ALLAHU AKBAR: Khuɗubar Annabi S.A.W Ta Ƙarshe Da Yayi Wa Al-ummarsa A Ranar Arafat 9 Ga Watan Zul-Hijja.
Daga Zaharaddeen Gandu
Annabi Muhammad S.A.W yayi khuɗubar ta ƙarshe ga al-ummarsa a ranar Arafat 9 ga watan Zhul-Hijja, ya yi khuɗubar a shekarar10 bayan Hijrarsa daga Makkah zuwa Madina.
Ya gudanar da Khuɗubar a saman Dutsen Arafat, wadda wannan khuɗubar ta kasance khuɗubar ƙarshe ta Manzon Allah S.A.W, inda Fiyayyen Hallita ya cigaba da khuɗubantar da al-ummarsa cewa;
“Ya ku mutane! Ku bani hankalinku domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka! ku saurari abin da nake gaya maku da kyau kuma ku isar da abin da zan gaya maku ga waɗanda basa wannan wuri a yau”.
“Ya ku Mutane! kamar yadda kuka riƙi wannan Wata na Aikin Hajji da wannan rana ta Arfa, da kuma wannan gari na Makka da girma kuma abin tsarewa, to haka kuma ku riƙi ran Musulmi da dukiyoyinsu da girma abin karewa”.
“Ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana, kar ku cuci kowa, kar ku yi zalunci, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, haƙika Allah zai yi sakayya a kan ayukakanku, Allah (SWT) ya hana cin riba, (wato kuɗin ruwa) saboda haka duk abin da aka ƙulla ta kuɗin ruwa sai an warware shi”.
“Ku yi hattara da Shaiɗan domin kiyaye Addininku yanzu kan ya fidda ran ɓatar da ku a kan manyan abubuwa na saɓo, saboda haka ku guji bin shi a kan ƙanana”.
“Ya ku jama’a haƙiƙa kuna da haƙƙi bisa matayenku amma suma suna da haƙƙi bisa kanku, to haƙƙinsu ne a kanku da kuciyar da su sannan ku tufatar da su a kan jin ƙai. Ku bi da su kyakkyawar biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majiɓintan al-amurran ku ne kuma mataimakan ku, hakki ne a kansu da kar su yi abota da duk wanda ba ku so kuma su nisanci zina”.
“Ya ku jama’a ku yi kyakkyawan bauta ga Allah (SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, ku azumci watan Ramadan, ku bada Zakka, ku aikata Aikin Hajji in har kun sami damar yi”.
“Ku sani fa, ko wanne musulmi ɗan uwan Musulmi ne, dukkan ku dai-dai kuke da juna