MAULUD

  • GWANIN BAN SHA’AWA: Yadda Kananan Yara Suka Gudanar Da Mauludin Manzon Allah a Zariya. 

    GWANIN BAN SHA’AWA: Yadda ƙananan yara suka gudanar da maulidin manzo a Zariya.

     

    Daga Barista Nuraddeen Isma’eel

     

    “Wani abun ban mamaki na wasu ƙananan yara wanda duk cikarsu haifaffun garin Zaria ne jihar Kaduna, inda suka sabunta maulidin Fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (SAW).

     

    “Shi dai wannan maulidin na ƙananan yaran sun saba gudanarwa a duk shekara kamar yadda rahoton hakan ke riskan Alfijir Hausa.”

     

    Yadda al’amarin maulidin ke tafiya cikin tsari da ƙayatarwa a halin yanzu haka, ganin yadda yaran ke gayyatar yayasu-yayasu Sa’o’in juna daga unguwanni daban-daba domin halartar wannan gagarumin Mauludin.

     

    “Rahoton na cigaba da bayyanawa kamar haka harda gagarumin walima da yaran ke shiryawa bayan kammala maulidin Fiyayyan halitta Annabi Muhammadu ( SAW).

     

    “Wannan maulidin ya gudanane a ranar juma’a 11/11/2022 a bakin kasuwanci Zariya cikin wani unguwa da ake kira a unguwar ƙarfe Gidan Hajiya ladi mai waina.”

     

    Allah ya saka masu da mafificin alkhairi, ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW. Amiiiin

    Share
  • An Sanya Maulidi Cikin Kundin Tsarin Tarukan Da Za’a Rinƙa Gabatarwa Duk Shekara A Saudi Arabia .

    Hukumomin Kasar Saudi Arabiya Sun Sanya Bikin Maulidi Cikin Jadawalin Taruka A Fadin Kasa.

     

    A wannan shekara 1444 AH ne hukumomin kasar Saudi Arabiya suka shirya taro na musamman a watan Rabi’ul Awwal (Mauludi) da sunan Maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW wanda suka gayyaci malamai sama da ɗari da hamsin 150 waɗanda aka gayyato daga ƙasashe hamsin a faɗin duniya kuma ya ɗauki ƙwanaki ana gabatarwa kuma sukayi ma taron Maulidin da laƙabi da taken:

     

     

     

    “ƊA’A TARE DA DARAJOJI A CIKIN RAYUWAR MANZON ALLAH MAI TSIRA DA AMINCI DA KUMA TASIRINSU GA DUNIYA GABA ƊAYA”

     

    “القيم الاخلاقية في السيرة النبوية واثرها في قيم السلام العالم”

     

    Cikin wadanda suka gabatar da jawabai akwai Maulana Prof. Ibrahim Maqary, shima yana ɗaya daga cikin malaman da aka gayyata kuma ɗaya daga cikin ginshi ƙai a gurin gabatar da taron wanda ya ƙunshi bijiman malamai masu jawabi a yayin gudanar da taron Mauludin.

     

     

     

    Tabbas hukumomin Saudi Arabiya sun taka muhimmiyar rawa tare da namijin ƙoƙari gurin yin watsi da halatta ko rashin halattar yin murnar maulidin fiyayyen halitta saw tare da sanya shi a cikin kundin tsarin tarukan da za’a rinƙa gabatarwa duk shekara a kuma cikin watan da aka haifi fiyayyan halitta Annabi SAW.

     

    Muna murna ne kawai saboda an girmama fiyayyan halitta Annabi Muhammadu SAW a gurin daya kamata ace nan ne tushen daya kamata su ƙarfafa sha’aninsa, AlhamdulilLah sannu dai a hankali abu nata samun tagomashi fiya da tunanin mu kuma dama munsan a hankali za azo gurin, In shaa Allah.

     

    Allah ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah SAW tare da ahalin gidansa da masu biye musu da ƙyautatawa har ya zuwa ranar sakamako, yasa muna cikin cetonsa. Amiin

     

     

     

    Daga Imam Anas

    Share
  • Duk Cikin Idin Sallar Babu Kamar Idin Samun Manzon Allah (SAW) Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA

    Duk Cikin Idin Sallar Babu Kamar Idin Samun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

     

    Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi RTA yace; Shehu Ibrahim Kaulaha RTA yana cewa:

     

    Duk wani Murna/idi yana zuwa ne bayan wani alkairi da aka samu Azumin watan Ramadan da muke murna ne da samun Alkur’ani, Idin Sallahr Azumi murna ne da kammala azumin lafiya, Idin Babbar Sallah (Layya) murnane na (Yan’uwan mu sun hau hajji sun sauka lafiya), Sallar Juma’a Idin sati kenan Murna ne na Allah ya bamu daman yin Sallar harna tsawon sati.

     

    Shehu Ibrahim RTA: yace ni kuma agu na babu wani Alkhairin da yakai Samun Annabi Muhammadu SAW a duniya, saboda haka Maulidin/Murna da samunsa yafi kowanne idi.

