KISSA

  • Ga Kadan Daga Cikin Abinda Ya Fada A Lokacin Ziyarar Da Yakai Kasar Palestine Shekara 1966.

    Sheikh Ibrahim Inyass (RA) A Cikin Ziyarsa A Masallacin Kudus Na Falasdin A Shekarar 1966. Ga Kadan Daga Cikin Abinda Ya Fada A Lokacin Ziyarar:

     

    Na sami alfarmar yin Sallar Juma’a a cikin masallacin Aqsa (Kudus) da Wazifa mai tsarki a karkashin Dutsen Sakhrah mai albarka, daga in da Manzonmu (SAW) ya tafi Mi’iraji.

     

    Ni da kaina ina kallon bala’in Falastin (Palestine 🇵🇸) a cikin zurfin rai na. Kudus tana wakiltar Zuciyar Al’ummar Musulmi, a gareni.

     

    Kudus tana bukatar mazaje masu tsarkin zuciya kwatankwacin Irinta Sayyidna Umar (RA), ba ’yan siyasa masu son duniya ba.

     

    Za a ci gaba da Jihadi a kewayen Baytul Maqdis har zuwa ranar sakamako, kamar yadda ya tabbata a Hadisi.

  • KISSA: Kissan Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA Da Wasu Jikokin Sa.

    Wasu Kananan Yara Daga Cikin Jikokin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi Suka Aikata wani karamin Laifi su Uku Ana Sallah sai Suka Kunna Famfo sunata Wasa da Ruwa Bayan Idar da Sallah sai Maualana Sheikh yasa

     

    Aka kirawosu gabansa yace a samo bulala sai yace dasu meye yasa ana Sallah Kuna Wasa sai Suka kasa magana sai Shehu yace ya’yan waye sai a kace Akaramakallh dan-wane -ne da Dan wane Cikin ya’yan Maualana Sheikh sai maulana Sheikh yace meye Sunanku sai daya.

     

    Yace sunana Muhammadu dayan yace Ahmad Tijjani dayan yace Ibrahim Inyass sai babu bata lokaci Shehu yace dasu Ku tashi ku tafi kunci Albarkacin masu Sunanku ko sunana Shehu Ibrahim Inyass R T.A. Shehu baya iya kira haka

     

    Gatsau sai dai Idan karatu ya biyo takai shiyasa ma yake Kiran khadimul Faida da Suna Shehu saboda takwarane ga Shehu Ibrahim Inyass R.T.A. to bari Kuma Shugaban Halitta Annabi Muhammadu S.A.W.. yakamata a kula Allah ya kiyaye mana Imanimmu don Alfarmam Annabi Muhammadu S.A.W.

     

    Daga: Abubakar Ibrahim Wunti

  • KISSA: Kissan Wani Dattijo Dan Shekara 80 Bayan Ya Dawo Daga Masallaci Sallar Isha’i.

    Dattijo ɗan shekara 80 ya dawo daga Masallaci Sallar Isha’i. Ya yi ta buga ƙofa amma matarsa ba t ji ba har ya gaji, JIRI ya ɗebe shi ya faɗi a wurin…!

     

    Bayan lokaci wannan matar taga mijinta ya yi jinkiri da yawa, sai ta leƙo waje ta gan shi a sume. Bayan ya farfaɗo ta yi ta ba shi haƙuri, tana cewa wallahi bata ji bugu ba…!

     

    Ya ce, ba na suma ba ne sanadiyyar tsayuwa ko gajiya ba, a’a, kawai ji na yi a raina, ya ya halina zai kasance in naje Lahira aka rufe mini ƙofar Aljanna, wannan tsoron ne yasa na suma…!

     

    Allah yasa mu gama da duniya lafiya, ya Bamu gidan Aljannah. Amiin Yaa ALLAH

     

    Daga: Sukairaj Hafiz Imam

  • KISSA; Kissan Sahabin Manzon Allah Abu Huraira Da Annabi Muhammadu SAW.

    ALBARKACIN HANNAYEN ANNABI (S.A.W).

     

    SAYYIDUNA ABU-HURAIRA (RTA) YACE:

     

    “Watarana nazo wajen ANNABI (S.A.W) da wani dabino dan kadan, Sai nace Masa :

     

    “YA RASULALLAHI YI MIN ADDU’A MANA, KA ROQA MIN ALBARKA ACIKIN WANNAN DABINON NAWA” Sai ya kar’ba, ya sanya shi a tsakanin hannuwansa, sannan yayi addu’a.

     

    Sannan yace min: “KAR’BI, KA SANYA SHI ACIKIN JAKAR DA KAKE ZUBA GUZURINKA ACIKI. KUMA DUK LOKACIN DA ZAKA CI DABINON, KA SANYA HANNUNKA KA DEBO DAGA CIKIN JAKAR, AMMA KAR KA JUYE”.

     

    Sai nace “to”.

     

    “Wallahi Sai da na rika ciyar da mutane masu yawa, kuma ina yin sadaqah daga cikin wannan dabinon. Kullum aciki nake ci nake sha. Ban ta’ba rabuwa da wannan jakar ba. Duk inda zanje tana nan a kwuibi na.”

     

    Na ci-gaba da cin Wannan dabino (Babu yankewa, babu Qarewa), Har ANNABI (S.A.W) yayi wafati, Har Tsawon lokacin Khalifancin Sayyiduna Abubakar Da Sayyiduna Umar, da Sayyiduna Uthman. (Allah ya yarda dasu)”

     

    Yayin da Aka kashe Sayyiduna Uthman (R.A), Sai jakar ta Fadi daga Hannu-na.” (Tsawon SAMA DA SHEKARA ASHIRIN KENAN).

