BIDIYO

  • BIDIYO 🎥; Wata Hira Mai Matuƙar Muhimmanci Tare Da MAULANA SHEIKH DAHIRU BAUCHI (R.A).

    MAULANA Lisanul Faidah Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.

     

    Daga Taskar BABBAN MALAMIN MUSULUNCI KUMA SHEHIN DARIKAR TIJJANIYYA MAULANMU SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI (R.A).

     

     

    Wata Hira Mai Matuƙar Muhimmanci Tare Da MAULANA SHEIKH (R.A).

     

    Anyi Wannan Hiran Ne Da Gidan TV A Shekarun Baya, Akan Al’amuran Yau Da Kullum Tare Da Fadakarwa Akan Addini.

     

    ALLAH Ya Ƙara Muku Yarda. Amiin

    Share
  • Biyayya Ga Manzon Allah SAW Shine Biyayya Ga Allah Subhanahu Wata’ala. Inji Sheikh Ibrahim Maqari.

    ALLAH YA KEBANCI ANNABI MUHAMMADU S.A.W. DA WASU DARAJOJI AKAN SAURAN ANNABAWA BA.

     

    An karbo hadisi daga “Jabir Dan Abdullah R.A. cewa Annabi Muhammadu S.A.W. Yace:

     

     

    “An bani wasu abubuwa guda biyar (5) wadanda ba a ba dasu ba ga wani Annabi da yazo gabani naba:

     

    1. An taimake Ni da tsorata abokan gaba wadanda tsakanina dasu akwai nisar tafiyar wata guda.

     

    2. An sanya min kasa ta zamo tsarkakakkiya (wajen yin taimama) kuma gurin sallah, don haka; duk wanda sallah ta riske shi a hanya sai ya tsaya yayi.

     

    3. Kuma an halattamin cin ganima wacce bata halatta ba ga wani Annabi daya zo gabanina ba.

     

    4. An bani damar yin ceto (a farfajiyar kiyama).

     

    5. Annabawan da suka zo gabani na sun kasance ana aiko sune zuwa ga mutanensu kawai; Amma Ni kuwa an aiko Ni ne zuwa ga mutane baki daya kai har da dabbobi ma”. [Bukari Da Muslim Ne Suka Ruwaito Shi].

     

    Ya zo a cikin Sahihu-Muslim a Hadisin Anas R.A. cewa Annabi Muhammadu S.A.W. Yace: “Nine farkon wanda zai fara yin ceto ranar kiyama, kuma nafi dukkan Annabawa samun mabiya ranar kiyama”. “Nine kuma zan fara kwankwasa kofar Aljanna don a bude”. Ya zo a hadisin Abu-Huraira R.A. Cewa Annabi Muhammadu S.A.W. Yace:

     

    “Nine shugaban ‘Yan-Adam” ranar kiyama. “Kuma Nine farkon wanda zai fara fitowa/tashi daga kabari ranar kiyama”.

     

    “Nine kuma farkon wanda zai yi ceto, kuma farkon wanda za’a bashi damar yin ceto”. Allah Ka Bamu Albarkacin Annabi Muhammadu S.A.W.

     

    Daga: Kamal Sa’eed Ibrahim

    Share
  • DANGALE WANDO BA SUNNAH BANE RA’AYINEE!!! INJI IMAM JUNAID BAUCHI

    Dangale Wando Ba Sunnar Manzon Allah SAW Bale, Ra’ayine. …Inji Imam Junaid Bauchi.

     

    Matashin malamin addinin Musulunci a Nigeria Sheikh Imam Junaid Abubukar Bauchi kuma (Limamin Masallacin Al’irfan) ya bayyana cewa dangale wando ba Sunnah Manzon Allah SAW bale ra’ayine.

     

    Imam Junaid Bauchi ya bayyana hakan ne a karatun da yake gabatar wa na littafin Shama’ilul Muhammadiyya duk sati a masallacin Al’irfan dake birnin Bauchi. Ya kawo hadisan Annabi Muhammadu SAW tare da bayyana cewa Manzon Allah SAW bai saka wando ba, kuma a lokacin rayuwar sa akwai masu saka wando.

     

    Read More »

    Share
  • BIDIYO: ZAFFAFAN RADDI GA BASALAFE DR, BIRNIN KUDU DAGA KHALIFA MADATAI

    ZAMANI YA FICE DA IRIN WANNAN YAKAR TUNANIN ZAI SAKE YIN TASIRI YAKAI Dr. B/KUDU

     

     

    Babu wata Al’umma da zata tsira daga tawaya, muddin gurbatattun cikinta ko jahilan cikinta ko kuma raunanan cikinta sune zasu zamo ababen kafa hujja akanta daga barin kafa hujja akan ayyukan nagartattun cikinta, da kuma gaskiyar abinda yazo cikin koyarwarta da aka nakalta daga Malamai ma’abota ilmi da fahimta, ba Malaman Bariki yan neman Followers ba

     

    Cewa “Abinda Yan Hakika sukeyi, na Allantar da bayi, tare da yaki da iyakokin ALLAH shine gaskiyar koyarwar Tijjaniyya” wannan zance nuni yake da tsantsar son zuciya, da kuma abin kunya ga mutum irinka wanda ke tutiya da lakabin “Dr.”.

     

    A matsayinka na Malami, idan zakayi zance akan hanyar wasu al’umma, littafin Malamanta zaka dauko, kace abu kaza da mabiyanta suke aikatawa ga inda suka koya, ba haka kawai zaka yiwa mutane hawan kawara ba.

     

    SABODA HAKA, YA DAI KAMATA A WAYE, A NEMI ABIN YI DAGA BARIN AIBATA MUTANE BA BISA HUJJA BA.

     

    ALLAH Ya Shirye Mu. Amiiiin Yaa Allah

     

    Daga: Muhaammadu Usman Gashua

    Share
  • BIDIYO: ,🎥 TARIHIN SHEIKH MUHAMMADU NGIBRIMA NGURU

    Share
Back to top button