SHEIKH DAHIRU BAUCHI

  • Duk Wanda Baya Son Mauludi, Baya Son Manzon Allah SAW. Inji Sheikh Dahiru Bauchi OFR

    Shahararen malamin addinin Musulunci kuma shehin Darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR ya bayyana Halarci yin murnan Mauludi.

     

     

    Sheikh Dahiru Usman Bauchi yace: Duk Wanda Baya Son Mauludi Baya Son Manzon Allah SAW. a cikin TAFSIR sa wanda yake gudanarwa duk shekara a Masallacin Tudun Wada dake birnin Kaduna a Nigeria.

     

    Alhamdulillah, Allah ya karawa Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR lafiya da nisan kwana albarkan wannan Mauludi. Amiiiin Yaa ALLAH

  • Sheikh Dahiru Bauchi RA; Wannan Shehin Malamin Duk Ni’imomin Duniya Babu Wacce Allah Bai Yi Masa Ba.

    ALLAH ABIN GODIYA: Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi (RTA)

     

    Wannan Shehin Malamin duk ni’imomin duniya babu wacce Allah bai yi masa ba:

     

    • Allah Ya yi masa baiwar ilmi

    •Allah Ya yi masa dogon kwana

    •Allah Ya yi masa baiwar lafiya

    •Allah Ya yi masa kyawun halitta.

     

    •Allah Ya yi masa baiwar ɗaukaka

    •Allah Ya yi masa baiwar zurri’a

    •Allah Ya yi masa baiwar wadata.

     

    Muna addu’an Allah ya karawa Shehu lafiya da nisan kwana albarkacin Manzon Allah SAW. Amiin

     

    Daga: Mutawakkil Gambo Doko

  • Mauludin Annabi Muhammadu SAW Umurnin Allah Ne, Inji Sheikh Dahiru Bauchi RA

    MAULUDI UMARNIN ALLAH (S.W.T) NE

     

    MAULANMU SHEIKH TAHIRU USMAN BAUCHI(R.A) Yana Cewa;

     

    “Idan Ka Ji Mutum Yana Sukar MAULUDI, To Ka Ce Masa; Ai MAULUDI Iri Biyu(02) Ne:

     

    *. Akwai MAULUDI Na Zamani Wato Watan RABIUL AWWAL, A Watan Bature Kuma a APRIL, Wannan Shi Ne MAULUDI Na Zamani,

     

    Akwai Kuma MAULUDI Na Makani(Wuri) Wato MAKKAH Da MADINA,

     

    SHEHU(R.A) Ya Ci Gaba Da Cewa; Idan Mutum Ya Samu Kudin Zuwa Hajji Zai Tafi Dolensa, Shin Anan Waye Ya ‘Kra Shi???

     

    Aka Ce; ALLAH(S.W.T),

     

    Don Haka Duk Wanda Ya Tafi MAKKAH Da MADINA, To Ya Tafi MAULUDIN MANZON ALLAH(S.A.W) Ne Na Makani,

     

    Zai Je Ya Ga Inda Aka Haifi ANNABI(S.A.W),

    Ya Ga MasallacinSA,

    Ya Ga GidanSA,

    Ya Ga Ababen Da ANNABI(S.A.W) Yayi Rayuwa Da Su,

     

    Don Haka Kenan Dole Ne Musulmi Yayi MAULUDI, Ko Na Makani Wato Zuwa MAKKAH Da MADINA, Ko Na Zamani ‘Din Wato Watan RABIUL AWWAL Ko APRIL, ALLAH Ya Barmu Da Son ANNABI(S.A.W)”.

     

    Allahumma Ameeeen

     

    ALLAH Ya Kara Lafiya Da Nisan Kwana MAULANA SHEIKH(R.A). Amiin

Back to top button