Karin Bayani Akan Karin Limami Da Akayi A Central Mosque FCT Abuja.
Tare Da da Maulana Sheikh Prof. Ibrahim Maqari (H).
Allah Ya Tabbatar Damu Akan Lamarin Duniya Da Lahira. Amiiiin Yaa ALLAH
Karin Bayani Akan Karin Limami Da Akayi A Central Mosque FCT Abuja.
Tare Da da Maulana Sheikh Prof. Ibrahim Maqari (H).
Allah Ya Tabbatar Damu Akan Lamarin Duniya Da Lahira. Amiiiin Yaa ALLAH
Yanda aka gudanar da Wazifa da Zikirin juma’a dake Masallacin Sa’adu Bn Abi Waqas dake birnin Gwanzu A Kasar China
A ranar juma’a ne 18/10/2024 aka bude wazifa da Zikirin juma’a wanda gidauniyar Maulana Sheikh Dahiru Bauchi OFR ta jagorancin budewa a birnin Gwanzu dake kasar China wanda sahabin Manzon Allah SAW ya gida tun lokacin rayuwar sa wato Saad Bn Abi Waqas.
Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Khadimul Faidha) shine ya jagorancin bude wazifa a ranar juma’a tare da Zikirin juma’a.
A shekarun baya Sheikh Ibrahim Inyass Al-Khaulaq RA ya taba ziyartan masallacin a lokacin da ya kawo ziyara kasar China, kamar yanda Shehu ya fada a DIWANIN sa.
Allah ubangiji tabbatar mana da alkhairi ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW. Amiin Yaa ALLAH.
Daga: Tijjaniyya Media News
KARAMAR SHEHU ABULFATHI
Yana daga cikin karamar da Allah ya yiwa Maulana Shehu Ahmad Abulfathi RTA, ya keɓance shi da wasu halaye sannan ya gadar da halayen ga dukkanin Almajiran sa da masoyan sa na gaske, halayen sune:
1. RASHIN JAYAYYA: Duk wanda ka gani a halarar Shehu Abulfathi, daga ya’yan sa zuwa almajirai da masoya, ba zaka same su da jayayya ko musu akan abinda bai shafe su ba, shiyasa ake cewa suna da taurin kai, saboda duk abinda shehi ya tarbiyantar dasu a kai, ba zasu saki su kama na wani ba.
2. KAWAR DA KAI: Sam ba zaka same su da kula da aibonin jama’a ba ballantana su dinga zurfafa bincike don tono aibobin, in a gaban su zaka yanka ka soya ka cinye, ba zasu kalle ka ba ballantana su kai maganar ka wurin wani.
3. WADATAR ZUCI: Yana wahala ka same su da bibiyar mutum don abin hannun sa, hasalima komi talaucin su a zahiri, kallon wadatattu ake musu saboda sirrin wadatuwar halarar Shehu Abulfathi RTA.
Wallahi ban dauke maka kowa ba, duk wanda yace maka ya jingina da Shehu Abulfathi kuma ka same shi yana musu da mutane akan sha’anin rayuwa ko addini, ko ka ga yana bibiyar aibobin mutane, ko ka ga yana yawan roƙo da shishigi ga masu kuɗi ko mulki, to ɗayan biyu ne, Imma dai ƙarya yake yi bai da alaƙar ruhi tsakanin sa da shehi, ko kuma halarar shehi bata tare dashi (salbu), Allah ya tsare mu.
ALLAH KA ƘARA MANA SOYAYYAR SHEHU ABULFATHI NA HAKIKA, KA GADAR MANA DA SIRRIN SA. Amiiiin Yaa ALLAH
✍️ Sidi Sadauki
Za Ka Iya Yin Komai Don Mauludi Matukar Ba Sabon Allah Ba Ne
— Sheikh Dr. Yusuf Ali
December 17, 2017, 10:3064
TAMBAYA:
Akrimukallah, wanne kira za a yi wa matasa kan maulidi?
