RASUWA

  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Allah Ya Yiwa Malamin Tijjaniyya Rasuwa A Garin Gombe.

    INNA’LILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN

     

    Allah Ya Karbi Rayuwar Daya Daga Cikin Manyan Shehunan Darikar Tijjaniyya A Nigeria.

     

    ….Allah Ya Yiwa Sheikh Muhammadu Kubuwa (Khalifan Shehu Manzo Gombe) Rasuwa.

     

    A Madadin Kungiyar Fityanul Islam Initiative Reshen Jihar Gombe Karkashin Jagoranci Malam Yauta Bappah Shanu Na Mika Sakon Ta’azziyya Ga Daukacin Al’ummar Musulmai Musamman Iyalan Da Yan’uwa.

     

    Allah Ya Jikan Sa Da Rahma Ya Gafarta Masa Ya Sadashi Da Manzon Rahma SAW. Amiin

     

    Babangida Alhaji Maina

    Tijjaniya Media News

    Share
  • Yanda Aka Gudanar Da Sallar Jana’izan Tsohon Gwamnan Jihar Yobe A Haramin Makkah.

    HOTUNAN JANA’IZA:

     

    Yadda Aka Gudanar Da Jana’izan Tsohon Gwamnan Jihar Yobe Sanata Bukar Abba Ibrahim Bayan Sallar Asuba A Masallacin Harami Dake Garin Makkah, A Kasar Saudi Arabia.

     

    Marigayi H.E Senator Bukar Abba Ibrahim, Shine Ya Gina Babban Masallacin Juma’a Dake Garin Damaturu A Jihar Yobe Wanda Yake Daukan Dubban Jama’a.

     

    Allah Ya Jikan Sa Da Rahma Ya Gafarta Masa, Allah Ya Sadashi Da Rahmar Sa. Amiin

    Share
  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Yiwa Tsohon Gwamna A Najeriya Rasuwa.

    Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un

     

    Allah Ya Yiwa Tsohon Gwamna A Najeriya Rasuwa.

     

    Allah Ya Yiwa Tsohon Gwamnan Jihar Yobe His Excellency Senator Bukar Abba Ibrahim (Wali of Gujba) Rasuwa Yau Lahadi 4/02/2023 A Saudiyya.

     

    Bayan Wata Doguwar Rashin Lafiya Da Ya Yi fama Da ita, sannan kuma za a binne shi a can.

     

    Allah Ya Jikan Sa Da Rahma Ya Gafarta Masa Tare Da Sauran Magabatan Mu. Amiin Yaa ALLAH

    Share
  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Yiwa Daya Daga Cikin Ya’yan Sheikh Tijjani Zangon Bare Bari Kano Rasuwa.

    INNA’LILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN

     

    Allah Yayiwa Sayyida Maimuna Yar Maulanmu Sheikh Mal. Tijjani Usman Z/Bare-bari Kano Rasuwa.

     

    Za’a Gudanar Da Sallar Janazar Ta Kamar Haka:

     

    – Lokaci: Karfe 2:30 Na Rana

    – Wuri: A Zawiyyar Maulanmu Sheikh Malam Tijjani Usman Zangon Bare bari Kano.

     

    Allah Ya’ jikan ta Da Rahma Ya Gafarta Mata. Amiin Yaa ALLAH

    Share
  • Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un; Allah Ya Yiwa Kakar Young Sheikh Sayyada Hajiya Fatima Rasuwa.

    INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJJI’UN

     

    ….Allah Ya Yiwa Kakar Young Sheikh Sayyada Hajiya Fatima Rasuwa.

     

    Mahaifiyar Babban Yayan Mu Barr. Musa Aliyu Mai Yasin National Legal Advicer 𝐅𝐢𝐭𝐲𝐚𝐧𝐮𝐥 𝐈𝐬𝐥𝐚𝐦 𝐎𝐟 𝐍𝐢𝐠𝐞𝐫𝐢𝐚 Kuma Kaka Ga Young Sheikh Zaria Zakeer M.S Ali

     

    An gudanar da sallar Janai’za ranar Yau Laraba Da karfe 11:00am Na Safe. A Zawiyyar Sheikh Aliyu Maiyasin Kake Sabon Layi Tudun Wada, Zaria jihar Kaduna.

     

    Muna Rokon Allah Jajaddada Rahama Gareta Yasa Aljannace Makomarta. Amiiiin

    Share
Back to top button