ZIKIRIN JUMA’A: Yadda aka gudanar da Zikirin Juma’a da yiwa kasa addu’a a fadar Sarkin Kano.

An gabatar da zikirin juma’a tare da yiwa kasa addu’oin a fadar mai martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Abdullahi Bayero kamar yadda aka saba gabatar duk shekara

 

Sheikh Ibrahim Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi (R. T. A) shine ya jagoranchi zaman addu’oin tare da zikirin juma’a daya gudana a garin na Kano.

 

Taron ya samu halarta Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Abdullahi Awais Limanci, Khalifa Sani Shehu Mai Hula, Khalifa Sayyidi Bashir Zangon Barebari, Khalifa Hassan Kafinga, Dr. Nasidi Abubakar Goron Dutse, Dr. Lawi Sanka Da kuma.

 

Alhaji Nafi’u Khalifa Isiyak Rabi’u, Imam Nasir Adam, Goni Yusif Lajin Khalifa Isiyak Rabi’u, Imam Dayyib Dan Almajiri, Malam Balarabe Dan Musa da sauran Shehunai, Mukaddamai, Sharifai, Zakirai da yan uwa Sha’irai masu yabon Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya jagoranci taron zikirin juma’a da yiwa kasar Nigeria addu’a.

 

Allah ubangiji ya karawa kasarmu zaman lafiya ya kawo mana saukin rayuwa. Amiin

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button