FAIDAH

  • MAULUD 2023: Za’a Gudanar Da Babban Taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA A Birnin Abuja FCT Karo Na 37th.

    DA DUMI DUMIN SA:

     

    Za’a Gudanar Da Babban Taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA A Birnin Abuja FCT Karo Na 37th.

     

    Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi RA zata gudanar da gagarumin taron bikin Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq RA a babban birnin tarayya Abuja FCT, Nigeria. a karkashin jagoranci Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR RA.

     

    Taron Mauludin zai samu halartan manyan baki daga sassa daban-daban na fadin duniya kamar yadda aka saba gabatar wa duk shekara.

     

    Za’a gudanar da taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass RA, ne kamar haka;

     

    – Rana: 27/Rajab/1444 – 18/02/2023.

    – Wurin: Abuja FCT, Nigeria

    – Lokaci: karfe 10:00 zuwa 1:00pm

     

    Allah ya bada ikon halartan taro. Amiin

     

    Babangida A. Maina

    Tijjaniyya Media News

    Share
  • Sheikh Ibrahim Inyass Al Khaulaq

    Akwai Wani Mutum Da SHEHU IBRAHIM NIASSE (R.A) Yake Burge Shi Kwarai Da Gaske Sai Ya Zo Wajen SHEHU IBRAHIM (R.A) Suna Hira, Sai Ya Ce Da Shi:

     

    “Ai SHEHU Girmanka Fa a Yau Ya Kai Ka Zarta Girman Mahaifinka SHEIKH ABDULLAHI (R.A)”.

     

    Sai SHEHU(R.A) Ya Ce Da Shi;

     

    “A’a Zan Zamo Na Fifici Babana Ne a Lokacin Da Na Haifowa Duniya Mutum Kamar NI”.

     

    (Duba Littafi Mai Suna:

     

    شاعر رسول الله صلى الله عليه وسلم

    شعر شيخ الإسلام من وجهة نظر أدبية.

     

    Na Imam (Prof.) Ibrahim Maqary Shafi Na 13-14).

     

    ALLAH YA BA MU ALBARKAR MASU ALBARKA, YA ‘KARA MANA SOYAYYAR SALIHAN BAYIN ALLAH, AMEEEEN

    Share
  • Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Tare Da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA

    ALAMAR TABEWA SHINE KIYAYYAR MAJIBANTA ZUWA GA SHIRIYA.

     

    Idan ka dauko kudi kimanin Naira dubu 50, da kuma Kunshin nama a cikin yar takarda ka aje gaban Kare, to zai kai bakine ga wannan nama ta hanyar wofintar da wannan kudin, saboda ALLAH bai sanya masa hankalin da zai gane cewa “Da wannan dubu 50 din zai iya sayen nama mai dinbin yawa yaci har ya koshi ya baiwa saura ba” mai yiwuwa karshe ma sai ya yayyaga wannan kudaden ko kuma yayi fitsari garesu, saboda rashin sanin kimarsu.

     

    Haka zalika, wanda duk kaga ya fiye nuna kiyayya ga irin wadannan jagororin Musuluncin, da kuma kokarin ganin sai ya aibatasu da kuma muzantasu ta hanyar gaza gano dimbin falalolin da dimbin alkairai da ALLAH ya dabai-bayesu dasu, to ka gane shi din kamar dai wannan karenne da ALLAH bai fahimtar dashi gane amfanin wannan kudin ba, sama da wannan dan kunshin naman da ya zaba.

     

    Ai abun a bayyane yake ALLAH ne yake fadi da kansa ومن يضلل فلن تجد له ولياً مرشداً

     

    Ma’ana : Kuma wanda ya batar (Da Adalcinsa), to, ba za ka sami majibanci mai shiryar da shi ba.

     

    ALLAH YA BARMU DA SO DA KAUNAR DUKKANIN WALIYANSA MAKUSANTA.

     

    Daga: Muhammadu Usman Gashua

    Share
  • Alakar Darikar Tijjaniyya Da Darikar Kadiriyya A Addinin Musulunci.

    ALAKAR MU DA YAN QADIRIYYA

     

    Dariqar Qadiriyya itace dariqar Sidi Abdulqadir Jilani al-Baghdadi Radiyallahu Ta’ala Anhu. Cikakken Sharifi, babban waliyi Qudubi, wanda ya fara bayyana karamar sa tun a tsummar goyo, shehin da har shehin mu Qudubul Maktum Shehu Ahmadu Tijjani Radiyallahu Ta’ala Anhu yayi dariqar sa.

     

    In ba don lallai Shehu Tijjani zabin Allah bane, toh da har tashin duniya, ba za ayi waliyyi kamar Sidi Abdulqadir ba, ba za a samu dariqa sama da tasa ba.

     

    Amma abinda ya faru shine, kamar yadda Annabi SAW yake tun azal shugaba kuma cikamakin Annabawa da manzanni, Haka Shehu Tijjani RTA yake shugaba kuma cikamakin waliyan farko da na Qarshe. Kamar yadda Annabi SAW yake bautawa Allah ta sigar Ibadar Manzanni magabata har zuwa lokacin da aka yi isra’i da mi’iraji dashi ya karbo tasa sallar, haka Shehu Tijjani RTA yayi sufancin sa bisa tsarin dariqun sauran waliyai magabata kafin ranar da Annabi SAW ya bayyana garesa yayi masa umurnin ajiye su da riqo da TIJJANIYA kawai.

