Yau Shekaru 47 Da Rasuwan Sheikh Ibrahim Inyass RA

Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Cika Shekaru 47 Da Wafati.

A Rana irin ta yau 26 Ga Watan Yuli 1975 Allah ya karbi Rayuwar Shiekh Ibrahim inyass ( RTA )

 

SHEIKH IBRAHIM INYASS SHINE MALAMIN MUSULMI NA FARKO & KADAI A DUNIYA WANDA SARKI FAISAL NA SAUDIYYA YA ZIYARA A KAUYEN SA (KAOLACK) A SENEGAL.

 

Wanene Shaihu Ibrahim Niasse?

 

Niasse shi ne dan Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci Masallacin Al-Azhar a Masar , bayan da aka yi masa lakabi da “Sheikh al-Islam”. Ya kasance kusa da yawancin Shugabanin masu fafutukar Neman ‘yanci a Afirka ta Yamma saboda gudunmawar da ya bayar na ‘yancin kai a kasashen Afirka.

 

Shehu Ibrahim ya tsaya tsayin daka wajen yakar mamaya (Imperialism) da sabbi da tsoffin salon mulkin mallaka da kare yancin kasashe da mutuncinsu da kuma ganin sun tsaya bisa kafafunsu, tareda kara dankon zumunci tsakanin Kasashen Africa dana Yankin Asia dama karfafa tsaron Duniya baki daya.

 

Menene ma’anar Inyass?

 

Abubuwa 2 da aka gabatar daga Najeriya sun yarda da sunan Inyass yana nufin ” Mutumin kirki ”

 

Ibrāhīm Niasse (1900–1975) – ko (Faransanci Ibrahima Niasse) , Wolof , Larabci: شيخ الإسلام الحاج إبراهيم إبن الحاج عبد الله التجاني الكولخي‎ التجاني الكولخي Shaykh al-‘Islām al-Ḥājj Ibrāhīm ibn al-Ḥājj ʿAbd Allāh at-Tijānī al-Kawlakhī – ya kasance babban shugaban Senegal (wolof) na Tijānī Sufi na Islama a Afirka ta Yamma . Mabiyansa a yankin Senegambiya suna kiran shi a harshen Wolof a matsayin Baay, ko “uba.”

 

Niasse shi ne mutumin Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci Masallacin al-Azhar a Misira, bayan an yi masa laƙabi da “Sheikh al-Islam”. Ya kasance kusa da masu gwagwarmayar neman ƴanci da yawa a Afirka ta Yamma saboda gudummawar da ya bayar don samun’ Ƴanci a Ƙasashen Afirka. Ya kasance aboki kuma mai ba da shawara ga Shugaban Ghana na farko, Kwame Nkrumah, da aboko Ga Gamal Abdel Nasser da Sarki Faisal na Saudi Arabia. Sheikh Ibrahim kasance Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya tare da Faisal a matsayin Shugaba.

 

An haife shi a Ranar Alhamis 8 Ga Watan Nuwamba 1900 a ƙauyen Tayba Ñaseen (wanda aka rubuta lafazin Taïba Niassène a Faransanci), tsakanin garin Kaolack na Senegal da iyakar Gambiya, shi ɗa ne ga Allaaji Abdulaay Ñas (1840-1922), babban wakilin Darikar Sufaye Ta Tijānī wanda galibi ake kira Tareeqat al-Tijjaniyya a, a yankin Saalum a farkon ƙarni na ashirin.

 

Yatashi Bisa kularwar mahaifinsa, ya Haddace Al-Qur’ani Mai Girma Hannun mahaifinsa A cikin kananan shekaru Yafa wallafa littafi yana da shekaru 21 a duniya.

 

A lokacin samartakarsa, Sheykh Ibrahim ya sake komawa tare da mahaifinsa zuwa garin Kaolack, inda suka kafa zāwiya (cibiyar addini) na Lewna Ñaseen. Bayan rasuwar mahaifinsa a Lewna Ñaseen a 1922, babban yayan Shaykh Ibrāhīm, Muhammad al-Khalīfa, ya zama magajin mahaifinsa ko Khalīfa.

 

Shaykh Ibrāhīm mai shekaru 22 ya shafe mafi yawan lokacinsa yana noma a gonar danginsa tare da koyar da yawan almajirai a ƙauyen da ke kusa da Kóosi Mbittéyeen. Duk da cewa Shaykh Ibrāhīm bai taba ikirarin cewa shi ne magajin mahaifinsa ba, saboda kwarjini da ilimin da yake da shi, ya samu dimbin almajirai, kuma rikici ya tashi tsakanin almajiransa da na babban yayansa, Muhammad al-Khalifa.

 

A cikin 1929, yayin da yake cikin gona a Kóosi Mbittéyeen, A lokacin Yana saurayi, Shaykh Ibrāhīm ya ba da sanarwar cewa an ba shi Mabuɗin Sirrin Ilimin Allah, kuma don haka ya zama Khalifa na Sheykh Tijani a cikin Dokar Tijaniyya, matsayin da ba wanda ya samu A wancan lokacin.

