RADDI

 • BIDIYO: ZAFFAFAN RADDI GA BASALAFE DR, BIRNIN KUDU DAGA KHALIFA MADATAI

  ZAMANI YA FICE DA IRIN WANNAN YAKAR TUNANIN ZAI SAKE YIN TASIRI YAKAI Dr. B/KUDU

   

   

  Babu wata Al’umma da zata tsira daga tawaya, muddin gurbatattun cikinta ko jahilan cikinta ko kuma raunanan cikinta sune zasu zamo ababen kafa hujja akanta daga barin kafa hujja akan ayyukan nagartattun cikinta, da kuma gaskiyar abinda yazo cikin koyarwarta da aka nakalta daga Malamai ma’abota ilmi da fahimta, ba Malaman Bariki yan neman Followers ba

   

  Cewa “Abinda Yan Hakika sukeyi, na Allantar da bayi, tare da yaki da iyakokin ALLAH shine gaskiyar koyarwar Tijjaniyya” wannan zance nuni yake da tsantsar son zuciya, da kuma abin kunya ga mutum irinka wanda ke tutiya da lakabin “Dr.”.

   

  A matsayinka na Malami, idan zakayi zance akan hanyar wasu al’umma, littafin Malamanta zaka dauko, kace abu kaza da mabiyanta suke aikatawa ga inda suka koya, ba haka kawai zaka yiwa mutane hawan kawara ba.

   

  SABODA HAKA, YA DAI KAMATA A WAYE, A NEMI ABIN YI DAGA BARIN AIBATA MUTANE BA BISA HUJJA BA.

   

  ALLAH Ya Shirye Mu. Amiiiin Yaa Allah

   

  Daga: Muhaammadu Usman Gashua

  Share
Back to top button