NASIHA

 • DA GASKE NE KARANTA SALATIL FATIHI YAFI SAUƘAN ALƘUR’ANI DUBU SHIDA LADA ? 

  DA GASKE NE KARANTA SALATIL FATIHI YAFI SAUƘAN ALƘUR’ANI DUBU SHIDA LADA?

   

  Tambayar da ake min a kwanakin nan kenan, yin shiru ko kuma kau da kai daga wautar jahilai ba zai zamo mafita a garemu ba. Ga yadda abun yake.

   

  Da farko mu fara sanin cewa lallai ko mun yarda ko bamu yarda ba salatil fatihi salatin Annabi sallallahu alaihi wasallam ne ingantacce, domin babu ambaton wani shehi ko wata Ɗariƙa a ciki sai sunan Allah da Annabi sallallahu alaihi wasallam da kuma ahlinsa masu daraja.

   

  Akwai abun da ake cewa falala da daraja, zan bada misali domin sauƙin fahimtar menene falala da daraja.

   

  Kaine aka baka dala 100 ta amurka da kuma Alƙur’ani izu sitti aka ce ka zaɓi ɗaya a ciki, ina da tabbacin mafi yawan mutane dalar nan zasu ɗauka su ƙyale Alƙur’anin, saboda meye? Saboda da wannan dalar zaka iya fansar Alƙur’ani sama da 50. Idan kuma Alƙur’anin ka ɗauka da iya shi kaɗai zaka tsira. A nan ba wai an ɗaukaka dalar akan Alƙur’ani bane a ah sai dan dalar tafi Alƙur’anin falala, shi kuma Alƙur’ani babu wani littafi da ya kaishi daraja da ɗaukaka a wajen duk wani musulmin kirki.

   

  Wannan kenan, sannan a duk lokacin da ka karanta duk wani harafi na Alƙur’ani akwai adadin ladan da Allah yace zai baka, amma salatin Annabi sallallahu alaihi wasallam Allah ne da kansa yace zai maka salati shima. Ya girman ladan salatin da Allah zai yiwa bawansa yake? Bamu sani ba.

   

  Saboda haka muke ƙara nanatawa lallai yiwa Annabi sallallahu alaihi wasallam salati aiki ne da babu wanda ya isa ya faɗa maka menene sakamakonka sai Allah.

   

  Allah ya bamu dacewa Duniya da Lahira ya kuma ƙara mana ƙaunar Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam. Amin

   

  Mustapha Abubakar Kwaro

  12/09/2023

  Share
 • IMAMU AL-FAZAZEE (R.A) Yana Yabon Sahabbai a Gwala-Gwalan Baitotinsa Inda Yake Cewa.

  IMAMU AL-FAZAZEE(R.A) Yana Yabon Sahabbai a Gwala-Gwalan Baitotinsa Inda Yake Cewa:

   

  أولو البر والتقوي وأهل الفضائل

   

  “Su Sahabbai Ma’abota Alkhairi Ne Da Nagarta Da Tsoron ALLAH Da Falaloli Ne”,

   

  عصابة إشفاق وخير ونائل

   

  “Jama’a Ne Masu Tausayi Da Alfahari Da Baiwa Da Kyauta”,

   

  سمت بقبول الحق من خير قائل

   

  “Su Fa Sun Daukaka Ne Ta Hanyar Karbar Gaskiya Daga Mafi Alherin Masu Magana (S.A.W)”,

   

  أقرت لأيات له ودلائل

   

  “Sun Tsaya ‘Kyam Gare Shi Ne, Saboda Ayoyi Da Hujjojinsa Da Su Ka Tabbata”

   

  بها الصبح طلق والطريق موطأ

   

  “Garai-Garai Suke Kuma Hanyarsu (Hanyar) Bi Ce!”.

   

  ALLAH YA ‘KARA DADIN TSIRA DA YARDA GA SAHABBAN MANZON ALLAH(S.A.W) YA BAMU ALBARKARSU, AMEEEEN

  Share
 • HANYOYI GUDA ASHIRIN DA BIYAR (25) NA SAMUN SHIGA ALJANNAH!.

  HANYOYI GUDA ASHIRIN DA BIYAR (25) NA SAMUN SHIGA ALJANNAH!

   

  1. ANNABI (S.A.W) yace : ”Duk wanda ya hina ma Allah Masallaci, to Allah zai gina masa gida a cikin Aljannah. (Bukhari da kuma, Tirmidhi hadisi na 318)

   

  2. ANNABI (S.A.W) Yace : ”Wanda yayi Salloli biyu na sanyi (Sallar La’asar da Sallar Asuba) zai shiga Aljannah. ” (Bukhari)

   

  3. An karbo Hadisi daga Abu Hurairah (RA) yace : ANNABI (S.A.W) Yace : ”Duk wanda yace : ”SUBHANALLAHI WABIHAMDIHI, SUBHANALLAHIL-AZEEM.” Sau bakwai (7)

  za’a gina masa bene a cikin Aljannah.

