nasih

 • Allah Ya La’anci Duk Mai Cewa Iyayen Annabi Salla Lahu Alaihi Wa Sallam ‘Yan Wuta Ne.

  Allah Ya La’anci Duk Mai Cewa Iyayen Annabi Salla Lahu Alaihi Wa Sallam ‘Yan Wuta Ne

   

  Daga: Alkali Abubakar Ibnul Arabi

   

  An tambayi Alkali Abubakar Ibnul Arabi daya daga cikin malaman mazhaban Malikiyya akan mutumin da yace iyayen Annabi Salla Lahu Alaihi Wasalam na cikin wuta, sai ya amsa da cewa duk wanda ya fadi haka la’ananne ne, domin Allah yana fada a cikin Suratul Ahzab aya na 57 :

   

  (إن الذين يؤذون الله ورسوله لعنهم الله في الدنيا والآخرة وأعد لهم عذابا مهينا) (الأحزاب 57).

   

  Ma’ana :

   

  ” Lallai wandanda suke cutar da Allah da manzonsa Allah ya la’ance su Duniya da Lahira kuma ya tanada musu azaba na wulakanci “.

   

  Babu wani cutarwa fiye da cewa iyayen Annabi Salla Lahu Alaihi Wasallam ‘yan wuta ne.

   

  An ruwaito Daga Abu Huraira ya ce wata rana Sabee’atu ‘yar Abu Lahabi ta zo wurin Annabi (saw) ta ce, ya manzon Allah Mutane na kirana da diyar kiraren wuta, sai Annabi Salla Lahu Alaihi Wasallam, ya tashi tsaye cikin fushi yana cewa :

   

  (ما بال أقوام يؤذونني في قرابتي ومن آذاني فقد آذى الله).

  Ma’ana :

   

  ” Me yasa mutane suke cutar da ni cikin cutar da dangina, kuma duk wanda ya cuce ni lallai ya cuci Allah “.

   

  Allah ka kiyaye mu ka kara muna son Annabi da iyayensa Amiin.

  Share
Back to top button