RAYUWA

  • Farfesa Ibrahim Maqari RA, Ya Fayyace Gaskiya Akan Al’amuran Rayuwa.

    YADDA BATUN YAKE (A FAHIMTATA).

     

    Dukkanin ANNABAWAN ALLAH sun kasance da wata sana’a da suka dogara da ita, wasu noma, wasu kira, wasu kiwo, wasu su wasu fatauci da sauransu baya ga aikin da aka aiko su da shi.

     

    Hakanan dukkanin halifofinsu nagartattu (Daga Malamai) basu kasance cima zaune ba, kowanne guda cikinsu ya tsaya da kafafunsa wajen yin kasuwanci domin samun abin dogaro, misali Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) da shuhurarsa ta fannin noma da kiwo a matsayin sana’arsa abar riko.

     

    Idan kayi duba zuwa zaben da ya gabata kadai zaka fahimci lallai a yau dayawa daga masu wadannan siffofi da aka ambata (Malamai) sun kasance ababen tausayi, domin kowanne guda cikinsu kokari yake yaga ya tallata wani dan Siyasa da siffofin da shi kansa yasan bai da yakini akan ingancinsu, a takaice dai kakar zabe ga dimbin Maluma ya zamo lokacin hada-hadar neman abin Duniya, a yayin da wasu kuma ke siffatuwa da wannan siffa domin damfara, zamba tare da cuwa-cuwa tsakanin bayin ALLAH, ayayin da wasu kuma dake da wannan siffa ke bin ofisoshin manyan Jami’ai suna Maula da sunan Addini.

     

    MUHALLI SHAHID.

     

    Idan ana sanya rawani, rike kwagiri tare da tasbaha domin siffatuwa da siffa ta kamala, amma a gaza nesantar cin harumun din da zai munanta haduwar bawa da ALLAH, to yafi alkairi mutum ya dauki fartanya yaje yayi noma, ko Gatari yake yayi faskare, ko kuma Baro yaje yayi dako dan ya samu halalinsa, da mai yiwuwa hakan ya kyautata haduwarsa da ALLAH ya zamo abin soyuwarsa (Waliyi).

     

    A TAKAICE DAI, ANA IYA SAMUN KUSANCI DA ALLAH, TA HANYAR NEMAN SANA’A KOMAI KANKANTARTA DA WAHALARTA TA HANYAR NEMAN HALALI, KUMA ANA IYA NESANTA DA ALLAH KO DA AN SIFFATTU DA SIFFA TA KAMALA AMMA IDAN YA ZAMO ANA CIN HARAMUN.

     

    WALLAHU -A’ALAM.

     

    NOTE: Wannan kawai fahimtace, mai yiwuwa sam shi ma’abocin rubutun ba haka yake nufi ba.

     

    ALLAH YASA MU DACE. AMIIN YAA ALLAH.

     

    Daga: Muhammadu Usman Gashua

    Share
  • Wani Matashi Dalibin Tsangaya Ya Rubuta Alkur’ani Da Hannun Sa.

    WANI MATASHI DAN MAKARANTAR TSANGAYA YA RUBUTA ALKUR’ANI

     

    Daga Babangida A. Maina

     

    Wani hazikin matashi kuma jajirtacce dan makarantan tsangaya wato makarantar Allo mai suna Goni Adam M. Sani ya rubuta littafin Alkur’ani mai girma.

     

    Goni M. Sani ya littafin ne wanda duk wani musulmin duniya yake shine littafin da Allah ya saukar masa mafi girma tun farkon duniya har zuwa karshen duniya.

     

    Muna addu’an Allah ya sanya Alkhairi a wannan hidimtawa addinin musulunci da yayi.

     

    Allah ya sanya Alkhairi ya sa Alkur’ani ya cece mu. Amin

    Share
  • Baiwar Da ALLAH Ya Yiwa Farfesa Sheikh Umar Sani Fagge.

    Prof Umar Sani Faqqe Yana Daya daga cikin Malamai na Nake So Na Haqiqa. Wallahi Nakan Zauna 1hr ko 2hrs don Sauraronsa.

     

    Idan Yana baka Tarihin ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA Billahillazi Zaka Rantse kace Yayi Zamani Da ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA

    .

    Haka Kuma Ina Yana bayani Akan Shugabanci Sai kace ko a gidanka baka son yin Shugabanci saboda Nauyin dake cikin ta

    .

    In Yazo bangaren gudun DUNIYA zaka Rantse kace ko takalmi ba zaka chanja ba har ka Koma ga Mahalicchinka

    .

    Ga tsoron Allah ga tawali’u ga gaskiya da rikon Amana wadannan Ababen duk inda ya Kama lectures akai Billahillazi har duniyan tsoron ta nake ji

    .

