LAFIYA A MUSULUNCI

  • GENOTYPE A MUSULUNCI TARE DA BINCIKEN MASANA KASHI NA UKU (3)

    GENOTYPE A MUSULUNCI (3)

    *

    A rubutun farko da na biyu, mun fahimci asalin samuwar mutum a fuskar musulunci da fuskar kimiyya, mun fahimci menene muhimman abubuwan da genotype ya ƙunsa da kuma maniyyi da abinda ya ƙunsa.

     

    A wurin yan kimiyya, genotype shine alamu na launin protein da ake samu a cikin RBC (red blood cell), sun raba genotype gidaje daban-daban daga biyar zuwa ashirin da wani abu gwargwadon binciken su akan “haemoglobin” wanda ake samu a RBC, mafi shahara sune AA, AC, AS, CC, SC da kuma SS.

     

    Sun tabbatar cewa mutane masu genotype din SC da SS sune masu cutar sickle cell (sikila), kuma babu makawa muddin iyaye suna da wannan genotype din (ko AS wanda ake tsammanin zasu haifar da sikila) suka yi aure, yara sikila zasu haifa, kawar da haka kuwa sai dai suyi amfani da “In vitro fertilization” wurin samar da ciki, ko kuma a kwashe jini da ɓargon mai cutar, a musanya da lafiyayyen jini da ɓargo.

     

    A MUSULUNCI KUWA

     

    Dole ne dukkan mumini ya yarda da

    وما تحمل من أنثى ولا تضع إلا بعلمه

    Wato “babu macen da zata dauki ciki ko ta haife cikin sai da sanin sa (Allah)”. Shiyasa za kaga wasu wayanda Allah bai nufa da samun haihuwa ba, in suka je asibiti sai likitocin suce tabbas lafiyan miji da matan kalau, to in lafiya suke me ya hana samun cikin?

     

    Bayan iznin Allah a harkar haihuwa, sai matakin samun cikin, wanda ya fara daga fitar Maniyyi (نطفة) daga namiji zuwa shigar ƙwayar maniyyin (سللة) cikin mace inda zasu hadu da ƙwayar haihuwar mace su zama (نطفة امشاج), daga nan Allah (da kansa) zai mayar dashi gudan jini, ya mayar dashi tsoka, ya fidda mashi siffofi, ya busa masa rai, ya bashi alqawari sannan a haife shi, (kamar yadda yazo a wurare da dama a Alqur’ani).

     

    Tabbas Annabi SAW ya hori al’umma da zaben uwa ta gari, domin yaro yana gadon halayya da suffa da cuta (irin kuturta) daga iyaye musamman uwa, amma kuma Allah da Annabi sun nuna abubuwan dake haifar da samun ya’ya marasa lafiya ko muni ko rashin tarbiyya da albarka, daga cikin su akwai:

     

    1. IKON ALLAH: Domin jarraba imanin mumini, Allah yakan fitar da rayayye daga matacce kuma yakan fitar da matacce daga rayayye, kamar yadda ya jarrabi Annabin sa da samun “kana’ana”.

     

    2. CIN HARAM: Hadisai mabanbanta sunyi nuni da illar haram ga JIKI da IMANIN musulmi, har a wani hadisin ma Annabi SAW ya nuna addu’ar mutum maciyyin haram bata karɓuwa, kuma maniyyi ana samar dashi ne daga abincin da iyaye suka ci, Idan har haram zai hana addu’ar ka karɓuwa, me zai sa ya kasa gurɓata maka ƙwayoyin haihuwar ka?

     

    3. SHAIDANI: Annabi SAW ya tabbatar akwai shaidanin aljani wanda yake saduwa da matar mutum yayin da mijin nata yake saduwa da ita muddin bai yi addu’a ba kafin ya fara jima’in, kuma tare da aljanin zai saki maniyyi a cikin matar tashi, haduwar maniyyin aljanin da nasu zai sa su haifi yaro mara lafiya ko mara jin magana da sauran su.

     

    MAFITA

    1. ABINCI: Kwayoyin haihuwa suna samuwa ne daga abinci, shiyasa a hadisai mabanbanta Annabi yayi nuni da tasirin dabino, zuma da nono ga lafiyar jikin mutum, musamman mace mai ciki, cin dabino sau uku da safe, yana sa mace ta haifi yaro lafiyayye kuma kyakkyawa.

