INYASS

  • Riko Da Hakikanin Sunnar Manzon Allah SAW A Wurin Shehu Ibrahim Inyass RA.

    Maulana Sheikh Ibrahim Niasse RTA Riƙonsa Da Sunnah.

     

    Imam Hassan Cisse RTA Yace: lokacin da akayi Yaƙin Ramadhan (October, 1973 wanda Kasashen Larabawa suka yaƙi Israel kuma suka ci Nasara ƙarƙashin jagorancin Egypt da Syria).

     

    Imam Hassan yace, Sai Sheikhu RTA ya umurce ni na Rubuta wasiƙar Taya Murna ga shuwagabannin ƙasashen Larabawa tun balle Sarki Faisal (Sarkin Saudia) da Anwar Sadat (Shugaban Ƙasar Egypt) Domin tayasu murnar Munasaabah guda biyu; Munasabar Nasarar Yaƙi da Munaasabar Idin Ƙaramar Sallah, Allah SWT Ya Kimsa mini Kalmomi Masu Daɗi da ma’anoni wajen rubuta wasiƙar sai dai da nazo karshen wasiƙar dana Rubuta ga Sarki Faisal sai nace:

    والاعتماد على الله وبكم

    Ma’ana:

    Dogaro yana ga Allah da ku

     

    Dana kawowa Sheikhu RTA wasiƙun domin ya saka hannu sai ya saka hannu a wasiƙar Anwar Sadat amma banda ta Sarki Faisal sai ya umurce ni dana sake rubuta ta Sarki Faisal kuma na canja wancan Jumlar ta koma:

    الاعتماد على الله ثم بكم

    Ma’ana:

    Dogaro yana ga Allah Sannan daku

     

    Dana tambayeshi Dalili sai yacemin za’a iya amfani da yadda ka rubuta sai dai kawai ta saɓa da abunda yazo daga Sunnah kuma ta saɓa da ladabi ga Allah, Saboda bai kamata ayi amfani da Harafin و da yake nuni izuwa ga daidaito tsakanin abu biyu a janibin Allah da bawa ba, sai dai ayi Amfani da Harafin ثم da yake nuna banbanci tsakani Martabobin guda biyu shi yasa Annabi SAW yace:

     

    لا تقولوا ما شاء اللهُ وشاء فلانٌ، ولكن قولوا ما شاء اللهُ ثم شاء فلانٌ

    Ma’ana:

    Kada kuce Abunda Allah Yaso da Abunda Wane Yaso sai dai kuce Abunda Allah yaso Sannan Abunda Wane Yaso.

     

    Domin Hakan yana nuna “Nufin” na haƙiƙa daga Allah yake shi kuma “Nufin bawa” kawai yana bin bayan Nufin Allah ne.

     

    “Yan uwa wannan shine SHEIKH IBRAHIM NIASSE RTA ƊINMU.

     

    Daga: Aliyu Uthman Bashir

  • Yanda Aka Fara Halartan Taron Mauludi Manzon Allah SAW A Khaulaq.

    MAULUD NABIY 2024

     

    Al’ummar musulmai na fadin duniya a wannan watan na Rabiul Awwal suke gudanar da gagarumin bukukuwan taron Mauludi Manzon Allah SAW don muna murna da watan da aka haife shi a kalandar Hijiriyya.

     

    Dubban mutane daga sassan fadin duniya suna halartan Maulud na Khaulaq dake kasar Senegal wanda Maulana Sheikh Ibrahim Inyass Al-Khaulaq RA ya sassan fadin wafatin sa.

     

    Wanna taro shine na 48 da fara shi wanda yake gudana a Madinatu Baye Khaolack Senegal.

     

    An shirya komai don fara gudanar da wannan taron Mauludi kamar yanda aka saba duk Shekara karkashin Jagorancin Khalifa Muhammadu Mahy Inyass

     

    Allah yasa ayi lafiya alhamdulillah.

  • Sheikh Ibrahim Inyass RA Gwarzon Musulunci Na Zamani.

    Shehu Ibrahim Inyass: Gwarzon Musulunci Na Zamani.

     

    Shehu Ibrahim (RA) ya taimaki addini da kayan zamaninsa da ya tarar wanda Turawan mulkin mallaka suke yin amfani da su. Shi ne farkon Musulmin da ya yi haka. Ya yi amfani da Rediyo, da Tarho, da Rikoda, da Kamara wajen isar da sakon Musulunci. Shehu Ibrahim ne ya wayar mana da kai a kan amfani da wadannan kayan a cikin addininmu na Musulunci. Haka nan amfani da motoci da jirgin sama, da lasifika, da agogo, da zuwa asibitoci.