  ”Al-wabilus Sayyib Shafi na 77.”

   

  4. Jabir, Allah ya yarda dashi, yace: ANNABI (S.A.W) Yace : ”Wanda yace ”SUBHANALLAHIL -AZEEM WA BIHAMDIHI. ” za’a dasa masa bishiyar Dabino a cikin Aljannah.”

   

  5. ANNABI (S.A.W) Yace : ”Duk Wanda Qarshen Maganarsa ta kasance ”LA’ILAHA ILLALLAH.” zai shiga Aljannah.” (Abu Dawud)

   

  6. ANNABI (S.A.W) Yace : ”Duk wanda Yace : ”Ya Allah Ina Rokonka, ka Shigar dani Aljannah sau ukku (3) (Allahumma Inniy As’alukal jannah) ALJANNAH ZA TA CE : ”Ya Allah ka shigar dashi Aljannah.” (Tirmiziy ne ya ruwaita shi)

   

  7. ANNABI (S.A.W) Yace : ”Ya ku Mutane ku watsa Sallama, kuma ku ciyarda da Abinci ga mai jin yunwa, kuma kuyi Sallah lokacin da Mutane ke bacci (da dare) sai ku shiga Aljannah da Aminci.” (Tirmiziy ne ya ruwaito shi)

   

  8. ANNABI (S.A.W) Yace : ”Lallai Allah yanada sunaye sasa’in da tara (99), Duk wanda yasan Ma’anar su kuma ya kiyayesu Zai shiga Aljannah (Bukhari)

   

  9. ANNABI (S.A.W) Yace : ”Wa zai Lamunce min Abinda ke tsakanin Habobinsa guda biyu da kuma Abinda ke tsakanin kafafunsa biyu (Wato : Harshen sa da kuma Farjinsa) In Lamunce masa Shiga Aljannah.”

  (Sahih Bukhari )

   

  10. An kar6o Hadisi daga Aisha (RAH) tace : ANNABI (S.A.W) Yace : ”Duk wanda ya ga wata kafa a cikin Sahu kuma ya toshe, Allah zai gina Masa gida a cikin Aljannah kuma zai daukaka darajarsa a cikin Aljanna.’

   

  Allah yasa mu dace. Amiin

  Share
 • Ruwan Da Ya ‘Bulbulo Daga Yatsan Hannun Manzon ALLAH(S.A.W) Yafi Zam-Zam, Alkausara Da Salsabila. Inji Sheikh Tijjani Zangon Bare-bari

  Shehu Tijjani Usman Na ‘Yan Mota (R.A) Yana Cewa

   

  “Ruwan Da Ya ‘Bulbulo Daga Yatsan Hannun Manzon ALLAH(S.A.W) Yafi Kowane Qorama Ta Duniya Da Lahira.

   

  Yafi Zam-Zam, Yafi Alkhausara, Yafi Salsabeela Da Sauransu”.

   

  SALLALLAHU ALAIKA WA SALLAAM!

   

  Kai Jama’a Sahabban MA’AIKI(S.A.W) Sun More Wallahi:

   

  Sun Gan Shi(S.A.W)

  Sun Yi Hira Da Shi(S.A.W)

  Sunyi Masa Mubaya’a(S.A.W)

  Sun Sha Ruwa Daga Yatsunsa(S.A.W)

  Sunyi Alwala Da Shi,

  Wasu Ma Sun Shayar Da Dabbobinsu Da Shi.

   

  YA SALAAM

   

  Ya ALLAH! Ka Yarda Ma’aikin ALLAH(S.A.W) Ya Shayar Da Mu Ruwa Daga Wannan Tafkin Da Yake Kwararowa Daga ‘Yan Yatsunsa Masu Albarka, Ameen.

