Za’a Sanya Wa Sabuwar Kafatare Kasuwa Zamani Sheikh Gibrima Guru A Jihar Yobe

LALLAI WANNAN KASUWAR ZATA RABAUTA DA ALBARKAR MA’ABOCIN ALBARKA.

 

Ko da yake ba’a sanar a hukumance ba, amma labarin ya matukar faranta mana rai, ayayin da mai bushara yayi bushara ga ‘yan uwa cewa “Sabuwar Kasuwar Zamani da Gobna Mai Mala Buni ya gina a manyan Local Government guda hudu da birninsu Gashua, to ta garin Nguru da yardar ALLAH za’a sanya mata sunan hamshakin Shehin da Gabas da Arewa kudu da Yamma ta cika da amon sunansa, da dimbin alkairansa, wato Maulanmu Sheikh Muhammad Ngibrima (R.T.A).

 

Babu shakka a garemu wannan abin farin cikine, domin sai wanda yake kaunarku, yasan kimarku, shine yake ganin darajar magabacinku, har ya iya tunanin ganin ya karramashi da irin na su karamcin.

 

Hakika suna Lamirine, muddin wannan batu ya tabbabta, to lallai wannan Kasuwar zata matukar rabauta, domin lallaine duk abinda ya rabi Waliyan ALLAH, to albarka bai yanke masa.

 

ALLAH YA KARFAFI WANNAN JAGORA CIKIN ABINDA YAKE NA DAI-DAI, YA GAFARTA MASA NA KUSKURE.

 

ALHAMDULILLAH.

 

Daga: Muhammad Usman Gashua

Share

Back to top button