     

    Shehu Ibrahim yana daga cikin wadanda ya tilasta wa almajiransa zuwa asibiti wanda a da ba a yarda da hakan ba. Sannan ya koyar da yin karatu irin wannan da ake yi na zamani a makarantu.

     

    Shehu Ibrahim (RA) shi ne farkon Musulmi kuma Malami da ya waye ya san cewa “technology” ba kishiyar addini ba ne. Shi ne farkon malamin da ya yarda cewa Turawa sun je duniyar wata a shekarar 1969 (Combo Apolo 11) har ma ya yi littafi a kan wannan. Kuma ya yi wa shugaban Amurka na lokacin wasika a kan Haka, Su Malaman Saudiyya cewa suka yi ma duk wanda ya yarda cewa an je duniyar watan kafiri ne, su kuma na Azahar (Misra) suka ce sam ma ba zai yiwu ba.

     

    Amma Shehu Ibrahim ne ya gamsar da su (da hujja) har suka yarda da Kasancewar Hakan Ya Faru.

     

    Allah Ya Yiwa Shehu Rahama Amiiiin Yaa ALLAH

  • MAULANMU SHEHU IBRAHIM NIASSE (R.A) Ya Halarci Tarukan Addinin Musulunci Da Dama a Fad’in Duniya.

    MAULANMU SHEHU IBRAHIM NIASSE (R.A) Ya Halarci Tarukan Addinin Musulunci Da Dama a Fad’in Duniya.

     

    Sheikh Ibrahim Inyass RA, Kamar Yadda Ya Bayar Da Gudunmowa Wajen Kafawa Da Tafiyar Da ‘Kungiyoyin Musulunci Masu Yawa a Duniya, Kuma Shine Ya Kafa Kungiyar Fityanul Islam Ta Kasa Don Yan’uwa Tijjanawa Suyi Musharaka A Cikin Harkokin Gwamnati A Cikin Kungiyoyin Daya Zama Member Akwai:

     

    •. Da Shi Aka Kafa, Ya Kuma Shugabanci Kungiyar:”Al-Ittihãd Al-Ifríkí Li Du’at Al-Islam”.

     

    •. Mataimakin Shugaba a Kungiyar “Al-Mu’utamar Al-Islãmí Bi Karãchí”, 1964.

     

    •. Kuma Memba a “Rãbidat Al-Ãlami Al-Islãmí”, Makkat Al-Mukarramah.

     

    •. Memba a “Al-Majlis Al-A’alã Li Al-Shu’ún Al-Islãmiyya, Al-Qahira”.

     

    •. Memba a “Jam’iyyat Al-Jãmi’at Al-Islãmiyya, Rabat”.

     

    •. Memba a “Majma’u Al-Buhús Al-Islãmiyya, Al-Qahira”.

     

    •. Memba a “Majlis Al-Islãmiyya Al- A’alã, Aljeriya”.

     

    Akan Irin Wannan Tsari Ya Gina Almajiransa Masu ‘Dimbin Yawa, Wadanda Suke Jagorancin Al’umma a Duk Inda Suke Zuwa Ga Alkhairai Masu Yawa, Lallai Abu Ne Mai Wuya a Iya Kididdige Almajiran SHEHU IBRAHIM NYASS(R.A), Dukansu ALLAH Ya ‘Kara Yarda Da Su.

     

    ALLAH YA ‘KARAWA SHEHU(R.A) KUSANCI GA SHUGABA(S.A.W), YA BA MU ALBARKACINSU AMEEEEEN.

  • Shehu Ibrahim Inyass mutum ne mai bin Sunnar Annabi, duk inda ƙafar Annabi yake bi nan yake. “Inji Ummuhani Ibrahim Inyass.

    Shehu Ibrahim mutum ne mai bin Sunnar Annabi, duk inda ƙafar Annabi yake bi nan yake, idan aka ga saɓanin koyarsa sheɗanci ya shigo ciki.

     

    ……“Inji Ummuhani Ibrahim Inyass RA.

     

    Wanene Shehu Ibrahim Inyass RA ???

     

    SHEIKH IBRAHIM INYASS SHINE MALAMIN MUSULMI NA FARKO & KADAI A DUNIYA WANDA SARKI FAISAL NA SAUDIYYA YA ZIYARA A KAUYEN SA (KAOLACK) A SENEGAL.

     

    Niasse shi ne dan Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci Masallacin Al-Azhar a Masar , bayan da aka yi masa lakabi da “Sheikh al-Islam”. Ya kasance kusa da yawancin Shugabanin masu fafutukar Neman ‘yanci a Afirka ta Yamma saboda gudunmawar da ya bayar na ‘yancin kai a kasashen Afirka.

