Za’a Gina Babbar Cibiyan Musulunci Ta Darikar Tijjaniyya A America Dake Birnin Washington DC

Mabiya Darikar Tijjaniyya Na Kasar Amerika Zasu Gina Babbar Cibiyan Musulunci A Birnin Washington DC

 

Rayyahi Sani Khalifa

 

Kungiyar Musulmai ‘yan Tijjaniyya a Amuruka mai suna ITFA (Islamic Tijjaniyya Foundation Of America) ta kirkiri shirin gina katafaren cibiyar musulunci mai suna ICC (Islamic Comunity Center) a birnin Washington dake kasar Amuruka. Za’a gina wannan cibiyar ne domin habbaka al’amuran addinin musulunci ta hanyar wayar da kan al’ummar duniya cewa addinin musulunci addinin zaman lafiya da soyayya da lumana ne. Bugu da kari wannan cibiyar na ICC zata kunshi bangarori kamar haka :

 

* Bangaren wurin ibada inda musulmai zasu rinka taruwa domin gudanar da ibadodinsu

 

* Bangaren bincike da dakin tarurruka domin habbaka zaman lafiya.

 

* Bangaren ilimi domin koyar da Alqur’ani da Sunna da koyar da zamantakewan iyali a tsarin musulunci.

 

* Bangaren al’adu inda shuwagabbannin addini da al’adu zasu yi majalisa domin tattaunawa akan al’amuran da suka shafi al’umma a yau da kullum.

 

Ita dai wannan kungiya na ITFA kungiya ce wacce ke da Hedikwata a birnin Washington DC kuma tana da rassa da ake kira hadara group guda 32 a fadin kasar Amuruka. An kafa wannan kungiyar ne domin samar da dubarun gadar da addini da riko da shi ga al’umma musamman ‘ya’yan musulmai da suke tasowa a yankin da al’adansu ba irin na musulmai ba. Kuma wannan kungiya tana aiki tukuru wajen Samar da agaji ga al’ummar musulmi musamman tijjanawa ta bangaren addini da zamantakewa da tattalin arziki. Babbar manufar wannan kungiya shine shiryar da mutane akan Sunnar Manzon Allah SAW da yada addinin musulunci cikin lumana..

 

Allah ya saka musu da alhairi kuma Allah ya bada ikon kamalla wannan aikin na ci gaba domain alfarmar Sayyiduna Rasulullahi SAW Amin

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button