MAULUD

  • Dubban Miliyoyin Masoya Annabi Muhammadu SAW A Garin Gombe Sun Gudanar Da Zagayen Takutaha 2024

    GOMBE TAKUTAHA 2024

     

    Al’ummar Musulmi Sun Gudanar Da Gagarumin Taron Zagayen Takutaha A Kofar Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar Na III Don Nuna Murna Da Ranar Suna Don Samuwar Fiyayyen Halitta SAW.

     

    Taron Zagayen Takutaha Wanda Shine Karo Na Shida Wanda Mai Martaba Sarkin Gombe Yake Shiryawa Tare Da Kungiya Shu’ara’ul Islam Ta Jihar Gombe Wanda Alhaji Barhama Adamu Damanda Yake Shugabanta.

     

    Mutanen Sun Samu Halarta Tare Da Nuna Farin Cikin Su Da Wannan Taro, Tare Da fatan Alkhairi, Allah Ya Maimata Mana.

     

    Hakimai Da Wasu Rike Da Sarautun Gargajiya Sun Samu Halarta Tare Da Manyan Malamai, Limamai, Da Jami’an Gwamnati Harma Da Jami’an Tsaro.

     

    Islamiyoyi Da Sha’irai Da Masoya Sune Suka Gudanar Da Zagayen Kamar Yadda Aka Saba Duk Shekara, An Gabatar Da Jawabai Da Nasihohi A Yayin Taron.

     

    ALLAH ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW, ya maimaita mana albarkan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiin

     

    Tijjaniyya Media News

  • Dubban Miliyoyin Masoya Manzon Allah SAW Ne Suka Gudanar Da Zagayen Mauludi A Garin Manumfashi.

    LABARI CIKIN HOTUNA:

     

     

    An gudanar da zagayen Maulidi a garin Malumfashi a jihar Katsina domin tunawa da zagayowar watan haihuwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

     

     

     

     

    Mabiya Manzon Allah SAW A fadin duniya suna gudanar da tarukan Mauludi Annabi ﷺ don tunawa da ranar da aka haife shi.

     

    A Najeriya kuma mafi yawan mutane dake arewacin Najeriya kashi 85% suna gudanar da wannan taruka na Mauludi a watan Rabiul Awwal duk shekara.

     

     

     

    Allah ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW A Rayuwar mu baki daya. Amiin Yaa ALLAH

     

    📸 -Ɗan Hausa Photography

  • Zaman Maulidi A Madinatu Munawwara Dake Saudi.

    BIDIYO: Zaman Maulidi daga Madinatul Munauwara dake kasar Saudi Arabia A Ranar Alkhamis 16-Rabiul Auwal – 1446 / 19-09-2024.

     

     

    Allah ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW. Amiin Yaa ALLAH

  • Sheikh Tijjani Zangon Bare Bari Shine Ya Fara Assasa Zaman Maulidi A Kasar Hausa.

    Game Da Zama A Gudanar Maulidin Annabi Shi Ya Fara Asssawa A Kasar Hausa.

     

    Sheikh Malam Tijjani Usman Zangon bare-bari Kano (RTA) yana da kamashon lada a duk taron maulidin da a kai a yankunan kasar Hausa da kewayenta saboda shi ya assasa zaman ana karanta sira wato tarihin Annabi Muhammadu SAW da kissoshi akan rayuwar Manzon Allah SAW.

     

    Sheikh Tijjani RA babban shehin malamin addinin islama ne kuma jagora a Darikar Tijjaniyya wanda ya bada gudumawa a bangarorin yada addinin islama a afrika dama duniyar Musulunci.

     

    Allah ya saka masa da Alkhairi ya jaddada rahma a gare shi albarkan Annabi ﷺ. Amiin

  • Na Sha Faɗin Haka, Duk Wanda Ba Ya Maulidi Ba Musulmi Ba Ne – Farfesa Maƙari 

    Na Sha Faɗin Haka, Duk Wanda Ba Ya Maulidi Ba Musulmi Ba Ne – Maƙari

     

    “Saboda Maulidi Manzon Allah (SAW) shine mujarradin murna da samuwar Manzon Allah (SAW) daka yi murna da samuwar Manzon Allah ko cikin zuciyarka kayi maulidi, kuma zaka samu lada.

     

    “Malamin ya ci gaba da cewa; sai dai hanyar daka gudanar da murnar ta yaya kayi wannan shine ake samun bambanci, wasu suna fitowa a ranar sha biyu ga watan suna raya ranar da bukukuwa, wasu kuma suna ciyarwa duk a domin Manzon Allah (SAW).

     

    “A Ƙarshe malamin ya ƙara da cewa; ba mai yiwa Manzon Allah (SAW) hidima matsayinsa na masoyi tamkar cikakken Mùsùlmì, ya zama tilas mu nuna murna da ranar da aka haifesa.

     

    ALLAH ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW. Amiin Yaa ALLAH

Back to top button