluntar da Turawa musamman a irin ƙasashen Rasha, Italiya, Faransa, sai kuma uwa uba ƙasar da ya ke zaune Switzerland, kuma dukkan wadannan kasashe babu inda bai kafa zawiyoyin ɗariƙar Tijjaniyya, ba. Ya kuma shahara sosai da kira zuwa addinin musulunci…..

 

Muna roƙon Allah ya ƙara kusanta shi da Shehu Tijjani saboda girman shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama. Amiin Yaa ALLAH

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button