AMSA:
Abinda malamai su ke cewa shi ne duk wani abu da za ka yi game da murna da haihuwar Manzon Allah (SAW) in dai bai sabawa addinin Muslunci ba kamar ya zama na cewa wasu maganganu ne na batsa ko kuma wasu maganganu ne da ba su da dangantaka da addinin Muslunci ko kuma a samu gwamutsuwa da cudanya tsakanin maza da mata ko kuma za a yi wasu abubuwa na sha kamar shaye-shaye ko wasu abubuwa na munkari in dai ba wadannan za a yi ba to ana so a yi Mauludi. Maulud ya zama mustahabbi ne duk abinda malamai su ka bayyana.
Ko a yanzu babu wani malami da zai budi baki ya ce mauludi ba kyau sai dai ya ce a na yin wasu abubuwa da bai dace ba wannan kuwa ko a musabakar Kur’ani koma a hailala ne abin da bai dace ba bai dace ba. Misali idan ka ce a Musulunci akwai mashaya akwai mazinata sai kuma ka ce a daina Musuluncin? In kai haka baka yi wa muslunci da Musulmin kwarai adalci ba. Sai dai a ce a gyara.
Mutane a gidajensu suna murnar zagayowar ranar haihuwar ‘ya’yansu ba kuwa ma da an tabbatar da salihancin dan ba bayan ya girma hatta aure in shekarar da aka yi shi ta zagayo sai a taru a yi murna. A majalisar dinkin duniya suna ware ranaku da ake tunawa ko a tunasar a ciki misali ranar mata ta duniya ranar ma’aikata ko a shekaran jiya an yi ranar masu ciwon Kanjamau . Wadanda ke cewa mauludi ba kyau wasu mutane ne da suke da wata manufa ta a sansu wanda in ba sun ware ba a za a san da su ba.
Matasa ya kamata su lura da irin duk wadannan abubuwa musamman a soshiyal midiya inda kowa Malam ne babu hujja babu komai mutum ya kafirta mutane inda in bayan maulidin ba za ka iya kama su a wani abin ba kamar sallah ko azimi ko zakka ko a karatun kur’ani ko a aure ko yadda suke kasuwanci ko mu’amalarsu ko iliminsu da sauransu in haka ne sai ka yi adalci tunda shi maulidin ba ka san shi ba amma ka san wadancan dai-dai suke sai ka sallama ko ka yi shuru. Matasa ya kamaa su sani Allah subhanahu wata’ala yana fada a suratu Yunus “Ka ce da Falalar Allah da rahmarsa da shi za su yi farin ciki ya fi duk abin da su ka tara”.
Falalar Allah an ce Kur’ani Rahmarsa shi ne Manzo Sallallahu alaihi wassalama. Abinda mu ke so matasa su sani kar ya zamana tunda an ce mauludi son Annabi ne to a yi shi ta kowacce siga ba, a’a a tsaya a binda ake cewa Hudud, wato iyaka ta shari’a don kuwa idan ka shigar da wani abu da ba na shari’a ba za a yi ma hisabi a binda ka shigar.
Haka Danfodiyo ya fada haka Ibn Hajj Al-Madkhal ya fada.Wadannan sun ce indai mauludi ba wani abu na keta shari’a to ya halatta . Malamai sun yi wallafe-wallafe inda suke cewa duk inda aka yi mauludin Annabi Allah zai raba wannan wajen da annoba da duk wani abu na ka-ka-ni-ka-yi da duk wani abu da yake ba na farin ciki ba kuma Allah zai yalwata su. Mai yin mauludi yana baiyana son Annabi ne kuma Allah subhanahu wata’ala a suratu dhuha y ace “ Idan Allah ya yi maka wata baiwa ka bayyanawa mutane” wannan ba riya ba ne ba yanda za a yi ka bayyana in ba ta haka ba. Ba yanda za a yi kana son abu ka iya boyewa.
Misali, ko da budurwa ka yi za ka fadawa abokinka ko wani na kusa in har kana sonta ba za ka iya daurewa ba, kuma da zai fadi wani abu na kushe kanta ta ba za ka ji dadi ba. Don haka ya na daga hanya ta nuna son Annabi shi ne ranar da aka haife shi ko watan da a ka haife shi ko kai kadai ne ko kai da abokanka ko da iyalanka ko ‘yan’uwanka ku hadu ku nuna soyayyarku gare shi. Annabi Muhammad SAW yace “ Ba wanda yai imani sai wanda ya zama yana sonsa fiye da iyayensa fiye da ‘ya’yansa fiye da dukiyarsa fiye da ransa tukunna.”