  Share
 • Wata Rana Abdullahi Bn Salam(‘Daya Daga Cikin Yahudawan Madina) Ya Zo Wajen MA’AIKI (S.A.W) Ya Ce Da Shi:

  Wata Rana Abdullahi Bn Salam(‘Daya Daga Cikin Yahudawan Madina) Ya Zo Wajen MA’AIKI(S.A.W) Ya Ce Da Shi:”Na Zo Ne Domin Na Yi Maka Wasu Tambayoyi Guda Uku(3) Wadanda Babu Wanda Ya San Amsarsu Idan Shi Ba Annabi Bane:

   

  1. Shin Menene Farkon Sharadin Tashin Al-Qiyama???

  2. Shin Menene Farkon Abincin Da ‘Yan Aljannah Zasu Ci???

  3. Shin Menene Yasa Wani Lokaci Idan Aka Haifi Yaro Ya Kan Yi Kama Da Ubanshi, Wani Lokacin Kuma Uwarshi???

   

  Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce Da Shi:”Yanzun Nan Mala’ika Jibrilu(A.S) Ya Zo Ya Bani Labarin Amsoshin Tambayoyin Nan Naka”.

   

  Sai Bn Salaam Ya Ce:”Mala’ika Jibrilu???”

   

  ANNABI(S.A.W) Ya Ce:”Eh”

   

  Bn Salam Ya Ce:”Ai Mala’ika Jibrilu Shi Ne Makiyin Yahudawa”.

   

  Sai ANNABI(S.A.W) Ya Karanto Masa Wannan Ayar Da Take Cewa:”Man Kana Aduwan Lillahi Wa Mala’ikatihi Wa Jibrila Wa Minkaila Fa’inallaha Aduwan Lilkafiriin”.

   

  Sannan Ya Bashi Amsoshin Tambayoyin sa Kamar Haka:

   

  1. Farkon Sharadin Tashin Qiyama Wata Wuta Ce Wacce Zata Koro Mutane Tun Daga Inda Rana Take ‘Bullowa Har Zuwa Inda Take Fad’uwa

  2. Farkon Abincin Da ‘Yan Aljannah Zasu Ci Shi Ne Hantar Wani Kifi,

  3. Idan Maniyyin Namiji Ya Riga Na Mace Sauka, To Sai Yaron Ya Zama Yana Kama Da Shi(Uban), Idan Kuma Na Macen Ne Ya Riga Sauka, To Sai Yaron Yayi Kama Da Ita(Uwar).

   

  Daga Wannan Lokacin Sai Abdullahi Bn Salam Wanda Ada Shi Ne Mafi Alkhairin Yahudawa Kuma ‘Dan Shugaban Yahudawan Ya Ce:”Na Shaida Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH, Kuma Haqiqa Kai MANZON ALLAH Ne,

   

  Ya RASULALLAHI! Haqiqa Yahudawa Mutane Ne Masu ‘Kage Da Sharri Ne, Idan Suka San Cewa; Na Musulunta Tun Kafin Ka Tambaye Su Game Da Ni, To Tabbas Zasu Yi Min Sharri Da ‘Kage”,

   

  Da Sauran Yahudawan Suka Zo Sai MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Tambaye Su Cewa:”Shin Menene Matsayin Abdullahi Bn Salaam a Cikinku???”

   

  Sai Suka Ce:”Shi Ne Mafi Alkhairin Cikinmu, Kuma ‘Dan Gidan Mafi Alkhairin Cikinmu, Kuma Shi ‘Dan Shugabanmu Ne”,

   

  ANNABI(S.A.W) Ya Ce:”Shin Yaya Kuke Gani Idan Shi Ya Musulunta???”

   

  Sai Suka Ce:”ALLAH Ya Tsare Shi Ba Zai Ta6a Musulunta Ba”.

   

  Jin Hakan Ke Da Wuya Sai Abdullahi Bn Salaam(R.A) Ya Fito Daga Inda Yake ‘Boye Ya Ce:”Ash-Hadu An La’Ilaha Illallahu Wa Anna Muhammadur Rasulullahi”.

   

  Daga Jin Hakan Sai Yahudawan Suka Ce:”Ai Wannan Shi Ne Mafi Sharrin Cikinmu Kuma ‘Dan Gidan Mafi Sharrin Cikinmu”.

   

  Sai Bn Salaam(R.A) Ya Ce:”Ya RASULULLAHI! Ka Ga Abin Da Nake Tsoro Kenan Tun Farko; Sharrin Bakinsu”.

   

  Sayyiduna Abdullahi Bn Salam(R.A) Ya Musulunta Kuma Musulunci Yayi Armashi Sosai Harma Ya Kasance ‘Daya Daga Cikin Malaman Sahabban ANNABI (S.A.W).

   

  Ya ALLAH! Ka Yi Dadin Tsira, Sallama Da Salati Ga Mijin Khadija Angon A’isha, Abul Qaseem Abban Fatima, Wanda Ka Aiko Shi Domin Ya Kasance Rahama Ga Dukkan Talikai.

   

  ALLAH YA ‘KARA MANA SOYAYYAR SHI(S.A.W) AMEEEEEN.

  Share
Back to top button