    Allah Ya Ja Mana Kwanan Sa, Allah Ya bashi lafiya da Nisan kwana Albarkan ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA. Amiiiin

    Share
  • Sheik Ibrahim Inyass yace; Amma ni bazan taba ganin Musulmi Mai sunan Manzon Allah SAW ba (wato Amadou Lamine-Guèye) na kyaleshi na zabi Kafiri ba,

    SIYASA DA TARIQA

     

    A 1960 lokacin da aka fara Siyasa A senegal Léopold Sédar Senghor Ya fito yana neman Shugabancin Qasa, Shima lokacin Amadou Lamine-Guèye Ya fito yana Neman Shugabancin Qasar.

     

    Kamar yadda Al’adar Siyasa take kowa Ya ringa tallata dan Takararsa kuma koya yakeso yace ra’ayinsa daya yake Dana Sheikh Ibrahim Niasse RTA, Har Abun yaso ya zama Rigima tsakanin Muridai.

     

    Da Sheikhu RTA Yaji Labari sai yasa aka Tara Muridai a masallaci sannan yace musu naji rikici yana so ya balle tsakaninku, Tsakanin wanda suke son Senghor da Lamine kowa yana danganta dan takararsa dani Toh ina so na gayamuku Abunda yake Tsakanina daku shine wannan (Sai Sheikhu Ya ’Daga Carbinsa Sama ya nuna musu). Ma’ana Tariqa ce kawai tsakanina daku.

     

    Sheikhu ya cigaba da cewa “Amma ni bazan taba ganin Musulmi Mai sunan Manzon Allah SAW ba (wato Amadou Lamine-Guèye) na kyaleshi na zabi Kafiri ba, Amma duk da haka Ban hana kowa ya zabi wanda yake so ba.”

    Naji wannan Qissar wajen Sheikha Bilqees Niasse RTAnha 2015

     

    ABUN LURA

    1-Wannan yana nuna mana Shehi bashi da iko ya takurawa Muridi wani dan takara.

    2-Haka zalika zamu fahimci cewa tariqa daban siyasa daban.

    3-Kamar yadda zamu fahimci wajibin Shehunnai ne su fito su hana muridai samun sabanin tsakaninsu.

     

    Daga: Aliyu Uthman Bashir.

    Share
  • Alkharan Da Sheikh Ibrahim Inyass RA Ya Jaddada A Rayuwar Sa.

    ABUBUWA DA MAULANA SHEHU IBRAHIM INYASS (R.T.A) YA JADDADA A RAYUWANSA

     

    Kadan daga cikin Abubuwan Da Maulana Shehu Ya Jaddada sune Kamar Haka:

     

    1: Yin Qabalu a cikin Sallah

     

    2: Raya daren Mauludin (S.A.W) da yawan ibada kamar yabon ANNABI S.A.W yadda akeyi akasar Hausa Yanzu

     

    3: Raya daren Isra’i da Mi’iraji da yin taro a ambaci Mu’ujuzojin ANNABI S.A.W

     

    4: Yin Bismillahi a fili acikin sallah kamar yadda yazo acikin Hadisai

     

     

    5: Maimaita “Qad Qamatissallati” sau biyu a iqama kamar yadda yazo a Hadisai

     

    6: Yawaita yabon ANNABI S.A.W da kuma saka kaunar ANNABI S.A.W a zukatan mutane

     

    7: Bayyana faira da kuma yin tarbiya a Hanunsa

     

    8: Zaburar da Al’umma da yawan karatun Al’qur’ani: wannan ne dalilin da yasa Shehu Ibrahim Inyass (R.T.A) duk sati yana saukar Al’qur’ani sau biyu daya tilawa na biyu takara

     

    9: Zaburar da mutane akan koyon harshen larabci.

     

    10: Jama’a su hadu su bayyana zikirin Allah yayin taruka na addini

     

    11: Gabatar da hudubobi a duk taruka na addini saboda kara yada musulunci

     

    12: Kwadaitar da almajiransa akan tsarkake Niyya da kuma Adalci tsakanin wadanda suke shugabanta tsakanin yayansu da almajiransu

     

    13: Shine wanda ya bayar da fatawar cewa za’iya saka karatun Al’qur’ani a Radio bayan duk malamai sun nuna rashin Amincewarsu da sakawa a Radio

     

    14: Shine wanda ya kafa makarantar koyon Addini da larabci dana zamani

     

    Wadanan sune Abubuwan kadan daga cikin miliyoyin abubuwan alkhairan da Maulanmu Shehul Islam (SHEHU IBRAHIM INYASS (R.T.A) ya jaddadasu

     

    ALLAH YAKARA AZURTAMU DA KAUNARSA DA YIN KOYI DA IRIN KYAWAWAN AYYUKA IRIN NA SHEHU R.T.A BIJAHI S.A.W. Amiiiin Yaa Allah

    Share
Back to top button