RAYUWA

  • Sakon Professor Ibrahim Maqary Zuwa Ga ‘Yan Mining.

    Mining yana cikin aiyukan Wasa’il, ba Maƙasid ba.

     

    Zai iya zama Halal ko Haram gwargwadon abubuwan da ke tattare dashi, da abinda zai kai zuwa gareshi.

     

    Koda yake ya saɓa da hanyoyin, da Musulunci ya tsara na neman kudi, amma ba za a, iya cewa Haramun bane yanke.

     

    Sai dai, ina baiwa Matasa shawara, su shagalta da nagartattun hanyoyi masu amfani, cikin ginin Addini da Rayuwa wajen neman kudinsu.

     

    ….Cewar Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary

  • A Rana Mai Kamar Ta Yau 7 Ga Watan Mayu 2018 Allah Ya Karbi Rayuwar Shiekh Isyaka Rabi’u.

    SHEKARU 6 DA RASUWAR HALIFA ISAYAKA RABIU.

     

    A Rana Mai Kamar Ta Yau 7 Ga Watan Mayu 2018 Allah Ya Karbi Rayuwar Shiekh Isyaka Rabi’u.

     

    Yadda rayuwar marigayi Khalifa Isyaka Rabi’u ta kasance.

     

    Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi’u malamin addinin musulunci ne, kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya dade yana ayyukan taimakawa al’umma a lokacin rayuwarsa.

     

    An haifi marigayi Isyaku Rabi’u a 1925 ga iyalan Muhammadu Rabi’u Dan Tinki, wanda mai wa’azin addinin musulunci ne daga Bichi cikin jihar Kano a Najeriya.

     

    Daga 1936 zuwa 1942, marigayin ya halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur’ani da Larabci.

     

    Daga nan ya tafi Maiduguri domin karo ilimi, kuma bayan ya gama karatunsa a can ne ya dawo gida da niyyar yin aure.

     

    Bayan ya yi auren kuma ya tafi Zariya gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na’iya, inda ya samu shekaru biyu yana dalibta.

     

    A shekarar 1949 ya kasance malamin addini mai zaman kansa, inda yake koyar da Larabci da Alkur’ani ga dalibansa. Kuma a cikin daliban akwai Ibrahim Musa Gashash.

     

    A farko shekarun 1950 Mallam Isyaku Rabi’u ya fara kasuwanci, duk da cewa bai bar koyarwa ba. Ya kafa wani kamfani mai suna Isyaku Rabiu & Sons a 1952.

     

    Da farko kamfanin ya fara da zama dilan kayan kamfanin UAC ne, wanda a wancan lokacin ke kasuwanci akan kekunan dinki, da litattafan addinin Musulunci da kuma kekuna.

     

    A 1958, kamfanin ya sami bunkasa bayan da aka kafa masakar Kaduna Textile Limited kuma kamfanin na Isyaku Rabiu & Sons ya zama daya daga cikin dilolinsa na farko.

     

    Marigayin ya zama babban dilan kamfanin a arewacin Najeriya, kuma a 1963 shi da wasu ‘yan kasuwa daga Kano suka hadu don kafa Kano Merchants Trading Company.

     

    Wannan kamfanin ya jure wa gasa daga kamfanonin da ke shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Ya kuma kafa wani kamfani mai dinka kayan sawa a 1970.

     

    A lokacin da aka fara siyasar janmuriya ta biyu, marigayi Sheikh Isyaku Rabi’u ya goyi bayan jam’iyyar NPN wadda ta mulki kasar.

     

    Kasuwanci.

     

    Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.

     

    A shekarun 1970, kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.

     

    A 1972 ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saka zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.

     

    Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci A kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.

     

    Amma saboda faduwar darajar Naira, kamfanin ya mayar da hankalinsa wajen kere-kere da kasuwanci kaya.

     

    Marigayi Isyaku Rabi’u ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya har da jikoki masu yawa, kuma a cikin ‘ya’yansa akwai Nafiu Rabiu, wanda shi ne babban dansa. Akwai kuma babban dan kasuwan nan, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA.

     

    Akwai kuma Rabi’u Rabi’u, mai kamfanin jirgin sama na IRS Airlines, da Naziru Rabi’u, da Quraish I Rabi’u, da Makiu Rabi’u, sai Abdullahi Rabi’u, da Muhammad Rabi’u, da Daha Rabi’u.

     

    Kuma a fili yake cewa gidan marigayin na cikin gidaje mafi girma a duk fadin Kano.

     

    Ayyukan taimako

     

    Ban da fagen karatun addini da kaswanci, marigayi Sheikh Isyaku Rabi’u ya yi fice wajen ayyukan taimako, wanda ya sa mutane da dama ke kaunarsa.

