DARIKA

 • Hadisi Shine Zance Wanda Ya Iso Daga Wurin Annabi SAW Wanda Ba Wahayin Qur’ani Bane…

  SAHIHIN HADISI A WURIN SUFAYE

   

  A bisa tsarin ilimin zahiri na shari’ar musulunci, hadisi shine zance wanda ya iso daga wurin Annabi SAW wanda ba wahayin qur’ani bane, dauke da umurnin aiki ko hani ko nasiha ko wanin haka daga gareshi sallallahu alaihi wa sallam.

   

  Hadisi yana zama ingantacce ne ta hanyoyin da aka samo shi daga wurin Annabi SAW, wato tabbacin ruwayar sa ta hanyar lura da kamalar wayanda suka ruwaito, tun daga kan sahabbai zuwa tabi’ai da sauran su.

   

  Amma a wurin sufaye, hadisi yana zama ingantacce ne in har suka sadu da Annabi SAW cikin barci ko ido da ido ya sanar dasu ko suka tambaye shi akan hadisin da aka ruwaito daga gareshi kuma ya gaskata eh lallai haka ne.

   

  Da yawa hadisan da zaka gani a litattafan sufaye, babu shi ko kuma ya sha banban da na sauran malaman zahiri wayanda suka farauto ilimin su daga littattafan magabata kawai babu saduwa da Annabi SAW. Shiyasa za kaga waliyi yace “Qala rasulillahi SAW …” babu an wane haddasana wane kaza da kaza, saboda direct daga Annabi ya samu wannan zancen babu wani a tsakani.

   

  Duniyar musulunci ya samu dawwamammen tsarki ne saboda kasantuwar sufaye cikin kowani zamani.

   

  Bayan wafatin Annabi SAW, an ruwaito wasu hadisai na qarya, an boye da yawa na gaskiya, anyi wa wasu ragi da qari, saboda son mulki ko kiyayya ga Addinin Allah, an kuma tilastawa magabata koyar da hakan ko kuma a bakin ransu, wasu sun yi, wasu sunyi shahada.

   

  A yau, babu inda za kaje a sanar da kai haqiqanin saqon Allah da manzonsa tun daga tafsiri zuwa hadisi da fiqhu sai wurin ma’abota saduwa da Annabi SAW wato sufaye.

   

  Nayi wannan rubutu ne saboda matasa masu shauqin neman ilimi musamman akan hadisi da fiqhu, toh kar ku rabu da tafarkin sufaye.

   

  Akwai maganganu na addini da dama wanda in kaji shi, muddin kana da tsarkakakken imani, kasan akwai rashin ladabi ko kiyayya ko tawaya cikin sa ga addinin Allah.

   

  Hankalin ku, jagoran ku!

   

  Amma mu a sufanci, ba hankali ke mana jagora ba, hasken imani ne.

  Sidi Sadauki

  Share
 • SU WAYE ƳAN HAƘIƘA NA GASKIYA CIKIN DARIKAR TIJJANIYYA ??

  SU WAYE ƳAN HAƘIƘA?

   

  Gargadi: wannan rubutun bashi da alaƙa da wani bayan ni.

   

  Babu wani abu da ke kawo saɓani da haifar da rabuwar kai cikin masu da’awar FAIRA da kuma ƴan FAIRA na gaskiya kamar kalmar HAƘIƘA. Yayin da wasu suka yi wa wannan kalmar mummunar fahimta saboda wasu dalilai da suka bayyana musu a zahiri, misali yadda ake sifffanta wasu mutane masu wani aiki da ya saɓawa shari’ah da ƴan hakika, da kuma yadda gama garin mutane suka fahimce ta kuma suke fassara ta.

   

  Abu mafi al’ajabi shine, har cikin da’irar ƴan FAIRAR na gaskiya, wasu sun wayi gari suna kyamar wannan kalma, kuma basa so ko da wasa a alaƙanta su da ita balle a jingina musu.

   

  Cikin wasiƙar da Shehu da yayi ta Risalatul Muntaqim, ya ambaci cewa akwai matasa da tuni sun manta ɗanɗano na sha’awa kuma har ta kai ga akwai wanda har manta matan su ma na Aure suke, saboda tsanin zauƙi da suka samu na Allah, basa zuwa wajen matan ma sai an musu izinin su tafi, wasu ma sai da tilastawa, saboda sun bar komai, da kowa, sun tare a wajen Allah. To wannan wata siffa ce ta ƳAN HAƘIƘA na gaskiya. Wannan kuwa ya saɓa da HAƘIƘAR da mutane ke da’awa yanzu wacce sha’awar ce ma ke musu jagoranci.

