FADAKARWA

  • DARASI MAI TAKEN: MUƘAMIN WALIYAI KASHI NA BIYU (2)

    MUƘAMIN WALIYAI (2)

     

     

    1. GAUSI: Shi ake kira Ƙuɗubul Gausi ko Ƙuɗubul Aƙɗab ko Insanul Kamil ko Al-Muktar ko Fardul Jãmi’i ko kuma Abdullahi.

     

    Kalmar ƙuɗubi (قطب) na nufin “pole” a turanci, a hausa yana nufin tsani, ginshiƙi ko dirka. Wanda ya samu muƙamin wulaya har ya kai yana wakiltar wani sashi na gari ko na al’umma, ya zama ƙuɗubin wannan garin ko wannan al’ummar, alfarmar shi Allah zai dinga saukarwa wa’yannan jama’ar ruwan sama (arziki) ya kuma rangwanta musu yayin da suka cancanci a halakar dasu ko a saukar musu da mummunar bala’i. Shugaban ƙuɗuban nan gaba daya shine Gausu, wato (الغوث) a larabci, kuma yana nufin “mai taimako”, wato mai taimakon Halitta baki ɗaya.

     

    Gausi shine khalifan Annabi ﷺ mafi girma kuma shine shugaban waliyai baki ɗaya, ba su iya tasrifi sai da sanin sa, shi kaɗai ne a zamanin sa har sai in ya rasu sannan a samu wani ya hau muƙamin sa. Shine Insanul Kãmil (cikakken mutum) saboda office din sa ne matattar cika (hadratul kamali), duk mutumin da ya samu wulaya ya shiga wannan office din, ya zama cikakken mutum, shine wanda Annabi ﷺ yake cewa ” Allah ba zai tashi kiyama ba muddin akwai cikakken mutum a doron kasa”.

     

    2. IMÃMÃNI: Sune mafi kusanci da Gausi kuma su biyu ne, tamkar wazirai suke gareshi. Sune masu muƙamin “Mafatihil Kunuz” wato Muƙamin Siddiƙiyyah. Dayan su sunan sa Abdur-rabbi, ɗayan su sunan sa Abdul Malik. Ɗaya cikin su yana iyakar Alamil Malakuti, Ɗayan su yana iyakar Alamil Mulki, ɗayan su ne yake hawa muƙamin Gausi da zarar Gausin ya rasu.

     

    3. AUTÃDU: Su huɗu ne, kowannen su yana kusurwa daya daga kusurwar duniya guda hudu, sune wayanda Allah ke cewa “wal jibalu Autada”, dasu Allah yake kiyaye kusurwar duniya, dayan su yana bisa muƙamin Sayyidina Abubakar a daman duniya, ɗaya yana muƙamin Sayyidina Umar a Haunin Duniya, ɗaya yana gabashin duniya a muƙamin Sayyidina Usman, ɗaya yana yammacin duniya a muƙamin Sayyidina Aliyu (Allah ya kara musu yarda).

     

    Alhamdulillah, Allah Ya Bada Lada. Amiin

     

    ✍️ Sidi Sadauki

  • DARASI MAI TAKEN: MUƘAMIN WALIYAI KASHI NA DAYA (1)

    MUƘAMIN WALIYAI (1)

     

    Al-waliy (الولي) suna ne daga cikin sunayen Allah SWT wanda yake nufin “Mai kulawa ko taimakawa halitta”, kamar yadda Allah da kanshi yake cewa “Allah shine waliyyi (mai taimako) ga wayanda suka yi imani, yana fitar dasu daga duhu zuwa haske. (Baqarah: 257)

     

    Su kuwa waliyai ba kowa bane illa wayanda Allah SWT yake cewa “Babu tsoro a garesu kuma ba zasu yi baƙin ciki ba, sune wayanda suka yi imani kuma suka kasance masu taƙawa). (Yunus: 62/63). Dogaro da wannan ayar, zamu gane Allah shine mai taimakon waliyai wato muminai masu taƙawa ba ordinary muminai ba, su kuma waliyai sune masu taimakon sauran halittu.