     

    “Shin kuna so in gaya muku ko buhu nawa na fitar naci daga cikin Wannan jaka?”

     

    “WALLAHI NA CI SAMA DA BUHU DARI BIYU”.

     

    AWATA RUWAYAR KUMA, ABU HURAIRA (R.T.A) Yace: “Watarana (awajen yaki) ANNABI (S.A.W) Yace min

     

    “KIRA MIN MUTUM GOMA”

     

    Sai naje na kira su, Suka ci, Suka ci sai da suka Qoshi, Sannan yace In Sake kiran wasu Mutum goma din, su ma suka ci, Suka ci sai da suka Qoshi. Da haka Sai da Gaba dayan rundunar Kowa yaci dabinon nan ya Qoshi, Amma Dabinon yana nan kamar yadda yake tun farko” (BAI RAGU BA).

     

    A WATA RUWAYAR KUMA YACE:

     

    “MUSIBU GUDA UKU NE SUKA TA’BA SAMU NA AMUSULUNCI WADANDA BABU KAMARSU:

     

    1. WAFATIN ANNABI (S.A.W).

    2. KISAN SAYYIDUNA UTHMANU.

    3. FADUWAR WANNAN JAKA”.

     

    • Hadisai ne ingantattu, aduba musnad na Imamu Ahmad bn Hambal, juzu’i na 2, shafi na 352.

     

    • Tirmidhy ma ya kawo shi acikin Manaqibu abu huraira.

     

    •Sannan Imamul Baihaqy ma ya kawo shi a cikin

     

    Dala’ilun Nubuwwah, Juzu’i na 6, Shafi na 110 zuwa na 111.

     

    Allah ya barmu da ANNABI S.A.W. AMEEEEN..

  • Professor Ibrahim Ahmad Maqari Hafizahullah Ya Bada Kissan Wani Sarki Haruna Rasheed.

    PROFESSOR IBRAHIM AHMAD MAQARI ZARIA A CIKIN TAFSIRIN SA YACE :-

     

    Daga Babangida A. Maina

     

    Watarana Sarki Haruna Rasheed, Ya Gayyaci Wani Malami Domin Yazo Yayi Masa Wa’azi, Ayayin Da Wannan Malami Yazo, Sai Yace Da Sarki Haruna Rasheed “Ni Wa’azina Mai Zafine,Fa”

     

    SAI SARKI HARUNA RASHEED, YACE DA WANNAN MALAMI “TO KARIKE WA’AZIN KA MAI ZAFI” BANA BUKATA.

     

    YA KARA DA CEWA ” Allah Ya Tura Wani Bawan Sa Wanda Yafika Daraja Zuwa Ga Bawan Da Yafini Zunubi Da Sabawa ALLAH, Amma Sai ALLAH Yace Idan Wannan Dan Aike Nasa Mai Daraja Yaje Zuwa Ga Wannan Bawa Ma’abocin Manyan Zunubai, To Ya Kirashi Da Zance Mai Tausasa Zuciya “Kaulan Layyilan ( Zance Mai Dadi).

     

    WATO DAI WANNAN SARKI, YAYIWA WANNAN MALAMI ISHARA NE DA TARIHIN ANNABI MUSA (as) DA FIR’AUNA, AYAYIN DA ALLAH YA AIKI ANNABI MUSA ZUWA GA FIR’AUNA SAI YACE DASHI “IDAN KAJE KA YI MASA ZANCE MAI KYAU” NA TAUSASAWA DA LADABI YAYIN KIRAN SA ZUWA GA ALLAH.

     

    ASHE KENAN GA DUK WANI MALAMI, KOMIN GIRMAN ZUNUBIN MAI ZUNUBI, IDAN AKAJE YI MASA KIRA TO ANAI MASA KIRANE TA HANYAR TAUSASA MURYA DA KUMA ZANCE MAI KYAU DA NASIHA

     

    KAMAR YADDA ALLAH YACE

     

    ﺍﺩْﻉُ ﺇِﻟَﻰٰ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺭَﺑِّﻚَ ﺑِﺎﻟْﺤِﻜْﻤَﺔِ ﻭَﺍﻟْﻤَﻮْﻋِﻈَﺔِ ﺍﻟْﺤَﺴَﻨَﺔِ ۖ ﻭَﺟَﺎﺩِﻟْﻬُﻢْ ﺑِﺎﻟَّﺘِﻲ ﻫِﻲَ ﺃَﺣْﺴَﻦُ ۚ ﺇِﻥَّ ﺭَﺑَّﻚَ ﻫُﻮَ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﻤَﻦْ ﺿَﻞَّ ﻋَﻦْ ﺳَﺒِﻴﻠِﻪِ ۖ ﻭَﻫُﻮَ ﺃَﻋْﻠَﻢُ ﺑِﺎﻟْﻤُﻬْﺘَﺪِﻳﻦ

     

    Kayi Kira Zuwa Ga Hanyar Ubangijin Ka Da Hikima Da Wa’azi Mai Kyau Kuma Kayi Jayayya Dasu Da Magana Wadda Take Mafi Kyau Lalle Ne Ubangijin Ka Shine Mafi Sani Ga Wanda Ya Bace A Hanyar Sa Kuma Shine Mafi Sani Ga Masu Shiryuwa

     

    ALLAH YASAKA DA ALKAIRI PROFESSOR ALLAH YAKARA YAWAN ILMI DA BASIRA DAN ALFARMAR MANZON ALLAH (SAW). AMIIIIN

Back to top button