HUJJAR MAULUDI

  • WALLAHI WANNAN HUJJAR KADAI TA ISA HUJJAH AYI MAULIDI

    A Cikin Suratu Hud(A.S) Bayan ALLAH (S.W.T) Ya Gaya Ma MANZONSA(S.A.W) Labarurrukan Annabawan Da Suka Gabace Shi Da Kuma Irin Gwagwarmayar Da Suka Yi Da Al’ummominsu, Daga Qarshen Surar Sai Ya Ce Masa:-

     

    “Kuma Da Yawa Mu Kan Qissanta Maka Daga Labarurrukan Manzanni(wadanda suka gabata), Gwargwadon Yadda Za Mu Tabbatar(Za Mu Qarfafa) Maka Zuciyarka”.

     

    (Suratul Hud: 119).

     

    Shehu Ibrahim NYASS(R.A) Yake Cewa:-

     

    ”In Dai Har MANZON ALLAH(S.A.W) Zuciyarsa Zata Qarfafa Idan An Bashi Labarin Annabawan Da Suka Gabata, To Yaya Kuma Mu Na Mu Zuciyoyin Ba Za Su Qarfafa Ba Idan An Karanta Mana Tarihin MANZON ALLAH (S.A.W)???”

     

    To Jama’a Idan Muka Kalli Wannan Ayah Da Idon Basira, Ai Ita Kadai Ma Ta Ishe Mu Hujjar Taruwa Ayi Maulidi.

     

    Jama’a Maulidin Nan Fa Wallahi Ayyukan Alkhairi Ne Masu ‘Dimbin Yawa a Kunshe a Cikinsa.

     

    MISALI:

     

    (A) Wa’azi Da Tunatarwa Da Nasihohi Ta Hanya Jiyar Da Al-ummah Tarihin MANZON ALLAH (S.A.W) Da Yakokinsa Da Sauran Gwagwarmayar Da Ya Sha Fama Da Ita Domin Isar Da Saqon Ubangiji(S.W.T).

     

    (B) Karatun Al’Qur’ani Da Hadisan MANZO (S.A.W).

     

    (C) Rera Yabon Manzon ALLAH(S.A.W) Da Iyalan Gidansa Sahabbansa Wadanda Suka Taimake Shi Wajen Isar Da Sakon Ubangiji (S.W.T).

     

    (D) Zikirin ALLAH Da Salati Ga SHUGABA (S.A.W).

     

    (E) Shigar Da Soyayyarsa Da Qaunarsa Cikin Zukatan Manya Da Qanqana, Ta Hanyar Fa’dar Siffofinsa Da Halayensa, Da Mu’ujizozinsa(S

    .A.W).

     

    (F) Taimakawa Juna Cikin Bin ALLAH, Ta Hanyar Zumunci Da Kuma Haduwa Da Juna a Bisa Manufa Guda, Wato Girmama Manzon ALLAH(S.A.W).

     

    (G) Ciyarwa Da Shayarwa Fi-Sabilillahi.

     

    To ‘Yan’uwa Idan Kuka Dubi Wadannan Abubuwan Da Na Lissafta a Sama Da Ma Wasunsu Wadanda Na Manta Ban Fa’da Ba, Ai Zaku Ga Cewar Dukanninsu Ayyukan Alkhairi Ne Wadanda Musulunci Yake Umarni Da Su.

     

    ALHAMDULILLAH!

     

    ALLAH KA SANYAMU CIKIN WADANDA IDAN AN TARU ANA KARANTA TARIHIN ANNABI(S.A.W) DA FADAN DARAJOJINSA ZUCIYOYINMU SU SAMU NUTSUWA DA FARIN CIKI.

     

    YA KARE MU DAGA AFKAWA CIKIN TAWAGAR DA IDAN AN TARU ANA BADA TARIHIN MANZON RAHAMA(S.A.W) DA FADAN DARAJOJINSA SAI SU JI KAMAR ANA ZUBA MUSU RUWAN DALMA A KUNNE, KUMA ZUCIYARSU KAMAR ZATA FASHE DON BAKIN CIKI AMEEEEEN.

  • HUJJAR YIN MAULIDIN ANNABI(S.A.W) DAGA CIKIN NASSIN AL’QUR’ANI KASHI NA BIYU (2)

    HUJJAR YIN MAULIDIN ANNABI(S.A.W) DAGA CIKIN NASSIN AL’QUR’ANI:

     

    WALLAHI WANNAN HUJJAR KADAI TA ISA HUJJAH AYI MAULIDI:-

     

    A Cikin Suratu Hud(A.S) Bayan ALLAH(S.W.T) Ya Gaya Ma MANZONSA(S.A.W) Labarurrukan Annabawan Da Suka Gabace Shi Da Kuma Irin Gwagwarmayar Da Suka Yi Da Al’ummominsu, Daga Qarshen Surar Sai Ya Ce Masa:-

     

    “Kuma Da Yawa Mu Kan Qissanta Maka Daga Labarurrukan Manzanni(wadanda suka gabata), Gwargwadon Yadda Za Mu Tabbatar(Za Mu Qarfafa) Maka Zuciyarka”.