     

    Yayin da Allah yayi nufin bayyanar da Muƙamin Wulaya cikin halitta, sai yace wa mala’iku “zan saukar da khalifa (wakili) na a doron ƙasa” (Baqarah: 30). Wannan khalifan shine shugaban mu Annabi ﷺ. Kamar yadda ya zamo farkon halitta kuma sanadin samuwar sauran halittu baki ɗaya amma a zahiri ya bayyana cikin su a tsakiya ko kusa da ƙarshen zamani, Haka ya kasance khalifan Allah a muhalli madaukaki, kafin daga baya Allah ya saukar da hasken khalifancin sa cikin Annabi Adamu A.S, ƙarni zuwa ƙarni har zuwa ga Sayyidina Abdullahi A.S.

     

    A ƙarƙashin wannan muƙamin na khalifa akwai mataimaka, kamar yadda Allah yake cewa “kuma sai muka sanya khalifofi a cikin ku” (Namli: 62), Khalifofin nan sune dukkan Annabawa da Manzanni (Allah ya kara musu yarda), da wasu daga cikin zaɓaɓɓun bayin Allah salihai, misali khidir A.S, ba Annabi bane balle ya zama manzo, kawai salihi ne.

     

    Annabi ﷺ shine khalifan Allah, sauran waliyai khalifofin Annabi ﷺ ne, muƙamin su ya rabu kashi tara kamar haka:

     

    1. Gausu

    2. Imãmãni

    3. Autãdu

    4. Budalã’u

    5. Rajibiyyun

    6. Nujabã’u

    7. Nuƙabã’u.

    8. Akh-yãru

    9. Auliyã’u

     

    ✍️ Sidi Sadauki

  • Yadda Izala Ta Shigo Nigeria Ka Saurara Kuma Ka Fahinci Manufofin Su. Daga: Sheikh Dr, Harisu Jos

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un

     

    Cikakken Bayani Akan Yanda Aka Bada Kwangilar Rusa Addinin Musulunci A Nigeria.

     

     

    Yadda Izala Ta Shigo Nigeria Ka Saurara Kuma Ka Fahinci Manufofin Su A Karkashin Kulawar Abubakar Mahmud Gumi.

     

    Allah Ya Tsare Mu. Amiiiin Yaa ALLAH

  • SIRRIN FITA DAGA KUNCI NA TALAUCI DA SAMUN FATAHIN SAMUN ARZIKI

    SIRRIN FITA DAGA KUNCI NA TALAUCI DA SAMUN FATAHIN SAMUN KUDI

     

    Wanda yake so ya fita daga kunci na talauci da Samun kudi to ya rinka aikata wannan sirrin shi wannan aikin ko hatimin talauci kake tare dashi wlh tallahi billahil’azeem saika samu wadatuwar kudi a hannunka wllh sai dai ka taimaki wani domin duk wani jalabi da kake dashi baka da kamar wannan domin irin Wanda nake amfani dashi ne.

     

     

    YANDA AKE AIKIN SHINE:

     

    Ana karanta aya 1 na suratun-nasri, sai ka karanta ya fattahu kafa 489,

    Sai kaje aya ta biyu bayan ka karanta sai kayi wuridin ya fattahu kafa 489,

    Sai aje aya ta uku bayan ka karanta ta sai a karanta ya fattahu 489.

     

    Wllh ka rike wannan sirrin bakai ba talauci kuma za’ayi hidindimu cikin jin dadi musamman irin wannan yanayin da muke ciki

    بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

    إِذَا جَاءَ نَصْرُ اللَّهِ وَالْفَتْحُ

    يا فتاح 489

    وَرَأَيْتَ النَّاسَ يَدْخُلُونَ فِي دِينِ اللَّهِ أَفْوَاجًا

    يا فتاح 489

    فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَاسْتَغْفِرْهُ ۚ إِنَّهُ كَانَ تَوَّابًا

    يا فتاح 489

     

    Amma shi wannan aikin Ana yinsa ne bayan idar da sallar asuba ko bayan idar da sallar la’asar duk a cikin satin da kayi wannan aikin sai kaga fatahi.

