FATWA

 • Shin Akwai Aljanu Yan Darikar Tijjaniyya Kamar Yanda Sheikh Dahiru Bauchi RA Yake Fada. ???

  SHIN AKWAI ALJANU YAN ĎARIQAR TIJJANIYYA KAMAR YADDA AKE YAĎAWA MAULANMU SHEHU ĎAHIRU BAUCI YA FAĎA?

   

  Banji hakikar abinda Maulanmu Shehu Ďahiru Bauci ya faďa kan wannan qadhiyya ba, sai dai koma yaya lamarin ya kasance wannan magana bata saba da shari’a ba balle ta zamto abin yin Isgili ga wannan babban bawan Allah da ya karar da rayuwar sa cikin hidimar Musulunci.

   

  Tamkar yadda mutane suke firaq daban daban Ahlussunah,Shi’a mu’utazila da Yan Izala haka abin yake cikin Aljanu.

   

  Allah ya faďa mana cikin qur’anin sa mai girma game da firaq na Aljanu.

   

  وَأَنَّا مِنَّا الصَّالِحُونَ وَمِنَّا دُون ذَلِكَ كُنَّا طَرَائِق قِدَدًا

  ( Daga cikin mu akwai Salihai akwai waďand basu ba, mun kasance tafarkai ne mabanbanta)

   

  Al’imamu Alqurďubi ya hakaito daga Suddiy yana lokacin da yake fassara طرأئق قددا.

   

  Yace 👉 السدي في قوله تعالى { طرائق قددا} قال : في الجن مثلكم قدرية، ومرجئة، وخوارج، ورافضة، وشيعة، وسنية. وقال قوم :

   

  Alhafiz Ibn Katheer cikin tafsirin sa karkashin wannan aya ya kawo kissar Sulaiman bin Mihrãn Al’a’amash yadda yayi magana da Aljani har ya tambaye shi abincin da yake so ya kawo mashi sannan ya tambaye shi Su Waye Rãwafidh cikin ku (Aljanu) sai Aljanin yace sune mafiya sharrin mu.

   

  سمعت الأعمش يقول تروح إلينا جني فقلت له ما أحب الطعام إليكم فقال الأرز قال فأتيناهم به فجعلت أرى اللقم ترفع ولا أرى أحدا فقلت فيكم من هذه الأهواء التي فينا قال نعم فقلت فما الرافضة فيكم قال شرنا

   

  Ibn Katheer yace ” Na karantawa Shehina Mizzi isnãdin wannan kissa yace min ta inganta”

   

  Kenan a wajen Malamai ba sabuwar magana bace ace an sami Aljani ďan ďariqa ko wata firqa.Wanda dama mu yan Tijjaniya bamu shakka ko kaďan akwai Aljanu masu tarin yawa da suke Tijjaniya.

   

  Haka kuma akwai Aljanun da suke bin tafarkin Bidi’a na Wahabiyya wanda waďannan Aljanu masu shiga jikin Yan mata su hana su Aure saboda…

   

  Allah ya kara wa Shehi lafiya. Amiiiin

  Share
 • Jawabi Mai Matuƙar Muhimmanci Daga MAULANA SHEIKH DAHIRU BAUCHI OFR (R.A).

  Daga Taskar MAULANMU SHEHU TAHIRU USMAN BAUCHI (R.A)

   

  Jawabi Mai Matuƙar Muhimmanci Daga MAULANA SHEIKH DAHIRU BAUCHI OFR (R.A).

   

   

  ALLAH Ya Ƙara Muku Yarda. Amiiin

   

  Allah Ya Kara Wa Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA Lafiya Da Nisan Kwana Albarkacin Manzon Allah SAW. Amiin

  Share
 • Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini Shugaban Majalisar Malamai Na Najeriya Baki Daya.

  Wani Ya Tambayeni Kamar Haka!

   

  Dan Allah Malam Imam Anas, me yasa ban cika ganin abubuwan Maulana ba, kuma mutanen Nigeria basu cika yaɗa abubuwan saba ina nufin Maulana Sheik Shariff Ibrahim Saleh Al-Husain Maiduguri kamar sauran malamai.

   

  Amasar Dana Bashi.

   

  Shi malamin malamai ne kuma malamin duniya ne, ba malamin Nigeria bane, a majalisar malamai ta duniya a yanzu haka shine mutum mai daraja ta biyu a majalisar malamai ta Azhar shine mai daraja ta biyu, a majalisar malamai ta Nigeria, shine mai daraja ta ɗaya.

   

  Duniya ce tasan waye shi amma yayi ma Nigeria girma shi yasa lamuransa sai dai ka gani ana yaɗawa a duniyance ba a Nigerian ce ba.

   

  Ba kaga gidauniyar daya haɗa ba, ta buɗe cibiyar bincike ta ilimi mafi girma a Africa ba, wacce akeyi anan Nigeria, babu wata ƙasa ta Musulunci da bata bada gudunmawa ba, tare da manyan attajirai na duniya dana Nigeria, kusan Trillion ya haɗa a lokaci ɗaya.

   

  Allah ya ƙara ma malam lafiya, tare da jinkiri mai amfani haƙiƙa a wannan ƙarnin wallahi babu kamarsa. Amiin Yaa ALLAH.

   

  Daga: Malam Imam Anas

  Share
 • GASKIYA MAGANA: Yawan Yajin Aiki Ba Shine Mafita Ba, Fahimtar Prof. Ibrahim Maqari RA.

  Karin Haske: Maulana Sheikh Ibrahim Maqari Ya Sake Karin Haske Akan Maganar Yajin Aikin Malaman Jami’a A Najeriya.

   

  Farfesa Ibrahim Maqari Ya Bayyana Cewa

   

  Yawan Yajin Aiki Ba Shine Mafita Ba, Fahimtar Prof. Ibrahim Maqari RA.

   

  ALLAH Ya Kawo Mana Karshen Wannan Yajin Aikin Da Malaman Jami’a Keyi A Najeriya. Amiin

  Share
 • Kira ga malaman jami’a da su koma aikinsu kuma su ingantashi har ya jawo hankalin masu gujewa. Inji Farfesa Ibrahim Maqari.

  Saƙonnin uku ne a cikin video din

   

  – Kira ga hukuma ta ƙara inganta rayuwar malaman Jami’a.

  – Kira ga masu samar da doka su nemo hanyar da zasu samar da dokar da zata tilasta jami’an Gwamnati sanya ƴayansu a makarantun Gwamnati.

  – Kira ga malaman jami’a da su koma aikinsu kuma su ingantashi har ya jawo hankalin masu gujewa.

   

  Mai yuyuwa mu haɗu da ɗaukacin Malaman Jami’a a 2/3. Sabaninmu ƙila kawai a sashin 1/3 ne, inda mai yuyuwa na yi kuskure wajen bada nisbar nagartattun aiyukan bincike a Jami’o’i da kuma rashin dacewar lokacin lura da halin da Malaman ke ciki.

   

  ALLAH ya kawo mana karshen wadannan matsalolin dake faruwa a najeriya. Amiin

  Share
Back to top button