Za’a Gudanar Da Gagarumin Taron Mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani RA Karo Na Takwas (8) A Jihar Bauchi.

Za’a Gudanar Da Babban Taron Mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani RA A Garin Bauchi.

 

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi RA zata gudanar da gagarumin taron bikin Mauludin Sheikh Sharif Ahmadu Tijjani RA (shugaban Darikar Tijjaniyya) karo na Takwas (8) a birnin Bauchí jihar Bauchi don tunawa da haifuwar jagoranmu Sheikh Ahmadu Tijjani RA a karkashin jagoranci Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.

 

Taron Mauludin zai samu halartan manyan baki daga sassa daban-daban na fadin duniya kamar yadda aka saba gabatar wa duk shekara

 

Cikin wadanda zasu samu halartan kamar haka

 

– Babban Khalifah Tijjaniyya na duniya Sheikh Khalifa Ali Bel Arabi daga kasar Algeria.

 

– Babban Khalifah Faidah na duniya Sheikh Khalifa Muhaammadu Mahy Niasa daga Senegal,

 

Tare da wasu manyan sharifai, da malamai da kuma muqaddamai daga sassa kasar mu Najeriya dama fadin duniya baki daya.

 

BABBAN TARO ZAI KASANCE KAMAR HAKA:

 

– Rana: Asabar 03/09/2023.

 

– Wurin: Filin wasa na Sir, Abubukar Tabawa Balewa dake cikin garin Bauchí, jihar Bauchi.

 

– Lokaci: Karfe 10:00 zuwa 1:30 na yamma

 

Allah ya bada ikon halartan taro. Amiin

 

Daga: Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button