Young Sheikh Yaro Mafi Kańkantar Shekaru Yà Kammala Jami’a A Fannin Shari’a.

Young Shèikh Mafi Kańkantar Shekaru Yà Kammala Karatuń Jami’a A Fannin Shari’a.

 

Fitaccèn karamin Malamin addinin Musuluncin nàn, Zakeer M.S Ali mai Yasin Wanda aka fi sani da Young Sheikh ya sake kafa wani sabon tarihi, inda ya kammala karatu a kan shari’a a wata babbar jami’a dake kasar Niger yana da karancin shekarun da basu wuce goma sha biyu ba.

 

Young Sheikh haifaffen garin Zaria dake jihar Kaduna wanda yake zaune a lungun Malam Aliyu mai Yasin, kuma kakaka yake ga Young Sheikh.

 

Shehin malamin yayi karatun sa na Firamari tare da sakandari a garin Zaria, Yayi karatun Alkur’ani mai girma tare da wasu littafafai a wurin mahaifin sa duk a garin Zaria daga bisani ya tafi Kasar Niger don cigaba da karatun Digree a fannin Shari’ar Musulunci.

 

Young Shièkh dai ya karancin Flfannin shari’a ne a wata Jami’a mai zaman kanta ta kasa da kasa dake gariń Maradin Jamhuriyar Nijar.

 

Allah ya kara lafiya da daukaka, ya kare shi daga sharrin makiya albarkacin Manzon Allah SAW. Amiiiin

 

DAGÀ Saifullahi Lawal Imam Zaria

Share

Back to top button