     

    Shehu Ibrahim ya tsaya tsayin daka wajen yakar mamaya (Imperialism) da sabbi da tsoffin salon mulkin mallaka da kare yancin kasashe da mutuncinsu da kuma ganin sun tsaya bisa kafafunsu, tareda kara dankon zumunci tsakanin Kasashen Africa dana Yankin Asia dama karfafa tsaron Duniya baki daya.

     

    Menene ma’anar Inyass?

     

    Abubuwa 2 da aka gabatar daga Najeriya sun yarda da sunan Inyass yana nufin ” Mutumin kirki ”

     

    Ibrāhīm Niasse (1900–1975) – ko (Faransanci Ibrahima Niasse) , Wolof , Larabci: شيخ الإسلام الحاج إبراهيم إبن الحاج عبد الله التجاني الكولخي‎ التجاني الكولخي Shaykh al-‘Islām al-Ḥājj Ibrāhīm ibn al-Ḥājj ʿAbd Allāh at-Tijānī al-Kawlakhī – ya kasance babban shugaban Senegal (wolof) na Tijānī Sufi na Islama a Afirka ta Yamma . Mabiyansa a yankin Senegambiya suna kiran shi a harshen Wolof a matsayin Baay, ko “uba.”

     

    Niasse shi ne mutumin Afirka ta Yamma na farko da ya jagoranci Masallacin al-Azhar a Misira, bayan an yi masa laƙabi da “Sheikh al-Islam”. Ya kasance kusa da masu gwagwarmayar neman ƴanci da yawa a Afirka ta Yamma saboda gudummawar da ya bayar don samun’ Ƴanci a Ƙasashen Afirka. Ya kasance aboki kuma mai ba da shawara ga Shugaban Ghana na farko, Kwame Nkrumah, da aboko Ga Gamal Abdel Nasser da Sarki Faisal na Saudi Arabia. Sheikh Ibrahim kasance Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya tare da Faisal a matsayin Shugaba.

     

    An haife shi a Ranar Alhamis 8 Ga Watan Nuwamba 1900 a ƙauyen Tayba Ñaseen (wanda aka rubuta lafazin Taïba Niassène a Faransanci), tsakanin garin Kaolack na Senegal da iyakar Gambiya, shi ɗa ne ga Allaaji Abdulaay Ñas (1840-1922), babban wakilin Darikar Sufaye Ta Tijānī wanda galibi ake kira Tareeqat al-Tijjaniyya a, a yankin Saalum a farkon ƙarni na ashirin.

     

    Yatashi Bisa kularwar mahaifinsa, ya Haddace Al-Qur’ani Mai Girma Hannun mahaifinsa A cikin kananan shekaru Yafa wallafa littafi yana da shekaru 21 a duniya.

     

    A lokacin samartakarsa, Sheykh Ibrahim ya sake komawa tare da mahaifinsa zuwa garin Kaolack, inda suka kafa zāwiya (cibiyar addini) na Lewna Ñaseen. Bayan rasuwar mahaifinsa a Lewna Ñaseen a 1922, babban yayan Shaykh Ibrāhīm, Muhammad al-Khalīfa, ya zama magajin mahaifinsa ko Khalīfa.

     

    Shaykh Ibrāhīm mai shekaru 22 ya shafe mafi yawan lokacinsa yana noma a gonar danginsa tare da koyar da yawan almajirai a ƙauyen da ke kusa da Kóosi Mbittéyeen. Duk da cewa Shaykh Ibrāhīm bai taba ikirarin cewa shi ne magajin mahaifinsa ba, saboda kwarjini da ilimin da yake da shi, ya samu dimbin almajirai, kuma rikici ya tashi tsakanin almajiransa da na babban yayansa, Muhammad al-Khalifa.

     

    A cikin 1929, yayin da yake cikin gona a Kóosi Mbittéyeen, A lokacin Yana saurayi, Shaykh Ibrāhīm ya ba da sanarwar cewa an ba shi Mabuɗin Sirrin Ilimin Allah, kuma don haka ya zama Khalifa na Sheykh Tijani a cikin Dokar Tijaniyya, matsayin da ba wanda ya samu A wancan lokacin.

    Daga nan Sheikh Ibrahim ya bayyana cewa duk wanda yake son ya sami ma’arifa, matakin Tabbacin Allah a cikin Darikun Sufaye, dole ne ya bi shi. A shekarar 1930, bayan Sallar al-Fiṭr (karshen watan Ramadān), fada ya barke tsakanin almajiran Shaikh Ibrahim da na Muhammad al-Khalīfa Lamarin da ya sa Shaihin Ibrahim nan da nan ya yanke shawarar komawa tare da almajiransa zuwa sabon wuri.