     

    Malam Isyaka Rabi’u sanannen dan darikar Tijjaniya ne, kuma yana daya daga cikin manyan almajiran shiek Ibrahim Nyass Kaulaha.

     

    Bayani kan darikar Tijjaniya.

     

    An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784

    Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta

    Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin Afirka

    Tana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya.

     

    Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girma.

     

    Sun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:

     

    Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita Allah.

     

    Ana alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta dama.

     

    An haife shi a kasar Senegal kuma jama’a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsa.

     

    Darikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Najeriya inda suke da mabiya sosai.

     

    YA ALLAH YA JIKAN SHEIKH ISYAKU RABI’U DA RAHAMA AMIIIIN YAA ALLAH

  • GAMSASSUN HUJJOJI NA HADISI MASU NUNA CEWA IYAYEN ANNABI (SAW) ‘YAN ALJANNA NE.

    DALILAI NA HADISI MASU NUNA CEWA IYAYEN ANNABI (SAW) ‘YAN ALJANNA NE.

     

    Sheikh Halliru Abdullahi Maraya Kaduna.

     

    Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da Ya ba mu dama , a jiya , muka gabatar da wasu daga cikin dalilai na hankali masu nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ba ‘yan wuta ba ne . Allah (SWT) Ya kara masu (AS) rahama da yarda. Insha’Allah, yau, zamu kawo wasu dalilai na Hadisin Manzon Allah (SAW) masu nuna haka Allah (SWT) Ya kara wa ManzonSa (SAW) matsayi da alfarma. Akwai dalilai na Hadisin Manzon Allah (SAW) da suke nuna cewa iyayensa (AS) muminai ne , ‘yan Aljanna . Daga ciki akwai:

     

    i. Waathilah Ibnu Asqa’i (RA) yace: Manzon Allah (SAW) ya ce “Lallai Allah Ya zabi Ismaa’iil (AS) daga cikin ‘ya’yan Ibraahiim (AS) kuma Ya zabi ‘ya’yan Kinaanah daga cikin ‘ya’yan Isma’iil (AS), kuma Ya zabi Quraysh daga cikin ‘ya’yan Kinaanah , kuma Ya zabi ‘ya’yan Haashim daga cikin Quraysh , sannan (daga karshe) Ya zabe ni daga cikin ‘ya’yan Haashim .”Manazarta : Sahiihu Muslim .

     

    ABUN DA HADISIN KE NUNAWA:

     

    Wannan Hadisi yana nuna cewa acikin kowace Jama’a , tun daga Annabi Ibraahiim (AS) har zuwa lokacin haihuwar Manzon Allah (SAW) , Allah (SWT) Yana zaben mutane ne mafifita a wurinSa (SWT), sannan Ya sa Manzon Allah (SAW) a tsatsonsu. A takaice, mai lafiyayyen hankali zai fahimta daga wannan Hadisi cewa iyayen Manzon Allah (SAW), tun daga Annabi Ibraahiim (AS) zuwa iyayensa na haihuwa, zababbu ne a wurin Allah (SWT). Kafirai kuwa ba zababbu ba ne a wurin Allah (SWT) . Saboda haka, Hadisin ya nuna cewa Abdul-Laahi (AS) da Aaminatu (AS) , iyayen Manzon Allah (SAW) , zababbu ne a wurin Allah (SWT) ba ‘yan wuta ba.

     

    ii. Sayyidunaa ‘Aliyyu (RA) ya ce : Manzon Allah (SAW) ya ce : ” An haife ni ne ta hanyar aure , ba a fitar da ni ba ta tsatson mazinaci tun daga Aadam (AS) har zuwa lokacin da mahaifina da mahaifiyata suka haife ni .”Manazarta : Imam At- Tabaraaniyyu , Mu’jamul-awsad.

     

    ABUNDA HADISIN KE NUNAWA:

     

    Wannan Hadisi na nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) , Abdul-Laahi da Aaminatu (AS) , ko zina basu taba yi ba , balle kafirci.

     

    Manzon Allah (SAW) na alfahari da cewa iyayensa (AS) ko zina basu taba yi ba . Wato cikakkun mutane ne na kwarai. Mu sani , kafirci shi ne sabon Allah (SWT) mafi muni da girma. Iyayensa (AS) ba kafirai ba ne , da kafirai ne , da bai yi alfahari da cewa ko zina basu taba yi ba.

     

    Domin da kafirai ne , da kenan sun aikata laifin da ya fi zina girma sosai . Saboda haka , da bai yi alfahari ba da rashin yin zinarsu. Misali: Mutum ne iyayensa ba sa shan taba , amma suna shan koken (Cocaine) , dan Allah zai iya alfahari saboda cewa iyayensa ba sa shan taba ? A nan zan tsaya yau. In sha’Allah, gobe ko jibi , zan yi magana a game da ainihin mahaifin Annabi Ibraahiim (AS) , wato daya daga cikin kakannin Manzon Allah (SAW) . In sha’Allah , zamu ji waye hakikanin mahaifinsa.