     

    Nayi izni ga wanda yayi comment da salatin Annabi, yayi share group uku, domin ‘yan uwa su qaru. Masha’Allah

  • SHEIKH USMAN KUSFA ZARIA – RIGI-RIGI NA ANNABI MUHAMMADU SAW.

    SHEIKH USMAN KUSFA ZARIA – RIGI-RIGI NA ANNABI MUHAMMADU Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallamm

     

    “Rigi-Rigi na Annabi Muhammadu” Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallamm. Yawanci idan yana Majlisi ya faɗi abubuwan al’ajabi ko na jinjina za ka ji taron ya kaure da kiran sunan Annabi “Aaaaannabi Muhammaduuuuuuu”, sai kaji an amsa.

     

    Tsawon Shekaru kusan Takwas ina ajiye da Folder guda ta Audios ɗin Sheikh Usman Kusfa Zaria, wanda nauyin Folder ya kai 8GB tun a wancan lokacin, banda daga baya da Ibtila’i ya afkawa Computer ta, na rasa kaso mai yawa na files ɗin da suke kan HDD ɗin wannan computer, harda wannan Folder. Kowane file na Audion da nake da shi a wancan lokacin babu wanda ya gaza Awa Biyu (2hours). Shi baza ka ji shi yana karatun Hadisi ko Fiƙhu ba (A Audios ɗin sa da nake da su a wancan lokacin) sai dai kaji irin su Fassarar Jauhara da Asraran ta, Fassarar Salatul Fatihi da duk wani abu na Halarar Shehu Tijani Radhiyallahu Ta’ala Anhu. Wannan yasa nayi ta mamaki da naga ana Izgilanci wa Iliman da yake fitarwa. Ko da yake, ba abin mamaki bane a irin sanin da muka yiwa Munkirai. Dama da yawan mutanen mu Ƴan Izala/Wahabiyya duk abinda basu sani ba, a wurin su babu wannan abin, ko kuma Bid’a ne ko Kafirci ko Shirka (Allah ya shirya mana ku). Amma ina mai tabbatar muku, in dai Rigi-Rigi ne, Wallahi waɗannan abubuwan da yake fitarwa ba komai bane cikin abubuwan da ya sani, domin shi wani Ilimi Allah yayi masa wanda idan mutum bai saba da terminologies ɗin ire-iren waɗannan Iliman ba, zai zata sabon Ilimi yake fitarwa. Allah ya yi masa baiwa mai yawa a fannin Ilimin Baɗini. Kuma a cikin gidan Tijjaniyyah Shehu Usman Kusfa Zaria bai kai ɗigo ɗaya na waɗanda suke ɓoye ba. Shi ɗin ma, Allah ne yasan dalilin bayyana shi a yanzu ga waɗanda basu san shi ba sai yanzun.

     

    Dalilin wannan rubutun shi ne, masu yi masa Izgilanci ba kai tsaye shi ko Ilimin sa suke yiwa ba. A’a! Shehu Tijani Radhiyallahu Ta’ala Anhu da abubuwan da suke da alaƙa da shi suke nufi da wannan Izgilancin, kuma mutumin da yake gidan Gilas ne yake kiran azo ayi wasan jifa saboda toshewar Basira. Akwai ƴanuwan mu da suke ganin kada adinga fitar da ire-iren waɗannan Iliman da Rigi-Rigi yake fitarwa, wanda Ni ina daga cikin masu ganin a fitar ɗin shi ne Alkhairi saboda shi Zamani ba shi da tausayi, idan yazo maka da wata Ƙa’ida, kayi haƙuri ka karɓa kawai, sai ku zauna lafiya, amma idan ka ƙi, kai ne za ka yi asara. Sai dai a kyautata amfani da kuma saka mizani. Amma maganar ɓoye irin waɗannan Iliman ayi haƙuri a bar ta. Wanda zai halaka, zai halaka, wanda zai rayu zai rayu kawai.

     

    Ya Ku Munkirai! Baza’a daina fitar da Ilimi saboda inkarin ku ba, haka baza’a daina ambaton Shehu Tijani Radhiyallahu Ta’ala Anhu ba!

     

    Daga: Mujtaba

Back to top button