     

    A wannan maraice, ya tashi tare da wasu rukuni na kusa da almajiransa don nemo sabon wurin zama, washegari kuma suka kafa sabuwar zāwiya a Madina Baay, wani ƙauye wanda daga baya aka sanya shi cikin garin Kaolack mai girma. shehin ya raba lokacinsa tsakanin koyarwa a lokacin rani a Madina Baay da noma a lokacin damina a Koosi Mbittéyeen. A lokacin bazara na Shekarar 1945 ya sake kafa kansa a gidan mahaifinsa a ƙauyensa na asali na Tayba Ñaseen, Ya sake ginawa da sake tsara garin bayan da gobara ta lalata yawancinsa.

     

    Shaharar Shaykh Ibrahim ta bazu cikin sauri a cikin ƙauyuka, kuma mafi yawan almajiran mahaifinsa daga ƙarshe sun zama almajiransa duk da Kasancewarsa ƙarami a cikin iyali. Koda yake almajiransa sun kasance ‘yan tsiraru a cikin Senegal, amma sun kasance mafi girman reshe na Tijānīyyah a duk duniya. A Shekarar Cikin 1930, shugabannin da yawa na Larabawa ‘Idaw ʿAli na Mauritania-ƙabila ɗaya da Su ke Bin Darkar Tijānī Ta Yammacin Afirka, sun bayyana kansu A Matsayin almajiran Shaykh Ibrahim. Sanannen cikinsu shine Shaykhāni, Muḥammad Wuld an-Naḥwi da Muḥammad al-Mishri. Tareeqa al-Tijaniyya al-Ibrahimiyya, kamar yadda aka san almajiran shaikhu, ya bunkasa kuma ya sami ɗimbin mabiya a cikin shekarun 1930s da 1940 a duk Arewacin da Yammacin Afirka.

     

    A shekarar 1937 lokacin da suka haɗu da Shaykh Ibrahim a lokacin aikin hajji a Makkah, Sarkin Kano, A Najeriya, Alhaji ‘Abdullahi Bayero ya yi mubaya’a ga shehin kuma ya bayyana kansa almajirin shaikh Ibrahim. Wannan lamarin ya sa Shaykh Ibrahim ya sami amincewar da yawa daga fitattun shugabannin Tijānīyyah A Arewacin Najeriya da ma wasu da dama wadanda ba Yan Darikar Ba.

     

    Alhaji Abdulmalik Atta – basarake ne daga Okene kuma Babban Kwamishina na farko a Najeriya A Kasar Ingila, yana daya daga cikin manyan almajiran sheik Ibrahim da kuma surukin shehin ta hanyar ‘yarsa Sayyida Bilkisu. Shaykh Ibrahim ya zama sanannen Shaykh al-Tareeqa (Jagoran Darikun Sufaye) a ko’ina cikin yankunan Kasat Hausa na Yammacin Afirka. A ƙarshe, yana da almajirai nesa da Senegal. A lokacin rasuwarsa a 1975 a Landan, Ingila, Shaykh Ibrahim Niass yana da miliyoyin mabiya a duk Yammacin Afirka. Ya Rasu 25 Ga Watan Yuli A St Thomas’ Hospital, London, United Kingdom 🇬🇧. Yana Da Shekaru 75 A Duniya, A Rayuwar Ya Rubuta Litattafan Addini 75. Ya Haifi Ya’ya 75.

     

    Dalilin Zuwan Sheikh Ibrahim Inyass Ne, Aka Samu Hutun Bikin Maulidin Manzon Allah SAW A Najeriya.

     

    Sanadiyar Shehu Ibrahim Inyass RTA Ne Gwamnatin Najeriya Ta Sanya Hutun Maulidi Ya Zamo Doka A Kasa, Bayan Shehu Ya Zo Taya Najeriya Murnan Samun ‘Yanci A Shekarar 1960

     

    Bayan Kasar Najeriya ta samu ‘yanci daga mulkin Turawa, Shehu Ibrahim Inyass RTA ya kawo ziyara Najeriya na musamman domin taya murnan samun ‘yanci, da Shehu ya gana da Firar minista na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, sai Shehu ya bashi shawara cewa tunda kai Musulmi ne, ya kamata ka sanya ranar Maulidi ya zamo ranar hutu a Najeriya domin murnar zagayowan ranar da aka haifi Annabi Muhammadu SAW, kamar yanda abokinka Shugaban Kasa wato (Head Of State) Namdi Azikiwe yake hutun Kirsimeti, nan da nan Sir Abubakar Tafawa Balewa Ya Aika Da Wannan Dokar Majalisa, Bayan Anyi Zafaffiyar Mahawara Daga Karshe Dai Majilisa Ta Amince A Ta ke Tafawa Balewa Ya sanya Hannu A wannan doka. Wannan shine dalilin da yasa duk ranar maulidi gwamnati ke bada hutu.

     

    Daga; Dr. Saliadeen Sicey

Back to top button