SHEIKH AHMAD TIJJANI

  • SHEIKH AHMADU TIJJANI RA; Haifuwar Maulana Sheikh Ahmadu Tijjani RA Tarihin Sa Kashi Na Biyu 2.

    MAULIDIN SHEHU AHMADUT TIJANI (R.A)!!!

     

    CI GABAN TARIHIN RAYUWAR SHAIKHU AHMADUT TIJANI(R.A) KAMAR KUNA TARE:

     

    KASHI NA BIYU(02):

     

    *. HAIHUWARSA(R.A):

     

    An Haife Shi Ranar ALHAMIS Sha Uku(13) Ga Watan Safar(2) Shekara Ta Dubu ‘Daya Da ‘Dari ‘Daya Da Hamsin Bayan Hijirar ANNABI(S.A.W) (1150 B.H). Wanda Yayi Dai Dai Da Sha Biyar(15) Ga Watan Shida(6) Shekarar Miladiyya Dubu Daya Da Dari Bakwai Da Talatin Da Bakwai(1737 A.D).

     

    A Garin AINU-MADHI Wanda Yake Cikin Lardin LAG’WAT a ‘Kasar Aljeriya, Kakansa Sayyidi Mahammadu ‘Dan Salimu Shi Ne Ya Fara Zama a Wannan Garin Amma Basu Da Dangantaka Da Mutanensa Sai Ta Surukuta Kad’ai.

     

    Abin Da Yasa Ake Cewa Da Shi ‘TIJANI’ Shi Ne Saboda Wata ‘Kabila Ce Mai Suna; ‘Tijanatu’ Wadda Ita Ce Asalin Kakanninsa Mata.

     

    Mahaifansa Suna Da Wadansu ‘Ya’yayen Banda Shi Maza Da Mata Yayye Da ‘Kanne Amma Dukkanninsu Sun Rasu Ne a Zamanin Rayuwarsa, Daga Cikinsu Akwai:

     

    1 – Yayarsa Sayyida Rukayyatu, Tana Zuwa Gidansa Bayan Bunkasar Lamarinsa, Ya Girmamata Ya Sanya a Rakata Har Gidanta a Ainu-Madhi, Ta Rasu Ta Bar ‘Da ‘Daya Mai Suna Sayyidi Abdullahi Wanda Makarancin Qur’ani Ne Kuma Malami Ne Ya San Ilmin Hisabi Sosai, Kuma Yana ‘Daya Daga Cikin Almajiran Shaikhu(R.A).

     

    2 – Sayyidi Muhammadu, Wanda Shima Mahaddacin Qur’ani Ne Kuma Masanin Shari’a Ne Wanda Yayi Fice a Bangaren Ilmin Gado Da Na Hisabi, Ya Rasu Ne a Ainu-Madhi Ya Bar ‘Ya’ya Biyu Namiji Da Mace Wadanda Shaiku(R.A) Ne Ya Rike Su.

     

    *. TARBIYYA DA NEMAN ILIMINSA(R.A):

     

    Shaiku (R.A) Ya Tashi a Cikin Tarbiyyar Mahaifansa Da Kamewa Da Tsoron ALLAH Da Son Addini Da Ladabi Da Kyawawan Dabi’u, Bai San Yawancin Al’adun Da Mutane Suke Yi a Cikin Gari Ba.

     

    Ya Haddace Qur’ani Mai Girma Da Ruwayar ‘Warshu’ a Wurin Malaminsa Sayyidi Muhammadu ‘Dan Hamu Yana ‘Dan Shekara Bakwai (7).

     

    Bayan Ya Haddace Qur’ani Sai Kuma Ya Shiga Neman Ilimi, Ya Fara Da Karanta ‘Akhdhari’ Da ‘Ibnu Rushdi’ Da ‘Risalah’ ‘Mukhtasaru Alkhalili’ a Wurin Malaminsa Sayyidi Mabruku ‘Dan Bu’afiyatu..

     

    ALLAH Ya Bamu Albarkar Masu Albarka. Amiin

    Share
  • TARIHIN SHEIKH AHMAD TIJJANI RA: Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani Kashi Na Farko (1).

    MAULUDIN SHEHU AHMADUT TIJJANI(R.A).

     

    TARIHIN RAYUWAR SHAIKHU AHMADUT TIJANI(R.A) KAMAR KUNA TARE:

     

    KASHI NA FARKO(01):

     

    *. DANGANTAKARSA(R.A):

     

    Shi Ne; Shaikhu Abul’Abbasi Ahmadu

    ‘Dan Mahammadu

    ‘Dan Mukhtaru

    ‘Dan Ahmadu

    ‘Dan Mahammadu

    ‘Dan Salimu

    ‘Dan AbuI’idi

    ‘Dan Salimu

    ‘Dan Ahmadul Alawani

    ‘Dan Ahmadu

    ‘Dan Aliyyu

    ‘Dan Abdullahi

    ‘Dan Abbasu

    ‘Dan Abduljabbari

    ‘Dan Idrisu

    ‘Dan Idrisu II

    ‘Dan Is’haku

    ‘Dan Aliyyu Zainul’Abidina

    ‘Dan Ahmadu

    ‘Dan Muhammadu Annafsuzzakiyyatu

    ‘Dan Abdullahi Alkamilu

    ‘Dan Hasanu Almusanna

    ‘Dan Hassanu

    ‘Dan ALIYYU Da FADIMATU(Radhiyallahu Anhuma) ‘Yar SHUGABAN HALITTA(S.A.W).

     

    SHAIKHU(R.A) Ya Gaji Wannan Dangantaka a Rubuce a Gidansu, Amma Bai Ta6a ‘Kiran Kansa ‘Sharifi’ Ba Har Sai Da Ya Hadu Da Wanda Baya Yin Magana Ta Son Zuciya(S.A.W) Ya Ce Masa:“Kai ‘Da Na Ne Tabbas”. Har Sau Uku(03).

     

    Kuma Ya Ce Masa:“Dangantakarka Zuwa Kan Hassan Ingantacciya Ce”.

     

    Mahaifiyarsa Kuwa Ita Ce Sayyida A’ishatu ‘Yar Muhammadu ‘Dan Sanusi.

     

    Baki ‘Dayan Kakanninsa Malamai Ne Masu Ibada Da Tsoron ALLAH Da Gudun Duniya, Kowa Ya Sansu a Fagen Ilimi Da Walittaka. Sai Dai Saboda Tsananin Bin Sunnah Suna ‘Boye Walittakarsu Ta Hanyar Bayyana Ilimi.

     

    (Daga Littafin; Khalipha Yahya Nuhu Sallau),

     

    ZA MU CI GABA GOBE INSHA ALLAHU….

     

    YA ALLAH! MUNA ROKONKA KA ‘KARA MANA SON WALIYANKA, KA KAR’BI RAYUWARMU MUNA CIKAKKUN TIJJANAWA NA HAQIQA DON ALFARMAR SAYYIDUL-WARA (S.A.W) AMEEEEN

    Share
Back to top button