Kenan Annabi (SAW) bai kebe wata hanya da za a nuna kaunarsa ba ko za nuna farin ciki da samuwarsa ba. Ya ragewa kowa ya yi tunaninsa sai dai kada ya kauce wa shari’a. In har ba ka yi murna da haihuwar Annabi ba to gaba za ka yi ko bakin ciki ? dole in kana sonsa ba ka kinsa in kana kinsa ba ka son sa saboda fadin Allah subhanahu Wata’ala y ace “ Bai sanya wa mutum zuciya biyu ba a cikinsa ba.”
Wanne darasi mauludi ke koyarwa?
Abubuwan da a ke fada kyawawan halayen Annabi (SAW) shi ne babban darasin da a ke so a dauka a mauludi bayan soyayyar kanta da ake nunawa ana ambaton Hakuri inda ake kawo wa daga tarihinsa yadda ya sha wahala wajen kira amma ya yi hakuri. Annabi (SAW) ya na kallo gumaka a ke bautawa 360, amma bai ce zai yi fito-na-fito ba da mutane har sai da ya sami dama, ko da ya sami damar ma ya shiga Makka rushe su kawai ya yi kuma yace duk ku tafi an sake ku.
Annabin da yake da yafiya irin wannan shi ake cewa a yi koyi da shi . Annabin da ya kasance babu wanda ya kai shi kykkyawar mu’amala a tsakaninsa da Allah babu wanda ya kai shi kyakkyawar mu’amala a zamantakewar iyali in dai har ya zama akwai wanda ake ba wa wani kambun girmamawa a duduniya to kuwa Annabi Muhammad shi ya cancanta. In har akwai wanda za a girmama a fadi halinsa don a yi koyi da shi to Annabi Muhammad (SAW).
Annabin da ya kawo shiriya gaba ki daya a duniya wanda duk halinsa na kirki ne wanda duk duniya an hadu da musulmin da kafiran in dai a kyan hali ne an yarda ba wanda ya fi shi. Kowanne aiki na alkahiri ba wanda Annabi Muhammad (SAW) bai yi ba ko bai umarni da shi ba. Darussan su na da yawa sai dai mu ce, kulli aamin wa antum bi khairin.
SIRRIN AYATUL KURSIYYU NA SAMUN BIYAN BUƘATA KOMAI GIRMANTA DA IZININ ALLAH.
Assalamu Alaikum.
Ayatul kursiyyu, aya ce wacce take da ƙarfi da tasiri sosai, wajen biyan buƙata. Aya ce wacce ake tasarrafin ta ta hanyoyi da dama kama daga, dafa’i, jalabi magani musamman abun da ya shafi, jinnu miyagu iska kambun baka da dai sauransu.
Babu wata aya, a cikin alƙur’ani mai girma da ta kai wannan ayar mai albarka ta Ayatul kursiyyu Tana ɗauke da manya manyan sirrukan wanda in Sha Allahu yau gamu ɗauke da wani babban sirrin ta, na samun biyan buƙata a wajen ALLAH.
YADDA ZA AYI AIKIN.
Ana farawa kowacce rana, amma sai za a kwanta bacci, sai ayi alwala a zauna a kalli alƙibla, a fara da yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati gwargwadon iko, sai a karanta wannan ayar mai albarka ta (Ayatul kursiyyu) Ƙafa. (305)
Bayan an kammala sai a sake yiwa Annabi salati gwargwadon iko ana yin wannan sirrin ne na tsawon kwana bakwai insha Allahu duk buƙatar da aka tunkara da wannan sirrin mai ƙarfi insha Allahu za’a samu biyan buƙata.
ALLAH YA BIYA, MANA DUKKAN BUƘATUN MU, NA ALKHAIRI AMEEN YAA ALLAH
Sadakar wannan, sirrin shi ne ayi comment da salatin ANNABI (S.A.W) ayi share da like domin ƴan-uwa, su amfana.