YANZU-YANZU; An Fitar Da Sunayen Tijjanawa Wadanda Suka Samu Tallafin Scholarship Zuwa Kasar Algeria.
YANZU-YANZU; An Fitar Da Sunayen Wadanda Suka Samu Scholarship Na Kasar Algeria.
AKWAI PDF NA LIST DIN SUNAYE A KASA
Gwamnatin kasar Algeria ta fitar da sunayen wadanda suka samu tallafin karatun na scholarship wanda aka bawa gidaunuyar Sheikh Dahiru Bauchi RA tare da hadin gwiwar Supreme Council for Faidha Tijjaniyya Islamic Affairs.
An fitar da sunayen mutum 88 cikin mutum 185 wanda suka cika gurbin karatu wanda gwamnatin kasar Algeria suka tantance su.
Idan mutum yayi nasara ana bukatar ya tura takardun su zuwa daya daga cikin garuruwan da suka fi kusa da su, da suka hada da babban birnin tarayya Abuja, Bauchi da kuma birnin Kano. Ko kuma a kira wannan number don karin batani – +234 704 090 0333.
A wata ziyara da babban malamin addinin Muslunci a duniya Maulana Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA, yakai kasar Algeria inda ya ziyarci Babban Khalifa Darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Khalifa Ali Bel Arabi tare da wasu jami’an gwamnatin kasar Algeria sun bawa gidaunuyar Sheikh Dahiru Bauchi tallafin karatun na scholarship zuwa kasar Algeria.
Tallafin karatun na scholarship ya gudana a karkashin jagoranci shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune tare da hadin gwaiwan babban Khalifan Tijjaniyya na duniya Sheikh Ali Bel Arabi inda suka bawa mutum dari uku (300) Tijjanawa tallafin karatu zuwa kasar Algeria kwauta don kara taimakawa tijjanawa a harkokin rayuwar su.
Cikin wadanda suka cika gurbin karatu sun kai mutum fiye da 350, inda gwamnatin kasar Algeria ta tantance mutum 88 a cikin su.
Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya bawa wadanda suka samu gurbin karatu ya amfanar dasu. Amiiiin Yaa Allah.
Ga List Din Sunayen Kamar Haka; 👇👇
Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News