YANZU-YANZU: Shahararren Malamin Musulunci A Najeriya Sheikh Dahiru Bauchi Yayi Magana Akan Batun Tsaro A Najeriya

YANZU-YANZU: Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA Yayi Tsokaci Akan Lamarin Tsaro A Najeriya.

 

……Sheikh Dahiru Bauchi RA Yace:

 

Inna Lillahi Wa’inna Ilahi Raaji’un, Inna Lillahi Wa’inna Ilahi Raaji’un, Lamarin kasar mu yakai abinda ya kai Allah mun dawo gare ka, kai mana magani. Ya Allah idan su wadancan basu sanka ba, mu mun sanka ya Allah mun dawo a gare ka.

 

Abinda yake damun mu na Kidnapped, Boko Haram, Bandits da sauran fitittun dake faruwa a najeriya, kai mana maganinsu da sauri da sauri ya Allah.

 

Allah kai kayi maganin Ash’habul Fi’ili, kai kai maganin dukkan kafuran da da suka wuce. muna rokon ka Albarkar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da matsayinsa a wajen ka, Albarkar Annabta da abinda ta kunsa, Albarkar Shehu Ahmadu Tijjani Radiyallahu Anhu da abinda walittaka ta kunsa a wajen ka, Albarkar Shehu Ibrahim Radiyallahu Anhu da faidharsa, Albarkar dukkan wanda yake yi maka Ruku’u da Sujjada, YAA ALLAH muna rokon ka kai mana maganin wadannan da sauri Yaa ALLAH.

 

Muna bada wurdi ariqa karanta;

 

Alamtara Kaifa: Million daya da dubu dari da dubu goma sha daya waton (1,111,000) za’aga sauyi da wuri wuri insha Allah. Anayi ana maimaitawa.

 

Shehu yace maza-maza a fara aiki (Addu’a).

 

Allah Ubangiji ya kawo mana sauyi a kasar mu Najeriya, Allah ya bamu shugabanni nagari.

 

Allah ya kara inganta lafiyar Maulanmu Sheikh Dahiru Bauchi RA da tsawon rai albarkar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Amiin.

Share

Back to top button