 

Daga nan Sheikh Ibrahim ya bayyana cewa duk wanda yake son ya sami ma’arifa, matakin Tabbacin Allah a cikin Darikun Sufaye, dole ne ya bi shi. A shekarar 1930, bayan Sallar al-Fiṭr (karshen watan Ramadān), fada ya barke tsakanin almajiran Shaikh Ibrahim da na Muhammad al-Khalīfa Lamarin da ya sa Shaihin Ibrahim nan da nan ya yanke shawarar komawa tare da almajiransa zuwa sabon wuri.

 

A wannan maraice, ya tashi tare da wasu rukuni na kusa da almajiransa don nemo sabon wurin zama, washegari kuma suka kafa sabuwar zāwiya a Madina Baay, wani ƙauye wanda daga baya aka sanya shi cikin garin Kaolack mai girma. shehin ya raba lokacinsa tsakanin koyarwa a lokacin rani a Madina Baay da noma a lokacin damina a Koosi Mbittéyeen. A lokacin bazara na Shekarar 1945 ya sake kafa kansa a gidan mahaifinsa a ƙauyensa na asali na Tayba Ñaseen, Ya sake ginawa da sake tsara garin bayan da gobara ta lalata yawancinsa.

 

Shaharar Shaykh Ibrahim ta bazu cikin sauri a cikin ƙauyuka, kuma mafi yawan almajiran mahaifinsa daga ƙarshe sun zama almajiransa duk da Kasancewarsa ƙarami a cikin iyali. Koda yake almajiransa sun kasance ‘yan tsiraru a cikin Senegal, amma sun kasance mafi girman reshe na Tijānīyyah a duk duniya. A Shekarar Cikin 1930, shugabannin da yawa na Larabawa ‘Idaw ʿAli na Mauritania-ƙabila ɗaya da Su ke Bin Darkar Tijānī Ta Yammacin Afirka, sun bayyana kansu A Matsayin almajiran Shaykh Ibrahim. Sanannen cikinsu shine Shaykhāni, Muḥammad Wuld an-Naḥwi da Muḥammad al-Mishri. Tareeqa al-Tijaniyya al-Ibrahimiyya, kamar yadda aka san almajiran shaikhu, ya bunkasa kuma ya sami ɗimbin mabiya a cikin shekarun 1930s da 1940 a duk Arewacin da Yammacin Afirka.

 

A shekarar 1937 lokacin da suka haɗu da Shaykh Ibrahim a lokacin aikin hajji a Makkah, Sarkin Kano, A Najeriya, Alhaji ‘Abdullahi Bayero ya yi mubaya’a ga shehin kuma ya bayyana kansa almajirin shaikh Ibrahim. Wannan lamarin ya sa Shaykh Ibrahim ya sami amincewar da yawa daga fitattun shugabannin Tijānīyyah A Arewacin Najeriya da ma wasu da dama wadanda ba Yan Darikar Ba.

 

Alhaji Abdulmalik Atta – basarake ne daga Okene kuma Babban Kwamishina na farko a Najeriya A Kasar Ingila, yana daya daga cikin manyan almajiran sheik Ibrahim da kuma surukin shehin ta hanyar ‘yarsa Sayyida Bilkisu. Shaykh Ibrahim ya zama sanannen Shaykh al-Tareeqa (Jagoran Darikun Sufaye) a ko’ina cikin yankunan Kasat Hausa na Yammacin Afirka. A ƙarshe, yana da almajirai nesa da Senegal. A lokacin rasuwarsa a 1975 a Landan, Ingila, Shaykh Ibrahim Niass yana da miliyoyin mabiya a duk Yammacin Afirka. Ya Rasu 25 Ga Watan Yuli A St Thomas’ Hospital, London, United Kingdom 🇬🇧. Yana Da Shekaru 75 A Duniya, A Rayuwar Ya Rubuta Litattafan Addini 75. Ya Haifi Ya’ya 75.

 

Dalilin Zuwan Sheikh Ibrahim Inyass Ne, Aka Samu Hutun Bikin Maulidin Manzon Allah SAW A Najeriya.

 

Sanadiyar Shehu Ibrahim Inyass RTA Ne Gwamnatin Najeriya Ta Sanya Hutun Maulidi Ya Zamo Doka A Kasa, Bayan Shehu Ya Zo Taya Najeriya Murnan Samun ‘Yanci A Shekarar 1960

 

Bayan Kasar Najeriya ta samu ‘yanci daga mulkin Turawa, Shehu Ibrahim Inyass RTA ya kawo ziyara Najeriya na musamman domin taya murnan samun ‘yanci, da Shehu ya gana da Firar minista na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Shehu ya bashi shawara cewa tunda kai Musulmi ne, ya kamata ka sanya ranar Maulidi ya zamo ranar hutu a Najeriya domin murnar zagayowan ranar da aka haifi Annabi Muhammadu SAW, kamar yanda abokinka Shugaban Kasa wato (Head Of State) Namdi Azikiwe yake hutun Kirsimeti, nan da nan Sir Abubakar Tafawa Balewa Ya Aika Da Wannan Dokar Majalisa, Bayan Anyi Zafaffiyar Mahawara Daga Karshe Dai Majilisa Ta Amince A Take Tafawa Balewa Ya sanya Hannu A wannan doka.

 

Wannan shine dalilin da yasa duk ranar Maulidin Annabi Muhammadu ﷺ gwamnati ke bada hutu.

 

Allah ya kara kusanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW. Amiin

Back to top button