YANZU YANZU: An Gabatar Da Jana’izar Mutum 4 Da Mahara Suka Halaka a Zariya.

YANZU YANZU: An Gabatar Da Jana’izar Mutum 4 Da Mahara Suka Halaka a Zariya.
Daga Mahmud Habibullah Zariya
An gabatar da jana’izar mutum huɗu da mahara suka suka halaka a garin Zariya a cikin daren na yau Asabar, maharan sun afka cikin wani anguwa da ake kira da anguwar dankali dake danmagaji Zariya jihar kaduna ɗauke da muggan makamai suna hare-hare kan mai uwa da wabi.
Wakilin jaridar ALFIJIR HAUSA ya samu tattaunawa da wasu ba’adi na al’ummar da lamarin ya faru a anguwar nasu.
Inda suka tabbatar masa da cewa maharan sun yi awon gaba da mutum biyar rigis duk da duba da irin ɓarnar da sukayi wanda har yanzu ba amo bare kuma labarin waɗanda suka tafi da su ɗin.
Muna kira ga gwamnati da tayi abunda ya dace don kawo karshe wannan lamari, Allah ya kawo karshe wannan masifa.
Allah ya jikan su da rahma ya gafarta masu, Allah ya karbi shahadar su baki daya. Amiiin