YA’YAN ANNABI SAW: Dukkanin Yayan ANNABI Maza Da Mata NANA KHADIJA Ce Ta Haifa Masa Su In Banda Ibrahim 

YAYAN ANNABI S.A.W

 

Dukkanin Yayan ANNABI S.A.W maza da mata NANA KHADIJA ce ta haifa masa su in banda Ibrahim

 

Mahaifiyar Ibrahim itace “MARIYATUL KIBDIYYA” wacce mukankis ya bada ita kyauta ga ANNABI S.A.W

 

YAYAN SA MAZA SUNE:

 

1. SAYYIDI ALQASIM (da shine akeyiwa ANNABI S.A.W Al-kunya, kuma bai jima ba a duniya ya rasu

 

2. SAYYIDI IBRAHIM: (shine a lokacin da ya rasu saida ANNABI S.A.W ya zubar da hawaye harma yana cewa da Ibrahim yana raye da shima sai ya zama Annabin Allah amma da shike babu wani ANNABI a bayana shiyasa Allah ya dauke shi

 

3. Sai dansa SAYYIDI ABDULLAHI

An haifi Abdullahi ne a Madina ya rayu tsawon watanni 22 ya riga ANNABI S.A.W Rasuwa da wata 3 yadda tarihi ya nuna

 

YAYANSA MATA SUNE:

1. SAYYADA ZAINAB: itace babbarsu Dan goggonta (Abul-Ass) ne ya Aureta

 

2. SAYYADA RUGAYYA: mijinta shine Usman Bin Affan (R.A)

 

3. SAYYADA FATIMA: mijinta shine SYYD ALIYU BN ABI-TALIB (tahaifa masa Al-Hassan da AL-Hussaini) shuwagabannin matasan Aljannah

 

4. SAYYADA UMMUL-KHULSUM: Usman Bin Affan” ne ya Aureta bayan Rasuwar SAyyada Ruqayyah.

 

IMAM NAWAWI (R.A) yace babu tsabani kan cewa “YAYAN ANNABI S.A.W mata su 4 ne haka kuma maza su 3 ne abisa ingantacciyar magana

 

Allah ka bamu Albarkansu gaba daya bijahi S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button