Yau Shekara Biyar Kenan Da Rasuwan Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu.

Khalifan Tijjaniyya Sheikh Isyaka Rabi’u Ya Shekara Biyar Da Rasuwa.
A rana irin ta yau 7 ga watan Mayu na shekarar 2018 Allah ya ɗauki ran Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u Kano. Malam Isyaka Rabi’u sanannen ɗan darikar Tijjaniya ne yana ɗaya daga cikin manyan almajiran sheikh Ibrahim Inyass Kaulaha.
Kafin rasuwarsa ya kasance malamin addinin musulunci kuma Khalifan Tijjaniyya a Najeriya, sannan shahararren ɗan kasuwa ne wanda ya daɗe yana ayyukan taimakawa al’umma da kuma hidima garesu a tsawon rayuwarsa.
Marigayi Isyaka Rabi’u ya rasu ya bar mata da ƴaƴa har da jikoki masu yawa, Allah Ubangiji ya cigaba da rahama a gareshi mu kuma ya kyautata ƙarshenmu. Amin
Mustapha Abubakar Kwaro
Tijjaniyya Media News