ZIYARA: BBC Hausa Ta Ziyarci Kabarin Sheikh Ahmadu Tijjani RTA A Kasar Morocco.
BBC Hausa ta kai ziyara kabarin Shehu Tijjani a Morocco
Daga BBC Hausa 31/8/2022.
Birnin Faaz na kasar Morocco na daya daga cikin wurare muhimmai da mabiya darikar Tijjaniyya a fadin duniya ke son kai ziyara, saboda a can ne hubbaren shugaban darikar na farko, Sheikh Ahmadu Tijjani yake.
Tafiya ce ta sa’a uku zuwa da rabi a jirgin kasa, a mota kuma sa’a hudu da doriya za ta kai ka birnin mai nisan kilomita 387 daga Rabat babban birnin kasar.
Tun kana ganin gine-gine a hanya har sai ka fara ganin hamada tsagwaronta.
Da ka doshi garin Fez, za ka fara ganin tsarin tsofaffin gine-gine irin na kasar Misra, dogayen katangu na ginin kasa da Larabci ana kiran Fez Madina Qadima wato tsohon birni.
Masana tarihi sun ce an kafa shi tun a karni na 9 kuma mutanen Tunisiya da Andalus wato Sifaniya da na Portugal ne suka kafa garin.
Lunguna ne da kwane-kwane za ka bi kafin ka karasa inda wannan Zawiya take.
Doguwar katanga ce samanta da katuwar hasumiya, mutane na shiga a kodayaushe, mun isa wurin daf da kiran sallar la’asar.
Masu yin wazifa a masallacinn sun gaje ta ne daga koyarwar Shehu Tijjani da aka haifa a garin Aini Madi a Algeriya a shekarar 1150, ya kuma rasu a 1230.
Kakan Shehu dan asalin wata kabila ne da ake kira Tijjana, asalinsu Morocco daga baya suka koma Algeriya, sannan shi da kansa ya kara komawa Morocco.
Muhammad Idris shi ne limamin masallacin zawiyar, ya ce babu wani abu a darikar Tijjaniyya sai zikiri da Hailala.
Sharifi ne shi gangariya, asalinsa na komawa ne ga Hassan dan Sayyadi Ali mijin Nana Fatima.
Limamin ya ce an gina darika ne kan abubuwa uku, Istigfari da Salatin Annabi da kuma hailala, kamar yadda kowacce darika take, Tijjaniya ba ta bukatar sanya wasu tufafi na daban, ko takurawa mutum kan sha’anin rayuwarsa.
”Ya tafiyar da rayuwarsa ne kan kira zuwa ga Ubangiji, kan ilimi da ba da shi, karatun kur’ani da sauransu. Ya haddace littatafai da yawa kamar su Sahihu Bukhari da Muwadda. Yana da ilimi na fikihu, da kuma na shari’a.