     

    2. MAGANI: idan kuna da mutum mai fama da cutar sikila, turawa basu da magani, Amma Annabi SAW yana da magani, ya tabbatar a hadisi cewa Suratul Fatiha tana maganace kowacce irin cuta, Imam Nazifi Alqarmawiy Kano ya kawo fa’idar fitsarin raqumi daga Annabi SAW. Malaman lafiyar musulunci sun tabbatar rubuta suratul fatiha sau 41 a wanke da ruwan zam-zam (3 litres) a zuba fitsarin raqumi (murfin bottle water) guda uku, a sha da safe minti 15 kafin a ci abinci, za a warke daga cutar sikila ko wanin sa wanda ya shafi kwayoyin halitta da IZNIN ALLAH.

     

    DAGA KARSHE

    Mai hankali zai fi gaskata turawa saboda a zahiri suna da na’ura kuma suna gwaje-gwaje, amma kar ka manta a gwaje-gwajen nasu ne suka zurfafa har suka saɓawa addinin ka. A wurin su asalin mutum ba yadda Ubangijin ka ya fada suka yarda ba, basu yarda da illar haram ko tasirin halal ba, basu yarda da shafar aljanu ko sihiri ko maita ba, basu yarda wani abu zai iya faruwa ko rashin faruwa bisa iznin Ubangijin ka ba.

     

    ABINDA AKE GUDU AKA HANA MUSULMI ZIYARTAR BOKAYE DON KAR SU YARDA WANI HALITTA NE YA HANA SU KO YA BASU WANI ABU BA DA IZNIN ALLAH BA, YANA FARUWA DA JAMA’A DA YAWA SABODA ZIYARTAR MASU KIMIYYAR TURAWA, SUNA GANIN AMSAR KIMIYYA GA MATSALOLIN SU ITACE MAFITA TA KARSHE BA QUDURAR ALLAH BA.

     

    Note: Bana jayayya da kowa, nayi rubutun nan ne don in karfafi imanin musulmai kawai.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • GENOTYPE A MUSULUNCI TARE DA BINCIKEN MASANA KASHI NA BIYU (2)

    GENOTYPE A MUSULUNCI (2)

    *

    ***A rubutun farko, daliban likitanci ko genetics za su iya ganin cewa nayi bayanin a gurgunce, ƙila haka din ne, amma ni nufina kawai inyi sharar fage ne kawai don mai karatu ya gane tushe da inda yan kimiyya suka yi tsalle suka bar Musulunci, ba koyar da genetics zan yi ba ballantana inyi komai filla-filla.

     

    A Musulunci, Annabi Adam A.S asalin sa yumɓu ne da ruwa suka samar da jikin sa, haske da iska suka samar da ruhin sa, wannan ake kira “Elements of creation” wato sinadaran halitta, sune Earth, Water, Fire/Light da kuma Air. Abinda mutum yake ci (Earth) da abinda yake sha (water) da samun hasken rana ko zama cikin duhu (light/fire) da iskar da yake shaƙa (Air) suna da tasiri a jikin sa, sune suke inganta lafiyar sa ko sanya shi ciwo.

     

    In aka yi binciken kwayoyin halitta a jikin Nana Hauwa, za a tarar da kaso mai yawa na kwayoyin halittar Annabi Adamu domin Allah ya halicci Nana Hauwa ne daga ƙashin haƙarƙarin Annabi Adamu, Amma ba tsaga jikin Adamu akayi aka ciro haƙarƙari aka halicci hauwa ba, kawai Allah yaso hakan ya faru ne kuma ya faru, cikin IKON SA.

     

    Amma sauran yayan Annabi Adam da hauwa (mutane), ba kwaɓa su akayi kamar yadda akayi wa Adamu ba, ba samar dasu akayi daga jikin Adamu kamar yadda aka yiwa Hauwa ba, Alaƙar jiki da jiki cikin sha’awa (jima’i/sex) ne ya samar da su ta sanadin MANIYYI daga Namiji, da ginuwar jiki da ruhi a CIKIN mace (buɗuni ummahatikum).

     

    MENENE MANIYYI?

    Maniyyi shine Sperm/Semen (a turanci). Musulunci ya fassara shi a matsayin farin ruwa mai kauri wanda yake tunkudo kanshi daga al’aura saboda sha’awa mai ƙarfi ta hanyar jindadi (jima’i) ko Al’ada (mafarki). A Qur’ani, maniyyi shine nuɗfa (نطفة), yana fitowa ne daga tsakanin ƙashin baya da haƙarƙari (yakh-ruju min bainis sulbi wat-tara’ib).

     

    A cikin Maniyyi (sperm/semen), Akwai “Sulalah” shine Spermatozoon (jimlar sa kuma spermatozoa), shine kimiyya ke cewa guda daya ne kawai cikin miliyoyin yan’uwan sa yake nasarar shiga cikin mace inda matakin juna biyu ke farawa, lallai haka ne a musulunci.

