ADDINI NASIHA

  • Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da sababbansa, da duk wanda yake biyayya ko koyi da abin da ya bari.

    SON ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA IMANI NE.

     

    Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da sababbansa, da duk wanda yake biyayya ko koyi da abin da ya bari.

     

    Duk wanda babu soyayyar ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA a ransa ko Yaji soyayyar wani tafi ta ANNABI a ransa, To Ya binciki imanin sa.

     

    A cikin Hadisai Guda 2 ANNABI ya sanar da mu. “Babu dayan ku da zai zama yana da imani

     

    Sai ya zamo yafi kauna ta fiye da kansa, mahaifinsa/mahaifiyar sa, Ko dansa/’yarsa da sauran mutane.”

     

    Mutane sun hada da malaminka/oganka/ mai kula da kai, ko wanda ya ke ba ka kariya cikin mutane in ka shiga kunci ko damuwa.

     

    Muyi koyi da ayyukan ANNABI da maganganun sa, Duk wanda ya saba da Umarnin da ANNABI (S.A.W) ya bayar, ko waye! kabi ANNABI ka kyaleshi.

     

    Muyi tutiya da son ANNABI (S.A.W) kuma ku bayyana shi a ko ina, a ko da Yaushe.

     

    Domin yafi kaunar da mu ke tutiya da ita ta matan mu, iyayenmu, ‘Ya’yanmu, da Makusantan mu.

     

    Yin salati ga Annabi yana cikin kauna da soyayyar sa.

     

    Mu yawaita salati gareshi.

     

    Allah ya kara mana son ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA. Amin.

    Share
  • KASUWANCI A MUSULUNCI TARE DA FARFESA IBRAHIM MAQARY.

    MAULANA PROF IBRAHIM AHMAD MAQARI ZARIA CHIEF IMAMS OF NIGERIA

     

     

     

    ALLAH YA KARA MASA LAFIYA DA NISAN KWANA BIJAHI SAYYIDUNA RASULULLAH ﷺ. AMIIIIN YAA ALLAHU

     

     

    GAME DA KASUWANCI A MUSULUNCI.

    Share
  • IBN TAIMIYYA MAKIYIN ANNABI NE. SHINE YA FARA HANA TAWASSALI DA MANZON ALLAH SAW.

    IMAM JUNAIDU ABUBAKAR BAUCHI YA FAYYACE WAYE MALAMIN DA YA SOMA KARANTAR DA KORE TAWASSALI DA MANZON ALLAH (S.A.W) A TARIHIN MUSULUNCI.

     

     

    Sheikh Imam Junaid Abubukar Bauchí cikin karatun sa wanda ya saba gabatar duk sati ya bayyana Ibn Taimiyya a matsayin wanda ya fara kore yiwa Annabi Muhammadu sallalahu Alaili Wasallam tawassali a tarihin Musulunci a duniya.

     

    Allah ya kara mana soyayyan Annabi Muhammadu Sallallahu Alaili Wasallam, kuma muna tawassali da Annabi ﷺ Da alkur’ani mai tsarki Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, ya bamu Aljannah. Amiin

     

    Tijjaniyya Media News

    Share
Back to top button