FAIDAH

  • An Bude Wazifa Da Zikirin Juma’a A Sahabin Annabi Muhammadu SAW A Kasar China.

    An Bude Wazifa Da Zikirin Juma’a A Sahabin Annabi Muhammadu SAW A Kasar China.

     

    Daya daga cikin manyan sahaban Manzon Allah SAW Sayyadina Sa’ad Bn Abi Waqas wanda ya rayu a kasar China yana da Masallaci a jiya Juma’a an bude gudanar da Wazifa da Zikirin Juma’a a Masallacin dake kasar China.

     

    Taron bude wazifa wanda gidauniyar Maulana Sheikh Dahiru Bauchi ta jagorancin budewa wanda Sayyadi Alhaji Ibrahim (Khadimul Faidha) ya bude tare da wasu muridai a kasar.

     

    Insha ALLAHU yanzu kullum za’ayi gudanar da Wazifa a Masallacin da kuma Zikirin Juma’a duk sati kamar yanda tsarin koyarwa a Darikar Tijjaniyya ya tanadar.

     

    Allah ya karbi ayyukan mu ya bamu albarkan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiiiin Yaa ALLAH

     

    Daga: Tijjaniyya Media News

  • ARFAT 2024: Kallin Yanda Aka Gudanar Da Wazifa A Filin Arfat Cikin BIDIYO.

    Yau ce ranar da al’ummar Musulmai da ke gudanar da aikin Hajjin bana ke tsayuwar Arfa.

     

    Tsayuwar Arfa na ɗaya daga cikin ƙololuwar aikin Hajji, inda ake buƙatar mahajjata su tsaya a filin domin yin addu’o’i na musamman.

     

     

    Mabiya Darikar Tijjaniyya a fadin duniya suna daga cikin wanda suke halartan Aikin Hajj duk shekara tare da gabatar da ayyukan su na sufanci a filin Arfat.

     

    Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR ya jagoranci Wazifa a filin Arfat tare da daukaci mutane daga sassan fadin duniya.

     

    Allah ya karbi ayyukan mu da Addu’o’in mu baki daya. Amiin Yaa ALLAH

  • Tsananin Bin Sunnar ANNABI (S.A.W) Da SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Iri Daya Ne.

    Misalin Tsananin Bin Sunnar ANNABI(S.A.W) Da SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yake.

     

    Akwai Watarana Da Ya Umarci Babban Jikansa, IMAM HASSAN CISSE(R.A) Ya Ja Sallah, Da IMAM Ya Tashi Yin Sallah, Sai Duk Bayan Fatiha Ya Ɗebo/Tsinto Ayoyi Daga Wata Surah, Sai Ya Biya Yayi Ruku’u,

     

    Da Aka Idar Sai SHEHU(R.A) Ya Ce; Idan Zaka Ja Ni Sallah Daga Yau, Ka Min Irin Sallar ANNABI(S.A.W), Idan Ya Ɗauki Surah Sai Ya Dire Ta,

     

    Kada Ka Min Irin Sallar Mutan Gari Kaza, a Tsinto Ayoyi, Duk Da Hakan Ba Laifi Bane, Amma Yadda ANNABI Ya Yi Nake So a Min.

     

    ALLAH Ya Ƙarawa SHEHU Karama, Ya Bamu Albarkar Masu Albarka, Ameeen.

     

    (©️Sabo Ibrahim Hassan).

  • Sama Da Almajirai Miliyan 100 Ne Suka Sallamawa Sheikh Ibrahim Inyass. Inji Kungiyar Rabidatu Alamil Islami Dake Saudi Arabia.

    Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq RA Yana Da Almajirai Miliyan 100 Wanda Suka Sallama Masa A Africa.

     

    ……Inji Kungiyar Rabidatu Alamil Islami Dake Saudi Arabia.

     

    Binkice Ya Tabbatar Da Cewa Akwai Almajiran Sheikh Ibrahim Inyass RA Sama Da Miliyan 100 A Kasashen Afirka.

     

    Wanda Suka Sallamawa Shehin Malamin A Africa Kadai. Inji Kungiyar Rabidatu Alamil Islami Dake Saudi Arabia.