     

    Daga baya kuma , in sha’Allah , sai mu je kotun koli , wato Alqur’ani Mai girma , a game da cewa iyayen Manzon Allah (SAW) ba yan wuta ba ne kamar yadda wasu ke tallatawa . Allah Ya kiyaye ! In sha’Allah , daga karshe , sai mu rufe da yin magana a game da hujjojin da masu wannan mummunar maganar suke amfani da su domin a yarda da wannan magana tasu mai munin gaske . Allah (SWT) Ya kara wa Manzon Allah (SAW) , alayensa (AS) , da

    sahabbansa (RA) matsayi da yarda. Mu kuma , Allah (SWT) Ya kara mana soyayyarsu.

     

    Allah Ya kara wa kasarmu, Nijeriya , arziki da zaman lafiya. Duk wadannan, Allah Ya amsa mana saboda alfarmar Manzon Allah (SAW). Amiiiin Yaa ALLAH

  • FALALA DA SIRRUKAN DA AKE SAMU A CIKIN DAREN NISFU SHA’ABAN

    FALALA DA SIRRUKAN DA AKE SAMU ACIKIN DAREN NISFU SHAABAN

     

    Ita Daren Nisfu Shaaban Dare ce Mai Daraja, Wanda Acikinta ne Allah yake Bononza Na Rahama da Alhairai na Shekara Gaba Daya

     

    Tana Kasancewa ne Ranar 14 ga Wannan Watan Na Sha’aban Da Daddare, (Wato Daren 15 ga Wata)

     

    Anaso Ka Raya Daren Da Ibadu >> Insha Allahu A Post Na Gaba Zamu Kawo Nafilar Da Akeyi Acikin Wannan Daren

     

    Anaso Ka Wayi Gari Da Azumin Bayan Kayi Wancan Nafilar, Allah Zai Sada ka Da Dukkan Alhairan da ake Rabawa

     

    Qissa Mai DaDi Game Da Wannan Dare Da Aka Bamu Mu Alummar Annabi Muhammadu SAW

     

    Wata Rana Annabi Isah Yaga Wani Dutse Yana Haske, Sai Yayi Mamaki, Sai Allah Yace Masa: Kanaso In nuna maka abinda Yafi Wannan Mamaki??

     

    Sai Yace Inaso Ya Ubangiji Sai Allah Ya Umurceshi da ya shiga cikin dutsen, Yana Shiga Sai Yaga Wani Mutum Yana Bautama Allah Aciki Shekaranshi Dari hudu Yana Ibada Bai Taba Fita Ba!

     

    Sai Yace : Ya Ubangiji : Anya Ka Halicci Wani Mutum Da Yayi Maka Bauta Irin Na Wannan Mutumin Kuwa?

     

    Sai Allah Yace: Akwai Wata Dare Wacce Na Baiwa Al umman Masoyina ANNABI MUhammadu S.A.W (Daren Nisfu Shaaban)

     

    A cikinta Duk Wanda Yayi Nafila Raka’a biyu, Zan Bashi Ladan Ibadan Wannan Bawan Allah Da Ya Sami Shekara Dari hudu Yana Bautamin. Allahu Akbar.

    Allah Ka Bamu Ikon Raya Wannan Dare Don Arzikin Annabi Muhammadu SAW. Amiiiin Yaa ALLAH

  • WADANDA KE TUNAWA DA MUTUWA DA TSAYUWAR HISABI A KOWANNE LOKACI.

    WADANDA KE TUNAWA DA MUTUWA DA TSAYUWAR HISABI A KOWANNE LOKACI.

     

    1- Basu gina dogon buri akan Duniya.

     

    2- Kullum suna cikin neman gafarar ALLAH da yardarsa cikin ayyuka.

     

    3- Suna iya kokarinsu wajen nesantar ha’inta ko cutar da kowaye.

     

    4- Suna kokari tukuru wajen yin ayyukan da zasu amfani lokacinsu da al’umma.

     

    5- Basu hassada ko kyashi cikin wata falala da ALLAH ya huwacewa wani.

     

    6- Suna saurin uzuri da yafiya ga wadanda suka saba musu.

     

    7- Basu neman girma wajen kowa balle tauyewa ya dame su.

     

    8- Suna iya kokarinsu wajen kiyaye neman halal ta hanyar nesantar haramun.

     

    9- Suna takatsa-tsan cikin ababen da suke furtawa saboda hisabin dake gabansu.

     

    10- Ba su girman kai, alfahari, takama, rena halitta ko kuma daukar kawunansu madaukaka akan wasu.

     

    ALLAH KA BAMU IKO MUYI KOYI DA HALAYENSU, KA YAYE MANA GAZAWARMU ALBARKAN ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA

Back to top button