   

  Saboda tsabar daɗin zauƙi na Allah da ƴan HAƘIƘA suka samu, to ni ban san masu kyautatawa halittu zato ba da kuma cikakkiyar himmar Wuridi da ƙarin nafiloli bayan na Farilla, da zama da kowa tsakani da Allah, wannan kuma ya samu asali ne saboda sirrin da suka riska na maida komai asalin sa, da kuma ganin komai a asalin sa har ma da fahimtar hikimar komai cikin nufin mai komai.

   

  Idan wasu suka ɗauka cewa HAƘIKA iskanci ce, da raina Allah da Manzonsa, da kuma keta shari’ah, to lallai za’a iya musu uzuri bisa lura da yadda wasu masu da’awar wannan tafiya suke, wanda ba ɓoyayye bane.

   

  Shi ɗan Haƙiƙa na asali idan aka ambaci Allah akwai wanda sai yayi mintoci bai ma san inda yake ba, saboda nauyin girman Allah da ke zuciyar sa, duk ɗan HAƘIƘA na gaskiya idan aka ambaci Manzan Allah fita yake cikin hayyacin sa, saboda an cire masa nustuwa da tunanin duk wani abu bayan Manzan Allah, wannan kuma shine haƙiƙanin nutsuwar zuciya.

   

  Su ƴan HAƘIƘA na gaskiya sun gama narkewa cikin Allah, jin su, ganin su, tafiyar su, da kuma ɗamkar su duk da Allah su ke, kamar dai yadda Hadisi ingantacce ya tabbatar. Sun bawa Alllah dukkanin su, saboda haka sai Allah ya zama komai na su. Basu da komai sai Allah, basu san komai ba sai Allah, kuma basa sha’awar komai sai Allah.

   

  Allah ya yarda mu zama ƳAN HAƘIƘA na gaskiya. Amiin Yaa ALLAH.

   

  Ibrahim Sabo Al-Musaddady

  Share
 • DOLE MASU ILIMI NE ZASUYI JAGORANCI A ADDINI MUSAMNAN TIJJANIYYA.

  KHALIPHA FATIHU SHEIKH MUHAMMADU GIBRIMA.

   

  DOLE MASU ILIMI NE ZASUYI JAGORANCI A ADDINI MUSAMNAN TIJJANIYYA FAIDAH.

   

  MU TARU MU GAYAWA KAN MU GASKIYA DAN MU GYARA.

   

  Jawabin Maulana Khalifah FATIHUL AGLAQ da ke cikin Recordin ‘DIN.

   

  1. Abubuwan da su ke faruwa ba qaramun damun mu su ke ba – inji Shehu Fatihul Aglaq (RTA).

   

  2. Sai ya ba da misalin abubuwan da suke damun na su kamar haka.

  A. Rataya hoto ana yawo da shi

   

  B. Tara suma ta zamo ita ce abin ado

   

  C. Daukar motoci ana yawon ZIKIRI ba karatu

   

  D. Zaman addu’a da Sallah a Qabarburan Bayin Allah

   

  E. Fifita Shehu Ibrahim RA akan Annabi Muhammadu S.A.W (kowa yasan akan suwa yake ramzi).

   

  F shafe Sallah.

   

  3. Sannan sai ya yi kira ga masu wa’azi Har SAU HU’DU da su dinga yi musu wa’azi saboda abin ya zamo masifa.

   

   

  4. Ya koka matuqa akan abinda ya ke faruwa na waqi’ar Abdul Inyass (L. A), Saboda fifita SHEHU IBRAHIM Inyass (RTA) da ake akan Annabi Muhammadu S.A.W.

   

  5. Ya cigaba da cewa Ko zamanin Shehu Gibrima da Halifa ba su ga ana al’adar TARA Suma da yawon ZIKIRI ba KARATU ba.

   

  7. Ya kara jaddadawa cewa duk fa wani mai daraja ya samu darajarsa ne da Annabi Muhammadu S.A.W.

   

  8. Sannan ya yi magana akan ziyarar RAUDAR BAYIN ALLAH da ake, da kuma abubuwan da ake na rashin kyautatawa.

   

  9. ya ta6a sawa an RUFE WAJEN ZIYARA (RAUDAR SHEHU GIBRIMA) saboda abubuwan da ake na su’ul adabi.

   

  8. Sannan ya jaddada tare da tabbatar da kafircin masu shafe Sallah.

   

  9. Ya qara jaddadawa akan ziyara Fadinsa “Fatiha da d’aya, qulhuwallahu 11, salatul fatihi 10, KURSIYYU 10”, sun isa (Ramzi akan masu tarewa a RAUDOJIN BAYIN ALLAH).

   

  10. Ya nuna haramcin yin sallah A Raudojin Bayin Allah.

   

  Allah ka kare mu ka kare mu zamiya cikin Allah alfarmar shugaba Annabi Muhammadu (saw). Amiin

   

  Daga: Sayyadi Sani Sadi Hassan

  Share
Back to top button