     

    Shehu yakara da cewa: Haka kuma Shehu Ibrahim RTA yake girmama Maulidin Annabi SAW ya daukeshi babu abinda ya kaishi a cikin Iduka, harma duniya tazo tai ta koyi da irin shirin Maulidin sa da ya keyi. Ko anan Nigeria da ba’asan Maulidi ba ana kiransa, A Kano Takutaha, Wani wuri Babbar Sallah, wani wuri kuma Sallahn Kaji da sauran su, to idan Muqaddamai sun je Kaulaha sun ga yadda Shehu Ibrahim keyin Maulidi in sun dawo Nigeria sai suke koyi dashi, haka nan in kowa ya gani sai yayi tambaya wai shin wannan kam meye ne ??

     

    Ace musu ai Maulidi kenan murnane da haihuwar Annabi SAW. Saisuce ah muma zamuyi, muma zamuyi inde abu na Son Annabi ne SAW baza abarmuba.

     

    Haka nan yanzu in watan ta kama to babu yaro ba babba kowa yana nuna farin cikin sa da zuwan Annabi Muhammadu SAW duk albarkar samun Shehu Ibrahim RTA, Masha’ Allah

     

    Allah ya sakawa Shehu Ibrahim Niasse RTA da Alhairi, Allah karawa Shehu lafiya Albarkar Manzon Allah SAW, Allah Kara mana soyayya A’min A’min

    Share
  • Yadda Aka Gudanar Da Gagarumin Mauludin Annabi SAW A Birnin Gombe.

    AN GUDANAR DA GAGARUMIN TARON BIKIN MAULUDIN MANZON ALLAH SAW A GOMBE

     

    Daga: Babangida A. Maina

     

    An gudanar da gagarumin bikin Mauludin Annabi Muhammadu SAW a gidan Alh Ibrahim Sufi dake anguwan Danaje cikin birnin Gombe.

    Taron Mauludin wanda aka saba gabatar duk shekara inda manyan baki daga sassa daban-daban na fadin Najeriya suke gabatar da kasidu da lakcoci akan tarihi na Manzon Allah SAW da halayen sada dabi’un sa.

    An gabatar da takarda mai taken koyi da kyawawan dabiu na Manzon Allah SAW wanda Sheikh Nuhu Abdulwadud ya gabatar da wasu daga cikin mahalarta taro.

    Hon Muhammadu Magaji Gettado kwamishina wanda ya wakilci gwamnan jihar Gombe Alh Muhammad Inuwa ya bayyana halaye na bayin Allah waliyai a matsayin abun koyi tare da godiya daga gwamnan jihar Gombe.

    Hon, kwamishinan matasa na jihar Gombe yayi kira ga dukkan matasa da suyi koyi da kyawawan halayen da dabi’u irin na Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ a kowanne hali na rayuwar su. Inda ya godewa duk wanda ya samu halartan taro Mauludin Manzon Allah SAW.

    Daga karshe Sallaman Gombe ya bayyana sakon mai martaba sarkin Gombe a taron Mauludin, an gabatar da jawabai mabanbanta daga wurin malamai da zikirin da yabon fiyayyen halitta Manzon Allah SAW.

     

    Sheikh Ibrahim Sufi wanda shine mai masaukin baki ya bayyana godiya ga Allah da masoya Manzon Allah SAW bisa halartan taro Mauludin Allah ya maimaita mana.

    Allah ya Maimaita Mana Ya Kara Mana Soyayyan Annabi Muhammadu ﷺ Ya Sakawa Wadannan Bayin Allah Da Alkhairi. Amiin

    Share
  • Kalaman Gwamnan Borno A Wurin Maulidi Manzon Allah SAW A Zawiyyan Sheikh Ibrahim Sale Maiduguri.

    MAULUD DAGA MAIDUGURI

     

    Zaman Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ Wanda Aka Gudanar A Zawiyyan Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini (Shugaban Masu Fatwa A Najeriya) Dake Birnin Maiduguri Jihar Borno.

     

    Gwamnan Jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum Tare Da Tawagar Sa Sun Samu Halartan Mauludin Da Kuma Dubban Jama’a Masoya Daga Sassan Duniya.

     

    A Cikin Jawabin Prof, Babagana Umara Zulum Gwamnan Jihar Borno Ya Bayyana Cewa Ya Zama Wajibi Duk Wani Musulmi Mai Kishin Addinin Sa Da Kuma Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ Yaso Annabi SAW.

     

    Ya Kara Cewa Soyayyan MANZON ALLAH SAW Wajibi Ne, Kuma Yana Kira Ga Daukacin Al’ummar Musulmi Na Kowanne Bangare Mu Dage Da Addu’o’i Zaman Lafiya A Ko’ina A Fadin Najeriya Musamma Jihar Borno.

     

    ALLAH Ya Maimaita Mana Ya Kara Mana Soyayyan Annabi Muhammadu SAW. Amiin

     

    Babangida A Maina

    Share
Back to top button