     

    Na zauna da wani batijjanen sufi a kano, Sidi Muhammadul Kabir, nake tambayar sa sha’anin Sidi Abdulqadir da Shehu Tijjani, yace Ai Imam Hassan ne Shehu Tijjani, Imamu Hussaini ne Sidi Abdulqadir. Abin nufi, ruhukan su ne a jikin wayannan waliyai.

     

    Tabbas muqamin Shehu Tijjani ya daukaka akan duk wani waliyyi banda sahabbai da Annabawa, za ka fahimci haka ne in ka samu ingantacciyar kissar haduwar Shehu Umarul Futi (Batijjane) da Shehu Usman Dan Fodio (Baqadire).

     

    FADAR QADAMAYA HATANI

    FA ILLA ANTA TIJJANI

    ABIN FA NUFA GA JILANI

    MUTANEN NASA ZAMANI

    FA KAI KO KULLU AZMANI

     

    A DON HAKA AULIYA’U DUKA

    SU KAYYO SUNKUYO GUN KA

    SUNA NEMAN FUYUDAN KA

    FA NIMA NA FAKE GUN KA

    IN SAM MADADI DA FAIDANI

     

    Inji Shehu Abubakar Ateeq Sanka RTA a cikin Tusamma.

     

    Magabata sun rayu da yan qadiriyya lafiya lau, tare suke sallah, tare suke maulidi da sauran mu’amala ba tareda kowannen su ya raina kowanne ba.

     

    Toh ina kira garemu matasa, musamman mawaqa da masu hawa mumbari domin karanta maulidi, idan kun tashi fadin daraja da martabobin Shehu Tijjani RTA, ku fada cikin ladabi, kar ku qasqantar da kowani waliyyi ballantana sidi Abdulqadir RTA, kamar yadda saboda fadin darajar Annabi ba zaku qasqantar da sauran Annabawa ba.

     

    Duk wani waliyyi mai dariqa, sharifi ne, ka ko san zagin sharifi zagin Annabi ne.

     

    Dan Allah mu kula, da yawa in kaga dan wata dariqar ya zagi Shehu Tijjani, toh wayanda suke kewaye dashi ne basu da hikimar isar masa da saqon martabar Shehu Tijjani, ko kuma shi din bai da haske RABBANIY.

     

    INA SO INJI ZANCEN KA NA’AM YA SHEHU TIJJANI

     

    ✍ Sidi Sadauki

    Share
  • RISÃLATUL-MUNTAKIM Wanda MAULAUNMU SHEHU IBRAHIM (R.A) Ya Rubuta.

    RISALATUL MUNTAKIM.

     

    “…Abin Da Ya Kamata Ga MURIDI Shi Ne;

     

    Ka Da Ya Dakata a Tafiyarsa Har Sai Ya Riske Ni, Idan Na Kasa Warware Matsalarsa, To a Wannan Hali Sai Ya Tafi Zuwa Ga Wani Shaihin Da Mukaminsa Ya Fi Nawa.

     

    Ku Sani – ALLAH Ya Yi Maku Rahma – Cewa;

     

    Lallai Mafi Yawan Masu Da’awar Mukamai Na ‘Karya, Suna Toshe Hanyar ALLAH Ne, Ta Hanyar Rashin Tsayawa ‘Kyam Akan Shari’a Da Suke Yi, Duk Wanda Ya Danganta Kansa Da ALLAH, Sannan Kuma Ya Koma Yana Toshe Hanyarsa,

     

    To Lallai Ya Yi Fito-Na-Fito Ne Domin Yin Ya’ki Da ALLAH, Ya Zamo Ba Shi Da Bambanci Da Masu Inkari Ta6a66u; Domin Shi Ne Sanadiyyar Inkarin Nasu.

     

    Dole Ne Ku Rinka Zuwa Wurinmu a Mafi Yawan Lokuta; Domin Ku Koyi Ladubban Suluki Kamar Yadda Kuka Koyi Hakikanin Jazba, Wanda Duk Ya Yi Haka Ya Sami Babban Rabo.

     

    Dole Ne a Gyara Abubuwan ‘Ki Da ‘Yan-uwa Suke Aikatawa, a Yi Haka Da Hannu, Ko Da Harshe, Ko a ‘Ki Abin a Zuciya, Kaman Yadda Hakan Ya Zo a Hadisi.

     

    Dole Ne Ga Duk Wanda Yake Son Ya Amfana, Ya Kiyaye Wasiyyoyinmu Da Suka Zo a Wakoki, Ko Suka Zo a Rubutun Zube,

     

    Lallai Kiyaye Wannan Wasikar Wajibi Ne Ga Gaba ‘Dayan Muridanmu, Duk Wanda Ya Same Ta Ya Rubuta Ta, Ya Mayar Da Ita Lazimi Yana Karantawa Kullum”.

     

    ~ Wanda Ya Rubuta Shi Ne: Ibrahim Ibn Alhaji Abdullahi Al-Tijani, Kaulakh 1349Ah.

     

    (Wannan Wani Sashi Ne Na RISÃLATUL-MUNTAKIM Wanda MAULAUNMU SHEHU IBRAHIM(R.A) Ya Rubuta).

     

    ALLAH Ya Taimake Mu Wajen Riko Da Wannan Risala Ta MAULANNU SHEHU IBRAHIM(R.A).

     

    ALLAH Ya Kiyaye Mu ‘Dibar Santsi (Zamewa) Ko Ratsewa Akan Wannan Hanya, Don Albarkar MAULANMU SHEHU TIJJANI(R.A). Amiin

    Share
Back to top button