Za’a Gudanar Da Gagarumin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA Karo Na 37th A Birnin Kebbi.

Za’a Gudanar Da Gagarumin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA Karo Na 37th A Birnin Kebbi.

 

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi RA tare da kungiyar Maj’ma’u Ahbabu Sheikh Ibrahim Inyass zasu gudanar da gagarumin taron bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq RA a babban birnin Kebbi, Nigeria. a karkashin jagoranci Khalifa Muhammadu Mahy Nissa RA da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.

 

Taron Mauludin zai samu halartan manyan baki daga sassa daban-daban na fadin duniya kamar yadda aka saba gabatar wa duk shekara.

 

Kungiyar Fityanul Islam Initiative Of Nigeria tana kasa sanar da daukacin yan’uwa masu zuwa taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA dasu kasance masu bin dokokin hanya tare da addu’an Allah ya kiyaye, ya kuma tsare mana hanya.

 

Za’a gudanar da taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA, ne kamar haka;

 

– Rana: 27/Rajab/1444 – 18/02/2023.

– Wurin: Filin sukuwa, jihar Kebbi

– Lokaci: karfe 10:00 zuwa 1:00pm

 

Allah ya bada ikon halartan taro. Amiin

 

Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button