     

    ALLAH Ya Karawa SHEHU Ibrahim Masoya Da Kusanci Ga Fiyayyen Halitta ANNABIN Mu Muhammadu SAW. Amiin

     

    Daga: Babangida A Maina

  • JERIN SUNAYEN YA’YA’N MAULANMU SHEHU IBRAHIM INYASS MAZA DA MATA SU (75).

    JERIN SUNAYEN YA’YA’N MAULANMU SHEHU IBRAHIM INYASS MAZA DA MATA SU (75).

     

    MAZA (38)

     

    1. Shehu Abdullahi

    2. Shehu AbdurRaheem

    3. Shehu Abdulmalik

    4. Shehu Abdul’Ahad

    5. Shehu Ahmadu

    6. Shehu Muhammadu Mujtaba

    7. Shehu Abubakar

    8. Shehu Muhammadu Mansuru

    9. Shehu Muhammadu Naziru

    10. Shehu Muhammadu Mahi

     

    11. Shehu Muhammadu Hadi

    12. Shehu Muhammadu Aminu

    13. Shehu Muhammadu Makiyu

    14. Shehu Muhammadu Ma’amunu

    15. Shehu Muhammadu Akibu

    16. Shehu Muhammadu Muntaka

    17. Shehu Muhammadu Arabi

    18. Shehu Muhammadu Muktar

    19. Shehu Muhammadu Nasiru

    20. Shehu Muhammadu Mahdi

     

    21. Shehu Muhammadu Mujtaba

    22. Shehu Muhammadu Kurashiyu

    23. Shehu Muhammadu Shafi’u

    24. Shehu Muhammadu Mahmudu

    25. Shehu Muhammadu Halifa

    26. Shehu Muhammadu Yasin

    27. Shehu Muhammadu Tuhami

    28. Shehu Muhammadu Murtadha

    29. Shehu Muhammadu Munhaminna

    30. Shehu Muhammadu Siraja

     

    31. Shehu Muhammadul Amin

    32. Shehu Muhammadul Abdurahman

    33. Shehu Muhammadu Abdulkarim

    34. Shehu Muhammadu Sahibu kahiri

    35. Shehu Muhammadu Nurul dini

    36. Shehu Muhammadu Sahibul Makami

    37. Shehu Muhammadu Sahibul Judi

    38. Shehu Muhammadul Muntazir.

    .

    MATA (37)

    1. Sayyada Maryam

    2. Sayyada Maryam

    3. Sayyada Maryam

    4. SayyadaMaryam

    5. SayyadaHapsatu

    6. SayyadaUmamatu

    7. SayyadaUmamatu

    8. Sayyada Umamatu

    9. Sayyada Fadimatu

    10. Sayyada Fatimatu

     

    11. Sayyada Fadimatu

    12. Sayyada Ummu Kulsum

    13. Sayyada Ummul Khairi

    14. Sayyada Ummu Haniy

    15. Sayyada Ummu Habibata

    16. Sayyada Ummul Salmata

    17. Sayyada Ummu Salma

    18. Sayyada Aishatu

    19. Sayyada Aishatu

    20. Sayyada Nafisatu

     

    21. Sayyada Nafisatu

    22. Sayyada Nafisatu

    23. Sayyada Hafisatu

    24. Sayyada Rukayyatu

    25. Sayyada Rukayyatu

    26. Sayyada Rukayyatu

    27. Sayyada Khadijatu

    28. Sayyada Khadijatu

    29. Sayyada Hauwa’u

    30. Sayyada Rabi’atu

     

    31. Sayyada Barakatu

    32. Sayyada Lubabatu

    33. Sayyada Aminatu

    34. Sayyada Safiyatu

    35. Sayyada Saudatu

    36. Sayyada Rahmat

    37. Sayyada Zainabu

    .

    Allah Yabamu Albarkacin Su, Ya Azurtamu Da Zuri’a Daiyiba Ta Maulanmu Shehu R.t.a. Amiin

     

    Muhammad Izzuddin Abubakar

    Shehu Manzo Media Team

Back to top button