Yau Ne Aka Kaddamar Da Alkur’ani Mai Girma Zuwa Harshen Igbo A Abuja.

A yau Juma’a ne aka kaddamar da AlKur’ani mai girma da aka fassara zuwa harshen Igbo a Abuja babbar birnin Najeriya.

 

Kungiyar Musulmi daga yankin kudu maso gabashin Najeriya ce ta fassara AlKur’anin.

 

  1. Shugaban kungiyar Malam Muhammed Muritala Chukwuemeka, wanda ya shaida wa BBC cewa manufarsu ita ce isar da sakon Allah ga ‘yan uwansa ‘yan kabilar Igbo, ya kara da cewa ya kwashe shekara biyar yana aikin fassarar.

 

ALLAH yasa Alƙur’ani ya cece, ya amfanar damu dashi cikin rayuwar mu duniya da lahira baki daya. Amiin

Share

Back to top button