     

    (Suratul Hud: 119).

     

    Shehu Ibrahim NYASS(R.A) Yake Cewa:-

     

    ”In Dai Har MANZON ALLAH(S.A.W) Zuciyarsa Zata Qarfafa Idan An Bashi Labarin Annabawan Da Suka Gabata, To Yaya Kuma Mu Na Mu Zuciyoyin Ba Za Su Qarfafa Ba Idan An Karanta Mana Tarihin MANZON ALLAH(S.A.W)???”

     

    To Jama’a Idan Muka Kalli Wannan Ayah Da Idon Basira, Ai Ita Kadai Ma Ta Ishe Mu Hujjar Taruwa Ayi Maulidi.

     

    Jama’a Maulidin Nan Fa Wallahi Ayyukan Alkhairi Ne Masu ‘Dimbin Yawa a Kunshe a Cikinsa.

     

    MISALI:

     

    (A) Wa’azi Da Tunatarwa Da Nasihohi Ta Hanya Jiyar Da Al-ummah Tarihin MANZON ALLAH(S.A.W) Da Yakokinsa Da Sauran Gwagwarmayar Da Ya Sha Fama Da Ita Domin Isar Da Saqon Ubangiji(S.W.T).

     

    (B) Karatun Al’Qur’ani Da Hadisan MANZO (S.A.W).

     

    (C) Rera Yabon Manzon ALLAH(S.A.W) Da Iyalan Gidansa Sahabbansa Wadanda Suka Taimake Shi Wajen Isar Da Sakon Ubangiji(S.W.T).

     

    (D) Zikirin ALLAH Da Salati Ga SHUGABA (S.A.W).

     

    (E) Shigar Da Soyayyarsa Da Qaunarsa Cikin Zukatan Manya Da Qanqana, Ta Hanyar Fa’dar Siffofinsa Da Halayensa, Da Mu’ujizozinsa(S.A.W).

     

    (F) Taimakawa Juna Cikin Bin ALLAH, Ta Hanyar Zumunci Da Kuma Haduwa Da Juna a Bisa Manufa Guda, Wato Girmama Manzon ALLAH(S.A.W).

     

    (G) Ciyarwa Da Shayarwa Fi-Sabilillahi.

     

    To ‘Yan’uwa Idan Kuka Dubi Wadannan Abubuwan Da Na Lissafta a Sama Da Ma Wasunsu Wadanda Na Manta Ban Fa’da Ba, Ai Zaku Ga Cewar Dukanninsu Ayyukan Alkhairi Ne Wadanda Musulunci Yake Umarni Da Su.

     

    ALLAH KA SANYAMU CIKIN WADANDA IDAN AN TARU ANA KARANTA TARIHIN ANNABI(S.A.W) DA FADAN DARAJOJINSA ZUCIYOYINMU SU SAMU NUTSUWA DA FARIN CIKI.

     

    YA KARE MU DAGA AFKAWA CIKIN TAWAGAR DA IDAN AN TARU ANA BADA TARIHIN MANZON RAHAMA(S.A.W) DA FADAN DARAJOJINSA SAI SU JI KAMAR ANA ZUBA MUSU RUWAN DALMA A KUNNE, KUMA ZUCIYARSU KAMAR ZATA FASHE DON BAKIN CIKI AMEEEEEN.

  • HUJJAR YIN MAULUDIN ANNABI (S.A.W) A CIKIN AL’QUR’ANI MAI GIRMA (Kashi Na Daya 1)

    HUJJAR YIN MAULUDIN ANNABI (S.A.W) A CIKIN AL’QUR’ANI MAI GIRMA (Kashi Na Daya 1)

     

    IDAN IDONKA BAYA GANI SOSAI SABODA HAZO-HAZO KO DISHI-DISHI KA ARO TABARAU NA HANGEN NESA DON GANEWA KANKA KAR A BAKA LABARI.

     

    Abin Da Za Mu Fara Kafa Hujja Da Shi, Su Ne; Ayoyin Al’Qur’ani Mai Girma!

