HUDBAR ANNABI S.A.W A KAN WATAN AZUMI
DAGA TASKAR UMAR CHOBBE
Ya Ku Mutane! Hakika watan Allah (Watan Ramalana) yazo muku da albarka da rahama da kuma gafararsa. Wata ne wanda a gurin Allah shine watan da yafi kowane wata, kuma ranakunsa su ne mafiya kyawun ranaku, haka nan dararensa su ne mafiya kyawun darare, kana kuma ranakunsa su ne mafiya kyawun ranaku, sannan kuma awoyinsa su ne mafiya kyawun awowi.
Shi wata ne da ake kiranku zuwa ga bakuntan Ubangiji. A wannan wata an zabe ku ku zamanto masu samun falalar Ubangiji. Numfashinku a cikinsa ibada tasbihi ne. Kuma barcinku a cikinsa ibada ce. Kuma ayyukanku a cikinsa karbabbu ne. Haka nan kuma addu’oinku a cikinsa abin karba ne. Don haka ku roki Allah Ubangijinku na kyakykyawan niyya da kuma tsarkakakkiyar zuciya da Ya ba ku daman azumtarsa da kuma karanta littafinSa. Hakika shakiyyi shi ne wanda aka haramta masa gafarar Ubangiji a cikin wannan wata.
Lalle yayin azuminku ku tuna da yunwa da kishirwar Ranar Tashin Kiyama ta hanyar yunwa da kishiruwan da kuke ji a cikin wannan wata. Ku taimaki fakirai da masakan cikinku. Ku girmama manyanku, kuma ku ji tausayin na kasa da ku, ku sada zumunci a tsakaninku, ku kiyaye harsunanku da kuma ganinku daga abubuwan da basa halalta ku gansu da jinku. Ku ji tausayin marayu don kuma a ji tausayin ‘ya’yayenku a lokacin da suka zama marayu. Ku tuba wa Allah daga zunubanku, ku daga hannayenku sama don rokon Ubangiji a lokutan sallolinku, don wannan (lokacin) shi ne mafi cancantan lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya ke duban bayinSa da rahama, Ya amsa musu idan sun kira Shi, kuma Ya biya musu bukatansu idan sun nema.
Ya Ku Mutane! Kun daure hankulanku da soyace-soyacen zukatanku, don haka ku ‘yantar da su ta hanyar neman gafara. Kun daura wa bayanku abubuwa masu nauyi, don haka ku sauke wannan nauyi ta hanyar tsawaita sujadanku, ku fa san cewa Allah Madaukakin Sarki Ya rantse da daukakansa cewa ba zai azabtar da masu sallah da sujada ba, kuma barai sanya su cikin wuta ba a ranar tashin kiyama.
Ya Ku Mutane! Duk wanda ya shayar da wani mumini mai azumi a cikin wannan wata, to Allah Zai ba shi lada tamkar wanda ya ‘yanta wuyaye da kuma gafarta masa zunubansa da suka gabata. Sai Sahabbai suka ce: Ya ANNABI (S.A.W.) ba dukkanmu ne za mu iya hakan ba! Sai ya ce: Ku kiyaye kawukanku daga koda kuwa ta kwayan dabino ne, Ku kiyaye kawukanku daga wuta koda kuwa da bakin ruwa ne, don kuwa Allah Zai saka kan hakan ga wanda ba shi da wani abin da yafi hakan.
Ya Ku Mutane! Daga cikinku duk wanda ya kyautata dabi’unsa a cikin wannan wata, to yana da lamuni tsallake siradi a ranar da duga-dugai suke zamewa. Haka kuma duk wanda ya saukaka wa abin da hannunsa na dama ya mallaka (bayi) cikin wannan wata, to Allah zai saukaka masa hisabinsa. Duk wanda ya kare sharrinsa cikin wannan wata, to Allah Zai kiyaye shi daga fushinSa a ranar da za su sadu. Kuma duk wanda ya sada zumunci a cikin wannan wata, to Allah Zai isar masa da rahamarSa a ranar da zai sadu da Shi. Haka nan kuma duk wanda ya yanke zumunta a cikin wannan wata, to Allah Zai yanke masa rahamarSa a ranar da za su sadu. Kuma duk wanda ya yi nafilolin salla a cikin wannan wata, to Allah Zai rubuta masa barranta daga wuta. Haka kuma duk wanda ya yi wani aiki na wajibi (farilla) a cikin wannan wata, to Allah Zai ba shi ladan irinsa duba saba’in (70,000) da ya yi a wani watan na daban (wanda ba Ramalana ba). Kuma duk wanda ya yawaita yi min salati, to Allah Zai nauyaya mizaninsa (sikeli) a ranar da mizanai suke fadowa kasa (wato suke dawowa kasa saboda rashin nauyi). Duk kuwa wanda ya karanta wata aya ta Alkur’ani, to yana da ladan wanda ya karanta dukkan Alkur’ani a wani wata na daban.
Ya Ku Mutane! Hakika kofofin aljanna a bude suke a wannan wata, don haka ku roki Allah da Kada ya rufe su a kanku. Haka nan kuma kofofin wuta a rufe suke, don haka ku roki Allah da kada ya bude su a kanku. Kuma shaidanu a kame suke, don haka ku roki Allah da kada su sami galaba a kanku, Allah yasa Damu za’ayi Wannan Azumin Mai Albarka.
Allah ya karbi Ibadun mu gaba daya wanda zamuyi acikin watan mai Albarka
Allah ya gafartamana zunuban mu Gaba Daya Albarkan Annabi S.A.W. Amiin Yaa ALLAH
Daga: Sayyadi Umar Chobbe