     

    Spermatozoon shine sperm cell, yana da chromosome 23, in ya shiga cikin mace ya riski ƙwanta, sai su haɗe (shine nuɗfa’tun amshajin), itama ƙwan nata yana da chromosome 23, daga nan matakin ciki ke farawa, bayan sun samar da chromosome 46.

     

    A gurguje, sharan fagen da zanyi kenan kan tushen mutum a fuskar addini da kimiyya, da matakin samun ciki. Yanzu yaya ake samun lafiyyen yaro a ciki, tun daga shigan maniyyi har haihuwa a fuskar musulunci, shine rubutuna na gaba Insha Allah.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
  • GENOTYPE A MUSULUNCI TARE DA BINCIKEN MASANA KASHI NA DAYA (1)

    GENOTYPE A MUSULUNCI (1)

    *

    Ilimin kimiyya abune karɓaɓɓe a musulunci sai dai hanyoyin samu ko tabbatar da ilimin ne ya kan iya cin karo da koyarwar musulunci, kafin in shiga bayani akan genotype, yana da kyau mu san wannan

     

    WAYE MUTUM?

    A wurin duk cikakken musulmi, Annabi Adam ne mutum na farko kuma uban dukkan mutane, Sannan Allah ya halicce shi ne a sama daga “yumɓu/laka”, ya shigar dashi aljanna sannan ya saukar dashi duniya shi da matar sa suka haifi yara. Amma a wurin kimiyar turawa, mutum shine duk wani halitta da yake a jinsin “Homo” (kalmar Latin dake nufin mutum) kuma jinsin homo na farko shine “homo habilis” wayanda suka rayu miliyoyin shekaru kafin zuwan Annabi Adam A.S.

     

    A wurin su, mutum na farko (homo habilis) kama yake da biri, haka yayi ta samun kyautatuwan halittar sa har ya dawo suffar mutanen yanzu (modern human) wayanda suke kira “homo sapien”.

     

    Turawan sun yi bincike na DNA ne akan ragowar jikin halittun da suka tono/samo wayanda suka rayu miliyoyin shekaru a duniyar nan kafin saukowar Annabi Adam shiyasa suka fadi haka. Tabbas sun nufo gaskiya amma cikin duhu, domin basu san cewa Allah ya aiko mala’iku duniya suka dibo mai ƙasa mabanbanta domin kwaɓa halittar jikin Annabi Adam ba, shiyasa ba abin mamaki bane don sun samu DNA din halittun da suka fara zama a duniya kafin zuwan Annabi Adam a jikin mutanen yanzu.

     

    Duk wanda ya fahimci wannan, zai gane ba za a samu cikakken bayanin halittar ɗan adam a wurin bature ba, dole sai an waiwaya musulunci.

     

    MENENE GENOTYPE?

    Genotype yana nufin “Dandali ko dunkulen sinadarai/kwayoyin da suka samar da halitta (organism)”, sun ƙunshi abubuwa kamar haka:

     

    A) “CELL” shine mafi ƙanƙantar ƙwayar halitta dake iya rayuwa da kanshi kuma shine yake haduwa ya samar da halitta mai rai (living organism). Cell yana da sashi uku, sune Membrane, nucleus da cytoplasm.

     

    B) “GENE” shine asalin sashi (basic unit) na gado (heredity) wanda yake zuwa ga yara daga iyayen su, wato gadon suffar jiki da halayya. Shi wannan “Gene” din ya kunshi na’ukan DNA (Deoxyribonucleic acid) wayanda aka jera su daya bayan daya.

     

    C) Chromosomes shine sashin da aka jera Gene, kuma yana cikin sashin NUCLEUS na jikin kwayar halitta (cell).

     

    Akwai kwayoyin Gene aƙalla guda 955 a cikin kowani Chromosome ɗaya, A cikin Nucleus din kowani ƙwayar halitta (cell) akwai chromosomes guda 23.

     

    Genotype shi yake haifar da “Phenotype” wanda yake nufin Halayya/dabi’a ko wani abu wanda halitta (organism) ta kunsa ko ta nuna.

     

    Da wannan ilimin ne ake iya gane wane kaza genotype din shi kaza ne, wane kaza ma genotype din shi kaza ne, sannan da yiwuwar su haifi yara iri kaza.

     

    A RUBUTU NA GABA ZA MU KAWO YADDA SUKE A MUSULUNCI DA KUMA YADDA ZA A TSALLAKE MATSALAR RASHIN DACEWAR SU INSHA ALLAH.

     

    ✍️ Sidi Sadauki

    Share
Back to top button