     

    Aya Ta Farko Za’a Same Ta a Cikin Suratu Yunus (A.S) Surah Ta 10 Aya Ta 58, Wajen Da ALLAH (S.W.T) Yake Cewa:

     

    ”(YA MUHAMMADU) Ka Ce Musu Da FALALAR ALLAH Ne Da Kuma RAHAMARSA; Da Wannan Ya Kamata Su Yi FARIN CIKI, Domin Shi Ne Mafi Alkhairi Daga(Arzikin) Da Suke Tarawa”.

     

    To Ga Shi Dai Ayah Ta Yi Bayani Qarara, Sai Dai Kash! Wadansu Mutanen Sun Kasa Fahimta. Harma Suna Yin Musu Da Kuma Jayayya Suna Cewa:

     

    “Ai Wannan Falalah Da Rahamar, Ai Ba MANZON ALLAH(S.A.W) Ake Nufi Ba” – Wa’iyazhu Billah.

     

    Saboda Haka a Ganinsu, Wai Ba Za Mu Yi Murnar Ba.. Ina Jin Dai Sun Manta Da Ayar Nan Ne Ta Cikin Suratul Anbiya:

     

    ”Ba Mu Aiko Ka Ba, Sai Domin Ka Zama RAHAMA Ga Dukkan Talikai”, (21:107).

     

    To Bari Mu Duba Mu Ga MEYE MALUMAN TAFSIRI SUKA FA’DA AKAN WANNAN AYAR TA SURATU YUNUS(A.S):

     

    *1. Ibnul Jauziy(Ba Taimiye Ne, Masanin Hadisi, Kuma Marubucin Litattafai Da Dama) Ya Fada Dangane Da Ma’anar FALALAR ALLAH Da RAHAMARSA Cewar:

     

    ”Dhahhak Ya Ruwaito Daga IBN ABBAS(R.A) Cewar Falalar ALLAH Tana Nufin ILIMI(Kamar Na Al-Qur’ani Da Tauheedi), – Ma’anar RAHAMAR ALLAH Kuma, Shi Ne ANNABI MUHAMMADU(S.A.W)”.

     

    (A duba littafinsa mai suna ‘Zadul Masir Fiy Ilmit Tafsir’ -Juzu’i Na 4 Shafi Na 40).

     

    *2. Abu Hayyan Al-Andalusiy(R.A) Shima Ya Fadi Cewar:”FALALAR ALLAH Tana Nufin ILIMI, RAHAMAR ALLAH Kuma Tana Nufin ANNABI MUHAMMADU(S.A.W)”.

     

    (A duba tafsirinsa mai suna ‘BAHRUL MUHEET’ juzu’i na 5 shafi na 171).

     

    *3. AL IMAM JALALUD-DEEN AS-SUYUTY(R.A) Ya Ce:”Abush-Shaikh Ya Ruwaito Daga Ibnu Abbas(R.A) Yana Cewa:”Ma’anar Falalar ALLAH Ita Ce Ilimi.. Rahamar ALLAH Kuwa, Tana Nufin Annabi MUHAMMADU(S.A.W) Tunda ALLAH Ya Ce:’Wama Arsalnaaka Illaa RAHMATAN Lil’Alameen”.

     

    (A duba littafinsa Ad-Durrul Manthuur, juzu’i na 4, Shafi na 330).

     

    *4. AL-‘ALLAMATUL ALUSIY(R.A) Shi Kuma Cewa Ma Yayi:”ITA KANTA FALALAR MA AI ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) Take Nufi

    Ya Ce: Imamul Khateeb Da Kuma Ibn Asaakira Sun Ruwaito Daga Ibnu Abbas(R.A) Cewar – Ma’anar Falalar ALLAH, Shi Ne Annabi MUHAMMADU(S.A.W)”.

     

    (A duba littafin tafsirinsa mai suna ‘Ruhul- Ma’aniy, juzu’i na 11 shafi na 141).

     

    Wadannan Hamshaqan Malamai Sun Tabbatar Mana Da Cewar Wannan Ayah Ta Cikin Suratu Yunus(A.S) – Ayah Ta 58. Tana Nufin ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) Shi Ne FALALAR ALLAH, Kuma Shi Ne RAHAMAR ALLAH. Kuma Saboda Samuwarsa Ne Ya Kamata Mu Yi MURNA Mu Nuna FARIN CIKINMU, Ba Wai Domin Samun Wani Abun Duniya Ba.

     

    DABARA DAI TA RAGE GA MAI SHIGA RIJIYA…….!

     

    WANNAN DAI NASSIN AL’QUR’ANI NE MAI GIRMA BALANTANA MA ACE KO DA’IFI NE!

    ALLAH YA QARA KARE MU DA SHARRIN BIYEWA SON ZUCIYARMU, DA MAKANTAR ZUCIYA, YA QARA TABBATAR DA DUGA DUGANMU AKAN HANYA MADAIDAICIYA AMEEEEEEN.

Back to top button